← Book details Tuzuru Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 8

Sashe 1

Tuzuru Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[18/12 à 08:14] Mrs SADAUKI 💫: *TUZURU*🙊
```Love
and
romantic story```

```MRS SADAUKI 💫✍🏻```

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*

_______________________

*PAGE 1&2*

MARADI ADS

A hankali ya ke saukowa daga matakala hannun shi riƙe da hullar kakin soja wadda tayi machin da tenue shi ta sojawa.Fuskar nan a murtuƙe kamar tsohon kunun da aka dama ba'a sha ba,dogo ne fari sol mai ƙirar ƙarfi ya na da saje baƙi siɗik wanda ya ƙawata doguwar fuskar sa.Ƙaton ƙirjinsa mai manya muscules kawai in ka kalla ya isa ya firgitaka saboda yanayin yadda ya buɗe yayi faɗi ƙwanjinsa tamkar za su fasa riga su fito.

Gaban mahaifiyar shi ya zo ya tsugunna ya sunne kai ba tare da ya kula ƙannan sa da suke jero mashi gaisuwar Barka da safiya ba.
Ɗan ɗagowa yayi kalleta jin tayi shiru ba kamar yadda ta saba mashi ba,ido ya rausaya uwanda suke blue kamar na mage can ƙasan maƙoshi yace "please"kawar da kai tayi kafin ta ɗora hannunta bisa sumar kan shi wacce ba ta dayawa sosai amman gyaran da ta ke sha yasa tayi kyau da sheƙi "Allah ya tsare ka a duk inda kake"shine abinda datijuwar matar ta faɗa miƙewa yayi tsaye ya na sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗora hullar sa a kai ya na daidaita mata zama.
Kallon ƙannan na sa yayi uwanda duk suka ƙame waje ɗaya su na numfashi sama-sama tsabar tsoro,kai ya jinjina masu alamar ya amsa gaisuwar da suka yi masa kafin ya fice.

Da sauri Faruk ya tarbe sa haÉ—i da sara mashi kafin ya buÉ—e masa mota ya shiga,gate man ya buÉ—e porte Faruk ya fita da mota a slow har sai da suka hau titi sannan ya fara sharara gudu kamar zai tashi sama.
Babu jimawa suka kawo compagnie ɗin wacce ta ke birjit da sojoji ta ko ina,shigowar motar shi ne yasa sojawan ƙara daidaita tsayuwar su haɗi da ƙamewa kamar wasu tsuntsaye.
Cike da ƙasaita ya fito lokacin da Faruk ya buɗe masa mota,tafiya ya soma irin ta jaruman maza duk in ya taka sai ƙasa ta amsa saboda yanayin ƙirar sa ta samudawa.

