Sashe 54
Wutsiyar Rakumi Complete Hausa Novel · about 5 min read
itama”. Gaba ɗayanmu mun tsorata da kalamanta, danni harma na fara hawaye, da ƙyar muka ɗauke numfashi yayinda zata wucemu, a ranar bamuyi barcin sauran darenba daya rage. Washe gari tunda safe muka nufi gidan ƙanwar mahaifiyarmu muka sanar mata abinda mukaji, itama hankalinta ya tashi, dan haka tace mu turo mata Ibrahim idan yazo. Dato muka amsa, cikin amincin ALLAH kuwa washe gari saiga Ibrahim, dayake a lokacin a ɓoye muke haɗuwa, shine na sanar masa da zancen Innarmu. Bai musaba mukaje wajenta. Bayan sunyi gaisuwar mutunci tace, “Bawan ALLAH da gaske kake son ƴata kuwa?”. Cike da ladabi Ibrahim yace, “Wlhy Ina sonta Inna, kuma a shirye nake na aureta ko a yanzunnan ne”. “To Alhmdllhi, yanzu inaso ka ɗauki Umma kuje garin ɗan-gamau a katsina, idan kunje garin kuyi tambayar gidan Malam Baushi, kuyi masa bayanin komai daya faru, kuce masa nace ya ɗaura muku aure, Ibrahim ga amanar Umma nan, idan kaci ALLAH ya ci taka, karku zo Ɗilau saita haihu”. Godiya mukai mata muduka muna kukan jin daɗi, a ranar muka tafi babu wanda yasani har Hindatu, duk yanda Inna tace muyi haka kuwa mukayi, Malam Baushi ya ɗaura mana aure, satinmu ɗaya a can Ibrahim ya ɗaukeni muka wuce legas wajen aikinsa, ban fuskanci matsala a wajen danginsa ba danshi marayane. Ban sake waiwayen garin ɗilau ba, dukda kuwa ina matuƙar kewarsu, sai da na shekara biyar, dan har lokacin ban haihu ba, saida na shekara biyar da wasu watanni nasamu cikin Abubakar, bayan haihuwarsa naso zuwa Ɗilau domin cika alƙawarin inna amma sai wani aiki ya riƙe Ibrahim, dan haka ya bani haƙuri, dan shi burinsa muje tare mu nemi gafarar baba, zamu-zamu tafiya bata yuwuba har na yaye Abubakar, kwatsam kuma saiga wani cikin, ganin haka sai Ibrahim ya lallabani akan nai haƙuri na haihu saimu tafi, ƙilama Baba yafi karɓarmu. Hakance ta faru kuwa, dan saida na haihu tagwaye duk mata sannan muka shirya zuwa ɗilau. Komai ya canja mini daga yanda na sanshi, abubuwa da yawa kuma sun faru, dan ansha tashin hankali bayan nemana da akai aka rasa, a maimakona sai aka ɗaurama Hindatu Aure da ɗan-asabe, baba kuma yace ya barma duniyani, har abada ya cureni cikin ƴaƴansa. Har zuwanmu ɗilau baba na akan bakansa na ƙin karɓata, dankuwa muna fita a mota bai bari nataka koda zauren gidanmu ba yace mu juya, tareda furucin inhar na sake dawowa garin ɗilau ALLAH ya isa bai yafemin ba. Hajiya Yaya ta fashe da kuka mai tsuma rai, wanda yasaka su Ummukulsoom da Attahir harma da Abba kuka suma, da ƙyar Hajiya yaya ta tsagaita taci gaba da faɗin, “Bansan yanda zan fassara muku halin dana shigaba dagani har ibrahim, da ƙyar nasamu wani ya faɗamin inda Hindatu take aure, Lurwanu kuwa na iske ya rasu sanadin zazzaɓi da yayi. Naje gidan Hindatu, muka rungume juna muna kuka, na isketa har tayi haihuwa Uku ita, ƴar da take goyo ma tsakanin haihuwarta da ƴan biyuna kwana ukune, na amshi ƴar saina ganta a langaɓe, hankali tashe na kalli Hindatu da itama take kallona tana kuka. “Hindatu miya sametane?”