← Book details Walijam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 19

Sashe 17

Walijam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inalillahi Anwar kaine Aka aura mawa bafullatanan??cewan Sadeeq yana fiddo da idanun sa waje kaman wanda aka kamasa yy karya .kai dallah malam Dan rufe mana baki ,a hamdalah zamuyi ma Allah domun ko samun Bafullatana a yanxu dace ne sai wanda Allah yaba . Cewan Abbas yana daukar cup din dake gaban Anwar yana shan ruwan giyan dake ciki .

Kallon Banza su duka suka watsa masa ,kamin Abbas ya cigaba da cewa " ni wlh kaga ma faduwa tazo dai dai da zama ,idan zamuje dauko amarya sai na tsaya neman tawa matan ko ya kukace . Kallon shi Anwar yayi kaman zai masa mgn sai kuma ya ta6e baki don ma baida lokacin sa yafara tunanin Abbas ba a hankalin sa yake ba . Uhmm mikewa Anwar yayi yana cewa kai kumu hade a wurin training yana fadin haka ya fice yabar Sadeeq da baki bude ,shi kuma abbas na cigaba da kwarara gear din sa .

**********

Bangaren Dr Haulat kam abun duniya ya dameta sam bata da walwala ko dariya ,fuskan ta kullum a daure yake babu fara'a sam ,abu daya take tunowa taji sanyi shine cewan da Zabeenart tayi a yanxu Anwar yana sakin mata fuska har suyi mgn amaimakon da baya .

Nisawa Mom Anwar tayi tana mgn a fili da cewa " tun a sali ni najawo mawa kaina ai ,da na fadi abun da nakeso anwar yayi da tuni ya Auri Zabeena da yanxu ban zauna da tagumi ba mtsww taja karamin tsaki tana cigaba da bin ma'aikatan da take hango su ta haraban gidan a jikin windon ta kowa na aikin sa .

Ji tayi an hugging din ta ta baya an rungumeta sanyaayyar turaren ta na mamaye ilahirin falon Dr Haulan ". Murmushi tayi kamin ta juya tana jagayo da zabeena ta gaban ta tana mai fadada fara'ar ta ganin zabeena ta saki jikin ta fiye da kullum , sanye take cikin shiga lace riga da skirt blue da milk colour nasa sai karamar mayafin dake rike a hannun ta mai launin milk ,takalmin kafarta mai dan tudu .

Kissing din ta Dr Haula tayi kamin tace " yau kuma Daughter na ina zataje ne da sanyin safennan ?. Murmushi Zabeena tayi tana far da ido kamin tace "Ai mom jiya na yanke shawarar zuwa zaria naje wurin Anwar acan gidan sa xan zauna don in shiga tsakanin su da wannan shegiyar yarinyar don Mom bazan dawo ba sai naga Aurennan ya mutu ,ya zama nice kadai a zuciyar Anwar sannan . Inaso naje mukara sabawa da juna sannan .

Murmushi Dr Haula tayi cike da jin dadin maganan Zabeena kamin tace " kai da kyau Daughter na ,nima kaina ina nan inata tunanin ta yanda zan bullo mawa al'amarin ,kije ki zauna tare dashi ya ware maki dakin ki ,Komai da yake faruwa a gidan mu rinka communicate kinji diya ta . Yanxu kamin ki isa Zan kira Anwar din maxa allah shi tsare ya kiyaye mun ke Zabeena .

Ameen Mommy na tafi ,tayi mgnan ta na juyawa hadi da ficewa daga dakin tana barin mum tana sakin murmushin farin ciki don zabeena itace wacce zata sa ta lalata komai na wannan tsakin . A zuciyar ta tana mai kara jin tsanar Hajiya Rahamatu da ta dauki komai na ragamar kayan lefe . Tuni dangi aka dauka masu farin ciki nayi masu taya hajiya Haula bakin ciki nayi ,duk da masu farin cikin sunfi yawa ,don kowa yasan makirci na Hajiya Haula ,taki kowa a dangin mijin ta ,babu mai ra6ar arxikin ta na d'anta da mijin ta ,wannan dalilin yasa da yawa suke farin ciki da wannan auren ,dama shi Alhji jalingo mutum ne da bai damuwa da Talaka da mai kudi dukka ya dauke su yan uwa kuma nashi ne .

*********

Tun da Anwar ya shiga barikin sojojin bai dawo gidan sa ba sai magriba don bai san da zuwan Zabeena ba .

Tun da ya shiga falon gidan nasa a saman cushunes din falon yaga jakar mace da mayafi . Mmki ne ke ciyosa a zuciya amma abunka ga muskili sai ya dake yana nufar bedroom din shi toilet ya fada hadi da watsa ruwa yana dauro alwala . Bai fito falon ba sai da yy sallan magriba kana ya fito sanye da jallabiya . Muryar Zabeena yaji a kitchen ita da mai kulada komai na girkin sa daniel . Mamaki ne ya kamasa matuka sai ya nufi daya daga cikin kujerun falon yana zama dai dai Zabeena na fitowa.

Da gudu ta nufesa cike da kissa da yaudararriyar murya ta ke fadin oyoyo wlcm back dear tana hayewa saaman cinyan sa hadi da rungumesa . Tana manna masa kiss a saman lips din shi .

Wani irin yarrr yaji tsikar jikin shi na tashi ,wanda cike da murtike fuska yace " Zabeena mai ya kawoki da wannan lokacin har a yaushe xaki koma gida ne ".

