← Book details Tarkon So Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 6

Sashe 4

Tarkon So Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yarda kamar wacce? Bayan Ni na amince dashi haka gidanmu, Abid bashida wani mugun hali ko makusa kedai Kawai saboda Unlce Hamza kike aikata hakan, kuma ni babu Unlce Hamza araina kuma bazai taɓa samun gurbi ba domin Abid ya gama mamaye komai a raina babu sauran wani gurbi dazan iya bawa Wani dakinsan yarda nakesonsa da bazaki dinga kawomin irin waɗannan kalaman ba, ƙofa buɗe take aike zaki iya Auran Unlce Hamza ɗin, Mtsww bazaki bar mutum da damuwarsa ba tunda ba tayani damuwar Zakiyi ba amma kike Neman ɓatamun raina a banza,"
Barin wurin tayi tana masifa da cigaba da gwada kiran Abid ɗin,

Sam bataji haushi ba tamata uzuri domin ta fahimce tana cikin *TARKON SO!*

Harsuka gama bikin babu Labarin Abid hakan yasa takoma gida sukuku

Koda mutane suka soma Zuwa dan Already baba yayi gayya kan za'azo Neman Auranta duk ƴan'uwa sun hallara amma Shuru number sa Kuwa taƙi shiga

"Suhana anya kuwa yaron nan baishirya Walaƙantamu bane a idan duniya gadai mutane amma Shuru shi babu ko alamansa balle ƴan'uwasa"

Cikin tsananin damuwa domin tafi kowa Shiga tashin hankali tace: "A'a baba kumasa zato Maikyau bana tunanin zaiyi hakan Matsayin yaudara domin yana sona kuma Bama hakan yake ba ni tsorona ma Allah yasa wani abin baisameshi ba,"

"Ke dallah rufewa mutane baki Saikace gareki aka soma soyayya idan ba mayaudarin bane meyasa shi ba'asamun wayarsa kuma babu ko ɗaya daga dangin nasa, kaga bukar kawai kaje ka sallame kowa kace suyi haƙuri yaron ya kira kan wani uzurin Rashin lafiya ya kama babbansa abari sai wani lokacin zasuzo," cewar inna Hure

Miƙewa Suhana tayi takoma ɗaki tana cigaba da gwada kiransa amma bata zuwa hakan yasa tarushe da kuka sam takasa yarda da cewar Abid zai shirya mata hakan matsayin yaudara

Shigowa Amana tayi ɗakin tasoma lallashinta,

Baba kuwa cikin nauyi da kunya dakuma baƙincikin ya sallame mutane dole ya dawo cikin gidan cikeda baƙin Cikin maidasa ƙaramin mutum da wanann Yaron yayi

Haka mutane suka watse kowa da Abinda yake Faɗi wasu naganin dama ai Ƙarya ce ina ɗan talaka damai Kuɗi zasu haɗu? Wasu na faɗin ƙwaɗayi ne yakaisu nan kowa dai da abinda yake faɗa,

Sauran dangin haka suka watse masu jimami da gulma duka sunayi kusan ko runtsawa batayi ba tayi kuka sosai har zazzaɓi ya saukar mata harzuwa lokacin kuma taƙi ta yarda cewar Abid mayaudari ne yajefata *TARKON SO!*

Zuwa safiya kuwa jikin ya matsa mata dole Sukayi asibiti magunguna akabata da allurai dakuma faɗan cire damuwa domin damuwace ke neman taɓa zuciyarta Zuwa tunanin ta

Bayan bata shawarwari da dokokin kiyaye lafiyarta ya basu sallama suka koma gida, sosai baba da umma Sukayi mata faɗan Cire wannan abun aranta amma takasa saboda tana sonsa sosai tagama faɗawa *TARKON SO!*

Ganin abun natadai yaƙi sauƙi Inna Hure tamaidata gidanta saidai babu wani cigaba,

A ɓangaren Abid Kuwa a daren aka kwaɓarsa tayi Ruwa domin Kuwa ɗaya daga cikin ƴanmatansa aka taso da Yaro kan cewar shine Ubansa abinda yayi masifar ƙona ran Daddy kenan yasa yace ranar dole ya dawo gida batareda yasan meke faruwa ba, dole yabari sai zuwa safiya jirginsa yatashi da safen yana hanyar barin airport yaga kiranta ganin taƙi daina kiransa ya kashe wayar duka daga bisani kuma yacire layukan yana jan tsaki ta watsar dasu,