.. “Yaya ta rasune yanzunnan, ina kukan mutuwartane ma kika shigo”. Sosai hankalina ya tashi nima, na rungume yarinyar a jikina ina hawaye, muna cikin haka saiga ɗan aike daga baba, yace inhar ban zo nabar garinnanba yazo gidan hindatu ya iskeni saiya min abinda ban taɓa tunaniba, kuka na kuma fashewa dashi, na kalli hindatu da itama kukan takeyi. “Hindatu dan ALLAH kimin wani taimako kafin nabar garinnan”. “Inajinki yaya ki faɗi komiye zan miki”. “Hindatu ba kowa yasan ƴarki ta rasuba, dan ALLAH ki bani gawarta, nikuma na baki guda ɗaya cikin ƴan biyu, inason ɗaya a cikinsu ta tashi a garin haihuwata, tunda ni an haramtamin koda zuwa cikinsa, dan ALLAH hindatu ki taimakeni, nasan har abada ba sake haɗuwa zamuyiba”. Fashewa tayi da sabon kuka tareda ƙankameni, tace, “Yaya mizai hanani aminta da shawararki, wlhy na yarda, ke kaɗai gareni kaf duniya, gashi kuma ƙaddara ta daɗe da shiga tsakaninmu, mizai sa bazan ji daɗiba idan har kika bar jininki a wajena amatsayin ƴar dana haifa”. Nace Na gode hindatu, sauri sauri muka cire kayan jikin Hassana muka maida jikin gawar Ɗahara, na ɗahara muka sakama Hassana, inaji ina gani nataho na baro ƴata hannun ƴar uwata, ko mahaifinta bai saniba, dan baba tozarci bana wasaba ya shigo har gidan Hindatu yanamin dagani har Ibrahim dake mota yana jirana shida Abubakar dake ya yayye. Saida mukazo gida nace masa Hassana ta rasu a madadin gawar Ɗahara ɗiyar Hindatu, damuwar da muke cikice ta kauda damuwar rasuwar Hassana a zuciyarsa, niko inata kewar ɗiyata tunda nasan bata rasuba. Tun daga wannan ranar ban kuma waiwayar ɗilauba, tunma ina kuka harna haƙura, naci gaba da rainon Husaina, bayan shekara biyu Husaina ta rasu saboda ƙyanda da tayi, daga nana Abubakar kaɗai ya rage mana a gabanmu, a legas muka cigaba da rayuwa har Abubakar yakai minzalin aure sannan muka dawo kd, koda muka dawo ban taɓa waiwayen ɗilauba, saboda katangar da Baba yaymin da ita, Har ALLAH yayma Ibrahim rasuwa bayan haihuwar Attahir kuma yanata burin hakan, amma ALLAH yay alƙawarin bazai sake taka ƙasar canba shiyyasa harya rasu bai cika alƙawarinsa na dai-daitani da Baba ba. Wannan shine labarina, inaji a jikina kuma lallai Ummukulsoom tanada alaƙa da ahalina, amma tambayoyin dazan matane kawai zasu bani wannan tabbacin. Jikin Hajiya Ummukulsoom ta faɗa ta fashe da kuka, “Hajiya wlhy basai kin tambayeni komaiba, ni ɗin jininki ce, dan kaf sunayen waɗanda kika ambata sun tabbatar min da hakan, Gwaggo hinde kakata ce, itace ta haifi mahaifita Ɗahara......” Ɗagota da sauri Hajiya yaya tayi, jikinta har rawa yake tace, “Da gaske kike ƴarnan?”. “Wlhy hajiya na tabbatar da hakane kuwa”. Fashewa da kuka Hajiya yaya tayi yanzu kam mai ban mamaki da yafi na ko yaushe, tabbas inhar maganar Ummukulsoom gaskiyane to itaɗin jinin ƴartace Hassana data bama Hindatu.