← Book details Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 8

Sashe 5

Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

'Yar mutan
Arkilla
____________
Zaku iya samun littafan mu a Facebook
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu
[email protected]
Dedicated to the loved Frnds 'yan uwa abokan aiki:
King Boy Isha
Kamala minna
Bamai A Dabuwa Kkm.
Zaidu Ibrahim. Mr. Zaid
Ramadan Mubarak (Mubson)
Mu gudu tare mu tsira tare. I am proud of you guys. Always
*Page 5*
* * * * *
Hawaye ne na gani fall sun ciko idon baba Malam, kasancewar kansa a sunkuye ya kara bawa hawayen damar surnanowa suka biyo kuncinsa. A take zuciyata ta harba hankalina ya kara tashi. A 6angare
aya kuma naji ina nadama da danasanin tunkarar mahaifina da wannan maganar. Kaico na da wannan rayuwar tawa, tunda na kasa samawa iyayena farin ciki. Gashi yau har na kai ga zama silar zubar hawayen Babana.
Sai na fashe da kuka na karasa ga mahaifina na rungume kafafunshi kasancewar yana zaune ne bisa kujera. Cikin kukan na fara magana "na shiga uku babana ka yafe min, dan Allah ka min aikin gafara. Da na san magana ta zata kona ranka da ban zo maka da ita ba baba. Wannan wace irin rayuwa ce dani? Ina son ku ina son yi muku biyayya baba dan Allah kayi hakuri wlh zan janye wannan kudurin nawa koda kuwa zai zamo sanadin fitar numfashi daga gangar jikina. Baba ka yafe min nayi alkawarin kawar da bukata ta Na rungumi taku bazaka koma zubda hawaye akai na ba, sai dai ko in na mutuwa ta ne."
Ahankali baba ya
ago ni ya zaunar da ni bisa kujerar dake gefensa. Na lura da sauyi sosai a tattare da shi, jikinsa yayi sanyi zuciyarsa ta karaya. Tsawon dakiku babu wanda ya koma yin magana a cikin mu. "Na'eema" baba ya kira suna na cikin sanyi da alamun tausayi a fuskar shi. Ban iya
aga kaina ba saboda wata kunyar mahaifina da nauyin sa da nake ji. Na amsa "na'am baba." baba ya fara magana cikin jimami da mutuwar jiki yace "Na'eema kin tuna min da
an uwana Jamal ne ta dalilin wannan yunkurin da kike yi akan soyayya. Nasan kinada labarin inada
an uwa guda
aya jal a wannan duniyar." yaja numfashi tareda sararawa niko nayi nutso a kogin tunani tabbas inada labarin yayan babanmu mai suna Jamal wanda aka ce ya bar gida tun yana saurayi kuma har yau ba'a koma ganin sa ko jin labarin shi ba.
Tsayawar tunanina yayi dai-dai da cigaba da maganar baba. "na san baki san cikakken tarihin wannan
an uwan nawa ba, baki san bisa dalilin da ya bar gida ba to yau zan gaya miki. Wannan labarin da zan baki shine dalilin mu ni da mahaifiyar ki na hana ki wata masaniya akan maganin cutar wannan bil'adaman da
kike so.
Na tabbatar koda ke ce a matsayin mu irin matakin da zaki
auka kenan." baba ya sarara kafin ya fara bani labarin yayansa wato babana Jamal wanda labarinsa kawai na sani ban san shi ba.
"Kamar yadda kika da
e kina ji Jamal yayana ne uwa
aya uba
aya, wanda mu ka
ai ne Allah ya azurta iyayenmu da haihuwa. Ba tare aka haife mu da Jamal ba, amma muna da matukar kama. Kasancewar ba wata tsera ce tsakaninmu ba yasa nayi kusa iso shi a girma. Hakan ne yasa da yawa idan suka ganni sai su
auka Jamal
in ne, gurare da dama nakan amsa sunan shi ga duk wanda ya kira ni da shi. Saboda son da muke wa juna yasa ko kaya za'a yi mana sai iri
aya muke sakawa. Haka muka taso har zuwa girman mu. Inda a nan ne mummunan lamarin ya afku."
Baba yai shiru yana share hawaye cikin tsantsan kunan rai ya ci gaba... "soyayya!" ya fa
a da karfi da kuma nauyin gaske. Kafin ya
ora "soyayya da kike gani abu ce mai matukar hatsari Na'eema, wata irin rikitacciyar soyayya ce ta 6alle tsakanin yayana Jamal da wata gimbiya 'yar sarkin birnin Durgas mai suna Sunita. Sunita ta kasance kyakkyawa ta gaban kwatance wadda masu ittafaki sun fa
a a wannan zamanin babu wata kyakkyawa kamarta a duk fa
in nahiyar nan.
an uwana Jamal ya mace sosai akan son Sunita wadda tunda take bata ta6a jin murya ta wani ko wata ko kuma wani sauti a duniya ba.
Hakan kuwa ya samo asali ne ga kasancewarta kurma, da cutar aka haife ta. Babu wanda ya ankara da haka har saida ta girma ta kai munzalin yi da kuma jin magana. Sai a lokaci kowa ya fahimta da Sunita kurma ce bata ji daga nan mahaifinta sarki Ashwar ya shiga fafutukar nema mata magani tun yana yi da malamai har ya koma kan bokaye, na ruwa dana tudu. Amma ina biyan bukata ya gagara. A cikin haka ne ya sadu da wani hatsabibin boka wanda ya gaya masa Sunita fa bazata ta6a warkewa ba har sai an
iga mata sihirtaccin ruwan nan na (ma'al dawa'u) wa
anda can binne a tsibirin Darul iks a cikin kunnenta. Ruwan ko yana can bangon duniya ne a karkashin ikon shahararre kuma azzalumin sarkin nan na bakaken she
anu sarki Dawwaz, wanda a wannan duniyar har izuwa yanzu ba'a sami na biyunsa ba a karfin sarrafa miyagun dodanni da she
anu na jinni. Baya ga tsagwaron karfin tsafi dana dantsen da yake da su. Jin hakan yasa mahaifin Sunita sarki Ashwar ya saka wata doka ga manema auren tauraruwar 'yar tasa
Cewa duk mai son ya mallaki Sunita da gaske to ya je ya nemo mata waraka ta hanyar samo mata wannan sihirtaccen ruwan na ma'al dawa'u. Wannan ne yasa duk masu tururuwar neman gimbiyar suka ja da baya saboda sanin
inbin hatsari da masifar dake cikin tafiya nemo wannan ruwan.
Ya kasance babu kowa a manemanta sai yayana Jamal. Saboda shi tashi soyayyar ta sha bam-bam da wadda sauran suke mata. Wato shi son gaskiya yakewa Sunita."
Babana yaja numfashi yana sharar kwalla. Wannan karon hadda ni kukan nake yi domin jin inda soyayyar gaskiya take, kasancewata ma'abociyar soyayya ina son mai maida hankali gareta da kuma bata muhimmanci.
Tunanina ya yanke ne lokacin da naji baba ya numfasa zai ci gaba da bani labarin...
*Nasmat*
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah:
*MARUBUCI...*

*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
_____________________________________
Chapter 5 · 0% Book details