Koda ya koma gida ganin abinda yake faruwa yaso ɗaga masa hankali amma dayake shi ɗan barikine ya kafe kan Ƙarya suke masa, akace ayi gwajin DNA Siye likitan yayi yabada wani result daban daga ƙarshe dai dole suka haƙura dacewar ɗansa, wanann dalilin yasa Daddy yace dole saiyayi aure, Shikuma bai shirya Auren yanzu ba domin baigama sheƙe ayarsa ba yabar ƙasar yakoma Malesia can ya ƙarasa sheƙe ayarsa Cikin turawa.

Kwanakin sunja har kimanin wata 8 kenan harzuwa lokacin Suhana takasa dawowa normal kullum Cikin saka ran ganin dawowar Abid gareta take amma Shuru ciwonta kuwa yana ƙara tsananta, dole inna Hure tamaidata gida ranar suna Zaune tayi Shuru kamaryarda tasaba, wani yaro yashigo yace ana sallama da Suhana,

"Waye" cewar Umma

"Yace TY ne Abokin Abid,"

Da Sauri Suhana tawaiga ta kalle yaron tana ƙoƙarin Miƙewa umma ta riƙeta tace kaje kace ya shigo,"

Kiran baba tayi dama banesa yakeba yazo kusanma tare suka shigo

A mutunce TY yagaidasu

Cikin damuwa da nuna farincikin ganin TY tace: "Ina Abid ɗina yana nan ko? Kagaya musu Abid ba mayaudari bane Domin yana sona nima ina sonshi, TY ka ƙaryata abinda mutane suke cewar wai ƙwaɗayin Abin duniya nake, TY ka ƙaryata cewar Abid ba Samarin Shaho bane baisakani a *TARKON SO!* ba,"

Ganin duk yarda tawani fita hayyacinta yasaka Yasoma hawaye

"TY ya mutun ne,"?

"Kaga yaro faɗamuna meke faruwa meke tafe dakai,"? Cewar baba

"Baba kuyi haƙuri ku yafemun banyi daniyar cuta ba wallahi bansan niyar Abid bamai Kyau bace, dama ba son Suhana na tsakani da Allah yakeba kawai yayi Amfani da itane domin cika wani buri nasa, kuma," duk Abinda Abid ɗin Yadaɗa na nufinsa kan Suhana ya faɗa musu yana hawaye

Shaƙe wayan rigarsa tayi cikin wani yanayi tace: "ƙarya kake Sam Abid bazai aikata hakan gareni ba Ƙarya ne wallahi Ƙarya kakeyi,"

Janyota mama tayi baba daka mata tsawa

"Kinatsu Sunana Saikace gareki aka fara yaudaran ko nine ko mamanki tamutu ai iyakar tashin hankalin da zaki nuna balle wai dan saurayi ya yaudareki kidawo hayyacinki,"

"Baba kabarta Abunda ciwo ace wanda ka yarda dashi shine zaicuceka amma wallahi Suhana gaskiya nake gaya miki wannan dalilin yarabani dashi amma kalli kiga wallahi Abid ba mutumin kirki bane,"
Bata wayarsa yayi photonan Abid suka Bayyana yana rungume da wata baturiya photona kala kala An ɗaukesu wasu suna kissing juna wasu suna rungume,

"Waɗannan photonan ba Editing bane shine dakansa yayi posting ɗinsu yana shirin Aure da ita ne"

Cikin tashin hankali take kallon photonan tabbas Abid ne kenan da gaske yajefata *TARKON SO!* Kuma ya Aure wata ba itaba ashe dama haka soyayya da mazan suke,

Ƙara tasaki tareda sakin wayar ta Faɗi ƙasa.