Office ɗin da aka tanadar dominsa Faruk ya buɗe kafin ya bashi gu ya wuce,wani dadaɗan ƙamshi ne ya bugi hancinsa wanda ya sa shi lumshe ido bai shirya ba.Office ɗin ya fara bi da kallo yadda aka ƙawata sa fiye da kullum yau ma ƙamshin daban ne,faux du fleure🌹 ɗin da ya gani tsakiyar teburin shi ya bashi mamaki a zuci yace "yaushe kuma aka za wannan?"taɓe baki yayi ya samu gu ya zauna takardu ya jawo domin dubawa sai dai tunanin Mami ya faɗo masa a rai yadda ta ɗaure fuska ta canza ma shi sam bai ji daɗin hakan ba.
Baya yayi da kujera ya na mai lumshe ido tare da sauke wani huci,Faruk ya turo ƙofa ya shigo hannunsa riƙe da coffe.Bisa table ya ajiye kafin yace "ya dai?"ɗagowa Général Waleed yayi ya dube shi kafin ya ɗan harare sa bai tankasa ba ya ɗauki Coffen ya fara kurɓa, murmurshi Faruk yayi yace "ɗan gaban goshin Mami yau kuma wa ya taɓo ka?"sai da ya gama shan Coffen sannan ya dubi Faruk yace "da farko dai kai ne na biyu kuma Mami"ya ƙare zancen da kwaɓe fuska kamar wani ƙaramin yaro.
Kujera Faruk ya ja ya zauna yace "to faɗa min mi nayi?dan dai ita Mami na san gatanar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi"hararar wasa ya kuma yi mashi kafin yace "wace gatana kuma?"Faruk yace "ta aure mana,ka san fah abun na damun Mami dan jiya ma mun yi zancen sannan ya kamata kai ma ka yiwa kan ka ƙiyamul laili ka girma ka ƙosa tun ka na cikin sahun samari yanzu har ka zama *TUZURU* duk sa'anin ka sun yi aure"kai Général Waleed ya dafe yace "aure?aure,aure dai?"Faruk yace "Yes !"tashi yayi tsaye yace "ni fah ba auren ba ne ban so a'a raini ne ban so yarinya ƴar ƙarama ta rinƙa baka ordre mtsw..."ya ja wani tsuki ya na girgiza kai ya cigaba da cewa "sam ba zan iya ɗaukar iskanci ba"dariya Faruk yayi yace "ai babu macen da ta isa ta dubi mon général ta raina sa ina sam hakan ba mai yiyuwa ba ne,ko mu da mu ke Mazan ya mu ka iya balle wata aba wai mace?"murmushi Waleed yayi yace "ɗan iska yau dai ka dawo a matsayin abokina shiyasa har kake gaya min magana son ranka"Faruk yace "eh toh kai ɗin ne akwai wuyar sha'ani dan wani zubin tsoron ka ma ni ke ji"
Kallon shi Waleed yayi yace "shiyasa tun da aka bani kai a matsayin mai min hidima na so na canza ka wlh sam ban son risinawar nan da kake min"Faruk yace "to ya zan yi ?a bakin aikina fah ne"Waleed yace "no banda in mun na gida please ka bari in mun zo nan"kai kawai Faruk ya jinjina kafin ya É—auki kofin da ya shigo da shi ya fita.

Takardun masu son permission ya fara dubawa kusan rabin su duk yayi rejeté dan wasu na neman izinin zuwa wani gun ba tare da babban dalili ba wanda kuma haka rauni ne ko kuma shagala cikin aikin soja.
Ya na gamawa ya tattara takardun ya maida gefe,Faruk ya shigo ya ɗauki takardun ya na cewa "Momy tayi dambun shinkafa tace na faɗa maka ko a kawo ma?"miƙewa yayi yace "no sai dai mu tai can mu ci tunda babu wani aiki ka ga nayi zumunci"da ƴar dariya Faruk yace "ai kuwa"kafin su fito.

***Gao

A gajiye ta ke tafiya cikin yashin da ya tuje sakamakon manyan motocin da suke zaryar wucewa,kallo ɗaya za ka yi mata ka san ta kwaso yunwa da ƙishi yadda jajayen laɓanta suka bushe.
Tafiya ta ke duk illahirin jikinta na motsawa kasancewarta ƴar lukuta mai ƙiba mai manya mazaunai da dukiyar Fulani.Ƙofar ta tura ta na mai shiga gidan bakinta ɗauke da sallama,amsawa Momy tayi ta na duban ƴarta ta tace "Nabeela yau ma ƙasa kika tawo?"a shagwaɓe tace "Eh Momy ba doli nayi tafiyar ƙasa ba ko na samu wannan ƙibar ta rage,dube ni fah ki gani yadda na ke kamar wata Hajiya 😆"dariya Nabeel yayi wanda ya ke can gefe ya na wanke babur ɗin shi yace "Allah kuwa gwara haka shiyasa na bar ɗaukar ki a babur ɗina kar ki fashe min taya"cike da jin haushi ta fara bubuga ƙafafu ta ce "wlh sai na hau kuma koya zan yi ta yadda zan rinƙa hawa in ba ka nan"dakatawa yayi da wankin babur ɗin yace "wai a hakan za ki hau babur?tab ai ina ga ke sai dai mota shiyasa na ke yi maki sha'awar auren mai kuɗi"Momy ta karɓe zancen da cewa "a'a Nabeel kar na kuma jin ka saka mata mummunar aƙida ta sai mai kuɗi Allah ya bata mai kyawawan halaye dai tayi aurenta ta huta"Nabeela tace "amen Momy can wadda ya sake gani sai ya ce mata lukuta"ta faɗa ta na mai buɗe frigo wacce ta ke a waje cikin rumfa,ruwan sanyi ta ɗauko cikin tasa ta sha ta na mai sauke ajiyar zuciya kafin ta shige ciki.

