Sashe 1
Wutsiyar Rakumi Complete Hausa Novel · about 3 min read
*_Typing📲_*
*_💡HASKE WRITER'S ASSOCIATION_*
_(Home of expert and perfect writer's)_
*_💞WUTSIYAR RAK'UMI....!!💞_*
_(Tai nesa da k'asa)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ*
_In the name of Allah, the Entirely Merciful, the Especially Merciful._
*_Alhamdulillahi, barkanmu da dake saduwa a wanan littafi WUTSIYAR RAƘUMI...., ALLAH ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al'ummar MANZON ALLAH, ka tsare harshena da hannayena rubuta abinda zai cutar daku dani baki ɗaya😭🙏🏻_*
*_Ya rabbi ka gafartama masoyina, mahaifina, da dukkan sauran al'ummar musulmi tundaga zamanin Annabi adam har kawowa yau😭🙏🏻_*
_Ban yarda wani wani yaymin amfani da buk ɗinnanba ta kowacce hanya sai da izinina😊🙏🏻._
*_No. 1_*
*_ƘAUYEN ƊILAU_*
Tun daga farkon dosowa kwanar gidan zaka farajin luguden daga da taɓare, yayinda mata ke arerewa da shewa irinna nishaɗin madaka, hardama masu buɗe hanci su callara guɗa a kwashe da dariya ana ƙara ƙaimi wajen dakan surfen masarar tuwo ko dawa da akeyi.
Na kutsa kai cikin gidan domin ganema idona wainar da ake toyawa, mata ne da adadinsu zai iya kai goma sha, sun kasu group-group suna daka a turame da aƙalla zasukai huɗu. A gefe kuma ƙarƙashin inuwar dalbejiya wasu matanne dasuka ɗan manyanta zazzaune suna tasu hira da taɓin daddawar sayarwa ta ɗaya a cikinsu, sai wata can gefe tana faman hura wuta a gabanta da bokitan fenti biyu, maida kallona nayi ga wadda ke gefenta tana ta motsa wani abu a tunya tamkar taliya, sai zabga zufa take saboda hucin wutar da itama take aiki kusa da ita, sai kuma da'irar yara daketa sheƙi da ƙasa suna wasa.
Wanda bai san BABBAN GIDA ba a garin Ɗilau idan yazo zai iya rantsuwa taron biki sukeyi kona suna, sai dai sam ba haka baneba, dukkan waɗannan jama'ar da kuka gani mazauna gidanne, a hakama babu wasu yaran masu wayo da kuma mazan gidan, wasu sun tafi binni neman kuɗi, yayinda ƙalilan a cikinsu suna waje a majalisun da mazan ƙauyen kan kafa, yara kam wasu an aikesu wasuko hidimar gabansuce ta fiddasu.
Duk bayanin dazan muku gameda alaƙar jama'ar wannan gida bazaku fahimtaba, dan kuwa ƴaƴan wane dana ƙanne da ƴaƴan ƴaƴa da matansu, kai harma da jikoki sun auro suma kuma sun hayayyafa.
Malam Buhari shima mazaunine a wannan gida, kuma yana ɗaya daga cikin wannan ahali, matansa uku da ƴaƴa goma cif, matarsa ta farko itace Yalwa, amma suna kiranta da suna baba yalwa, yaranta biyar, uku maza biyu mata, kasancewar mazan sune manya duk sunyi aure, suma matansu na nan acikin gidan, sai ta biyu, Ɗahara, itakam ƴarta ɗaya Ummukulsoom, haihuwarta kusan huɗu amma suna wabi (suna mutuwa bayan ta haihu), sai akan Ummukulsoom ne ALLAH ya barmata, bayan haihuwar Ummu takuma samun ciki, a wajen haihuwar cikinne ta rasu, lokacin Ummu tanada shekara Uku a duniya. Sai amarya Asabe, yaran Asabe huɗu, mata uku sai Namiji ɗaya shine auta.
Sana'ar Malam Buhari itace Saƙar mafitai da tabarma, fai-fai irinna fulani dadai sauransu, shiyyasa ake cemasa MAI KABA. Bama shiba duka jama'ar gidan wannan sana'ar suce, sai dai kuma wasu sun bari tuni, sai ƙalilan a matan gidan keyi, shidai ya riƙe gam kuma yanacin amfaninta, dan yakan ɗauka yashiga birnin Kaduna da Zaria ya sayar ya dawo gida, wani lokacin kuma ƙanwarsa Laraba dake aure acan take aiko ɗanta ya karɓa kokuma ita tazo da kanta.
Da wannan sana'ar malam Buhari ke riƙe da iyalansa, sai noma da yake a kowacce damuna.