Yana mgnan hadi da rabata da jikin sa ta mike daga jikin sa badon taso ba .. Lokaci daya taji ranta ya baci ya kuma sosu ,murtike fuska yayi ganin yanda ta kafesa da ido ta rashin kunya ,don bayason raini sam .

Ba magana nakeyi maki ba?? Yayi maganan yana kare gimtse fuskar sa tamau . Abunka ga yar duniya ,tuni tafara matso kwallah tana jah da baya a hankali hadi da cewa" yo dama don na taho gidan ka shikenan nayi laifi ,baxan zauna gidan ka ba ,ai mom tace zata fada maka zan zo 😣, Amma shikenan tun da bakayi farin ciki da zuwa ba ba kaso ba ba damuwa kayi hakuri nayi laifi .

Tana fadin haka ta juya tana nufar dakin ta da tayada zongo da komai nata ...dafe kanshi yayi don sai asannan ya tuna da Kwarai kuwa Mom ta fada masa zuwan ta . A hankali ya mike yana bin bayan ta don yasan yanxu kayanta zata hada tace xata bar gidan...!!

Abunko da yayi tunani hakan ta faru don kuwa har ta gama hada kayanta tana daukar jakarta .

Zama yayi zaman royal bed din yana kallon ta kaman bazai mata mgn ba sai kuma yace " Ina ne kike hada kayanki zakije . Shiru tayi bata basa amsa ba don tukukin bakin cikin dake ciyota ,sai kuma a gajarce tace " zan koma inda na fito gidan Mom nasan ita baxata wulakantani ba ko bayan ran iyayena bare kuma dasu a raye .

Tana maganan hadi da daukar jakarta tana takawa hadi da nufan kofa...bai tankata ba sai danna wani lock remote da ya rufe ko ina Bedroom din . Burda kofan tayi da zummar ficewa daga dakin nan taji ta a rufe .

Kara murdawa tayi nan ma taji a rufe yake hakan yasa ta juyowa don ta tayi masa mgn ,amma cike da mmki ta bude baki ne ta ganshi ,shi ya koma ma ya kwanta ne abun shi bama ya ta kanta ,sai idon shi dake akan wayan hannun shi fuskan shi na kallon sama.

Mu tare a page na 25 kuma na karshen free page inshaallh💃💃

Hazarta wajen biyan naki kudin littafin Kar ayi baki ,domun kuwa lbrn yanxu take yanxun zaa fara💃💃

_*Littafin WALIJAAM na kudi ne kaman yanda kuka sani*_
_*Ga masu bukatar wannan littafi xasu na iya mgn dani ta wannan whatsap link din👇*_
https://wa.me/qr/7UGIAODZY3LON1

_Normal grp 200_
_Vip grp 500_
_Spc group 1k👌_

_Idan kati xaki turo MTN ne ._
_Idan kuma ta account ne ta nanan👇_
_0028799846_
_Farida Hashim stanbic bank_

_Yan niger kuma zaku tura katin 500f ne na Airtel ta wannan number na kasa👇_
_+22797780373_
_Idan kuma Spc grp kk bukata 800f ._

_*Maman teddy🧸*_
08081202932
*🐄WALIJAAM🐄*

LAST FREE PAGE
25

_Daga wannan shafin free page yak'are mai bukatar cigaban wannan labarin zai iya biyan kudin sa ta wannan number....08081202932...Vip payment 500...normal payment 200...Special payment 1k. Zaku iya turo da katin MTN ko ta wannan Account din Hashim Farida Stanbic Bank 0028799846... Yan nijer zaku iya tura 500f airtel sai ku tuntubi wannan number +22797780373_
_Don Allah kar wasun ku su jira fitowar na sata ,babu abu mai muni da yakai cin hakkin mutum ,wannan Hakki na ne dana 6ata shi tsawon lokaci don kawai na isar da sakon da nakeso... akan wannan dan kud'a d'en bai kamata ku karanta shi a bulus ba Don nasan dai 200 babu wacce zata ce batafi karfin shi ba indai kina media... kar ki ci Hakkin wani wlh masiba ne cin hakkin da banaka ba mu kiyaye don Allah..._
_________________________
"Bin shi da kallo kurum Zabeena ta tsaya tana yi kamin ta koma ta ajiye jakar nata...tana zama gyefen gadon hadi da karkade kafarta don tagama har zuka da lamarin Anwar a yanxu". Tsawon lokaci suka kasance a hakan babu wanda yakara ce mawa dan uwan sa ci kanka ,kamin daga bisani ya mike yana nufar kofa hadi da ficewa daga bedroom din yana kara sa mawa Kofan key...murmushi zabeena tayi tana tunanin abubuwa da dama data kudurta yin shi a wannan gida ,ta lashi takobin tarwatsa duk wata farin ciki na Anwar indai akan wannan bagidajiyar bafullatanan ce...

"Tun ana saura kwana biyu tarewan Shatu Hjy Rahmatu ta sauka a gidan Anwar na barack din da masu room decoration wanda suka kara kayata Gidan matuka wanda sam bazaka ce wai a cikin wannan barikin sojojin yake ba...Bata damu da ganin Zabeenart ba duk da taasan zuwan nata da akwai dalili akwai kulalliyar da suke shiryawa ita da Dr Haulan ,amma ta kawar da lissafin su a kwakwalwarta don tariga da tasan komai zasuyi aikin gama yagama ihu ne bayan hari kawai .
Chapter 17 · 0% Book details