← Book details Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 8

Sashe 3

Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yar'mutan
Arkilla
____________
Zaku iya samun littafan mu a Facebook
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu
[email protected]
*Page 3*
Alaka alaka ce kamar yadda so yake riki
ewa ya zama kauna. *ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION* Na yarda da kaunarku GAREMU. Babu shakka aminci ne mai karfi tsakani mu *ZAMANI WRITERS* daku. Fatan mu a nan Allah ya bar zumunci da kaunar juna. Nasmat da
aukacin members na *ZAMANI* suna yin ku irin totally
in nan, ku huta
*Shamsiyyah Salis* naki daban ne Allah ya kara basira da zakin hannu.
Cikin zafin rai da
acin zuciya "kaicon ka yarima Haiman, shin me ka yiwa wannan zuciyar taka ne da har take ingiza ka take tursasa ka son wadda kake da yakinin cewa bata sonka ba kuma zata ta6a sonka ba?." dama nasan a rina. A madadin Haiman yaji haushin kalamaina sai na tsinci wani lallausan murmushi a kan fuskarshi.
Al'amarin da ya kara zafafa zuciya ta kenan, da har zan koma wurga masa wata mummunar maganar sai zuciyata tayi gaggawar kwa6a ta, tare da yi mini tuni a kan ko wane ne Haiman. Nan da nan sai na sassauta fushina na fara kirkirar abinda na san shi ka
ai ne zai sa Haiman ya saurare ni kan wannan batu. Kuka na fara yi ina zubda hawaye. Ai kuwa da sauri Haiman ya tashi daga kishingi
ar da yayi ya zauna da kyau ya fuskance ni, cikin tsananin ru
ani.
Dama na sani idan kalamaina basu ru
a shi ba kukana zai nutsar da shi. Sai ya shiga magiya yana roko na a kan in taimaka in daina kukan nan zai fahimce ni. Ni kaina ina mamakin tashin hankalin da Haiman ke shiga idan ya ga zubar hawaye na wannan shi ne dalilin da yake sawa na yarda cewa Haiman *son gaskiya* yake yi mini. Amma fa sanin hakan bai ta6a sawa na ji tausayinsa ko da na rana
aya ba, wannan ne yake tabbatar min cewa bana son Haiman ba Kuna zan ta6a sonsa ba.
Na kalli yadda hankalin jarumin
an sarkin ya tashi saboda ganin zubar hawayena. Tabbas so na musamman ne, duk wanda kaga bai girmama so ba to bai tsinci kansa a ciki bane.
"Haiman" na kira sunansa cikin muryar kuka. Ya amsa idanunshi da nutsuwarshi duk suna gareni. "Haiman wallahi bana sonka, ba kuma na tunanin zan so ka koda a gaba ne. Ban san ya zan yiwa zuciyata ta so ka ba da nayi Haiman. Dan Allah ka taimake ni ka bar ni, ina da wanda nake so. Muhsin shi ka
ai zuciyata ta yarda da shi a matsayin masoyi ka taimaka min yarima." na tashi na tsuguna a gabanshi ina ko'karin kama kafafunshi.
Wani irin zafin kishi ne ya daki zuciyar Haiman ya mike tsaye hannunsa dafe da kirjinsa ya juya min baya. A lokaci
aya wani zazzafan gumi ya fara yanko masa ta ko'ina a jikinsa. "ki yi hakuri Na'eema tsakanin zuciyata da taki da akwai wata dangantaka mai karfi wadda na tabbata kema da sannu zaki santa, kuma kema zaki fara so na a lokacin da wannan dangantakar ta bayyana ga taki zuciyar. Ina son ki Na'eema ba zan iya rabuwa da ke ba. Zan iya zama dake koda bakya so na, zan jira zuciyarki har sai ta so ni koda kuwa lokacin zai kai ga lokacin tsufana ne, zan kasance mijinki har zuwa lokacin. Ni kam ba zan iya rabuwa dake ba. Zan aure ki in kuma baki dama ki ci gaba da zama a gidana har zuwa lokacin da zaki so ni. Zan zama bawa gareki Na'eema ina ji a raina saboda ke kawai aka halicce ni, na yarda da so
aya ne tak! Kuma shi nake miki Na'eema."
Yana kawowa nan a zancensa ya bar wurin ba tareda ya koma waiwayen inda nake ba. Wani wahaltaccen kuka ne ya su6uce mini, na shiga rera shi kamar wadda aka ce iyayenta sun cika. Ina cikin kukan ne iyayena suka bayyana a gabana cikin 6acin rai. Na kalle su sau
aya na sunkuyar da kaina. Malam wanda dama a cike yake da takaicina ya fara yi mini fa
a kamar zai dake ni.
"Nikam ban san yadda kike so ki maida ni ba Na'eema, da na
auka haukar da kike na son Bil'adama kuruciya ce sai gashi abin naki sai gaba-gaba yake, shin me kika maida kan ki ne? Ko dai bakida hankali ne Na'eema? Banda shi a ina kika ta6a ganin an ha
a auren Bil'adama da Aljan? Koko haka kike tunanin zamu zuba miki ido ki kare rayuwarki ta har abada babu aure kina bin bayan Bil'adama?."
Ummy ta kar6i maganar da cewa "Wata kila a kanta za'a fara, banza mara hankali to wallahi tun wuri ki nutsu ki dawo hayyacinki maganar aure babu fashi kuma nan kusa bada nisa ba." a tare suka 6ace rayukansu a 6ace. Hankalina ya koma tashi damuwata ta koma ninkuwa ko ka
an bana son ran iyayena yana 6aci ta dalilina, na shiga uku ni Na'eema ya zan yi da rayuwata?.
Sai na koma fashewa da Kuka na fa
i kwance bisa shimfi
ar nan ina ayyanawa a raina cewa inama mutuwa zata zo ta
auke ni da na huta bakin ciki da kallon kaina a matsayin matar wanin da ba Muhsin
ina ba.
*Nasmat*
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah:
*MARUBUCI...*

*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
_____________________________________
Chapter 3 · 0% Book details