Cikin tashin hankali sukayi kanta, Ruwa suka yayyafa mata amma bata dawo hayyacinta ba hakan yasa dole sukayi Asibiti da ita,

Ganin Irin yarda ciwon nata yakai yatada hankalin likita domin Kuwa takamu da ciwon damuna Depression mai tsanani wanda yanzu yana fatan ciwon baikai ga ƙwaƙwalwarta saita farka zasu tabbatar idan kuwa yakai to shakka babu Suhana ta haukace,

Kuka Umma take sosai da tsinewa Abid,

Nanne likitan yasamu labarin duk kan wannan guy ne daya kawota Asibitin shikanshi yajinjina yaudara irin tawasu mazan,

Harzuwa dare bata falka ba hakan yasa baba ya koma gida Mama ce Kawai tarage Bacci ɓarawo ne yasace ta wanda cikin daren Suhana ta farka, cikin mugun yanayi na gushewar hankali fishe ƙarin ruwan tayi jini yana zuba bako takalmi Ƙafarta kanta babu ɗan kwali tafice, batasan inda tadosa ba tafiya Kawai takeyi tana ƙarawa da gudu,.

Sai zuwa Assuba mama tafalka saidai me? Babu suhana balle labarinta hankali tashe taje gurin likitan aka soma nemanta amma Shuru CCTV aka duba can aka hangeta tafice,

"Tabbas hasashena yazama gaskiya Suhana ta haukace"

Ƙara mama tasaki tareda faɗuwa, taimakon gaggawa akabata, zuwansu baba yasa suka fita nemanta harda gurin ƴansanda amma Shuru tun suna karai har suka fidda

Suhana kuwa mota tagani aje ta itace Kawai tashige bayan batareda kowa yasani ba, driver yana Zuwa yaja motarsa yanufe Abuja yabar kano.............................

_*(MRS_MLM GRAPHIX & NOVELS ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 💥 ✨ 💥 07064904617)*_

Whatsapp number 07064904617 or 07031012948

*TARKON SO!*
_PAID BOOK ₦400 ONLY_

*_LOVE, BETRAYAL, DEPRESSION & SYMPATHY ALL IN TARKON SO!!!_*

_Labari maid'auke da darasin Rayuwa, fad'akarwa ilimantarwa, dama Wa'azantarwa, gamida nishad'antarwa_

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

(MRS_MLM GRAPHIX & NOVELS ALƘALAMI DA FASAHA STUDIO 💥 ✨ 💥)

```MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA..... And Other's BUT NOW (18) SAURAYINA.. (19)D.S.P ANNUR PAID BOOK....(20) SAKACINA PAID BOOK.... (21) SO!!! FREE BOOK... (22) FATALWAR ☠️ BUDURWAR MIJINA PAID BOOK... (23) D'AUKE D'AI D'AI DUNIYAR SHAID'ANU PAID BOOK...(24) RUHIN JINN PAID BOOK.. (25) JAMI'IN SIRRI C~I~D PAID BOOK 300 ONLY.. (26). SANADIN PARTY HORRO STORY..(27) ASHRAF_LOVE 💞STORY....(28) TAWA K'ADDARAR 😢 FREE BOOK..., (29)GUBAR MATSAFA!!! HORROR STORY ☠️💀👹😈... (30)NUR RAINON D'AN FASHI!!! FREE BOOK. (31) ZUCIYA..(32) YARIMA ASHMAN🤴🏻 (THE PRINCE) PAID BOOK 300 ONLY.. (33) SILAR GRADUATION PARTY, HORROR ☠️💀😈👹☠️💀 FREE BOOK. (34) SULTHAN ANEEM🤴👑 PAID BOOK. (35) And know AKAN AIKIN MIJINA🧟👹🧟 FREE BOOK is (36). TANGARAS.... FAD'I KAFASHE PAID BOOK (37). BARRISTER NAZEEYAH PAID BOOK (38).. (39) CAPTAIN AMEESH FREE BOOK....(40) DAREN HANA BACCI ☠️ 💀 ☠️ (41) BARRISTER ARMAN! (42) TARKON SO!
loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 QUEEN OF WRITER 📝```

_Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken_ *TARKON SO!*
PAID BOOK ₦400 ONLY

_Ina fatan yabada darussuka dama ilmantarwa Kamar dai yarda sauran littafaina suka bayar....._
Chapter 4 · 0% Book details