Wanka tayi ta canza kaya zuwa riga t-shirt da zane, kitchen ta shiga ta zubo abinci ta fara ci.
Chaîne ta canza ta kamo Tauraruwa tv inda suke haska wani Film na sojoji,cike da jin daɗi ta sauka ƙasa ta na mai ƙara volume.
Nabeel ya shigo ya zauna kan kujera mai zaman mutum ɗaya yace "albishirin ki?"ba tare da ta juyo ba tace "goro" hararta yayi yace "a hakan zan gaya maki albishir ɗin kin wani ƙurawa tv ido?"juyowa tayi ta fuskance sa tace "to ina jin ka"
Sai da yayi wani murmushi sannan yace "jiya Faruk ya kira ni zuwa compagnie ɗin su ai kuwa na ga mutumen ki"da sauri tace "wa?mon général ?"dariya ya sheƙe da ita har da riƙe ciki ita kuwa taji haushi ta kai masa duka tureta yayi ya ta faɗi ai kuwa ta taso ta jibge sa shi ma da yaji haushi ya sharara mata mari plate ɗin da ta ci abinci ta buga masa ta yo waje a guje ta na ihu ta na kiran sunan Momy idonta duk sun rufe saboda hawayen da suke zuba,gijibbb taji ta gabji wani ƙaton abu tayi tangal-tangal za ta faɗi kuma taji an taro ta....
[18/12 à 13:32] Mrs SADAUKI 💫: *TUZURU*🙊
```Love
and
romantic story```

```MRS SADAUKI 💫✍🏻```

☀️ *FIRST CLASS WRITERS ASSOCIATIONS ☀️*

_______________________

*PAGE 3&4*

"Ya Salam !Waleed ya furta jin dukiyar Fulaninta bisa fafafaɗan ƙirjinsa kuma alamu sun nuna ba ta saka bra ba ta yadda har yaji taushin su sun shiga ƙirjinsa sun ratsa ɓargon sa.
Cikin yanayin ruɗu da tsoro ta ɗan buɗe idonta sai ta ga kakin soja kawai sai ta ƙara shigewa jikin sa ta na cewa "Ya Faruk ka cece ni wlh duka na zai yi"ta fashe da kuka saboda zafin marin har yanzu bai sake ta "Innalillahi wa'inna iley raji'un"kawai Waleed ke maimaitawa a zuci duk ta ruƙunƙumesa hakan ya sakar masa kasalar da ya kasa taɓuka komi balle yayi ƙoƙarin cireta daga jikinsa.
Nabeel kuwa ya na can ɗaki dafe da goshi ya na fitar da jini shiyasa ma bai biyota ba,wani irin fincikota Faruk yayi daga jikin Waleed ya na cewa "ke ba ki da hankali général ɗin ne kika cakume haka"jin muryar Faruk ya na ambaton général yasa kukanta tsayawa cak ta na mai waro ido kallo ɗaya Waleed yayi mata ya ɗauke kai ya na mai shiga falon dama can Faruk yace ya wuce kafin ya shaidawa Momy zuwan su wacce ta ke ɗakin Abba ta na gyara.
Chapter 1 · 0% Book details