Sashe 4
Soyyayar Mutun Da Aljan Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Yar'mutan
Arkilla
____________
Zaku iya samun littafan mu a Facebook
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu
[email protected]
*Page 4*
Wannan shafin ga baki
ayansa sadaukarwa ne gareki kawar kirki. *QUEEN HAFSY* aminta ta da ke ta musamman ce, ina yi miki barka da dawowa tawan Allah ya bar zumunci da kaunar juna.
Lokaci mai tsayi na
auka ina wannan kukan ganin babu abinda zai kare ni da shi yasa dole na hakura na rarrashi kaina na mike na nufi
akina.
Duk tsananin da nake ciki sai da naji saukar ni'ima da sanyi a zuciyata, lokacin da idanuwana sukayi tozali da manya-manyan hotuna na zanen fuskar farin ganina Muhsin. Wa
anda ke makale a kowace kusarwa ta
akin. Duk da ba can na nufa ba amma sai naji zuciyata ta jagoranci gangar jikina ta jani zuwa gaban hoton. Na tsaya kikam ina karewa Muhsin kallo wanda yake zaune da kayan aikinsa wato littafi da Alkalami yana son fara rubutu. Nice na zana wannan da hannuna saboda babu inda Muhsin yake min kyan gani kamar in gan shi a karkashin bishiyar nan yana gwada fasaharsa ta rubutu.
Na shafi fuskarsa ta jikin hoton na fara magana cikin shaukin so dan a lokacin ji nake kamar Muhsin
in ne a gabana. "Muhsin kasan ina sonka ina kuma kaunarka. Amma gashi ra'ayi na yasha bam-bam dana iyayena. Muhsin bazan iya bijirewa iyayena ba, kamar yadda nake ji bazan iya rabuwa da kai ba. Ya kai masoyina hakika rayuwata tana cikin hatsari, wanda ni kaina ban san makomarta ba. Sai dai ina da buri a kan ka Muhsin. Koda ace ban aure ka ba, ban kuma kasance da kai ba, na so ace na cika maka babban burinka ta yadda har abada zan kafa hujja a zuciyata cewa na taimaki masoyina wajen zama abinda yake so ya zama. Muhsin in dai ban sami ko
aya daga cikin wa
annan ba zan iya mutuwa."
Na kifa kaina jikin hoton ina zubda hawaye. Can na
ago kai na sumbace shi sannan na shiga tunaninsa shin ya tashi daga bacci ya tafi gida ko dai yana nan 'fadarsa'? Karkashin bishiyar nan nake nufi domin nan ne fadar masoyina.
Nan da nan sai naji zuciyata ta kwa
aitu da son koma ganin fuskarsa. Juyi
aya nayi na 6ata sai gani na bayyana karkashin bishiyar nan Amma ban sami Muhsin ba. Wannan yana nufin ya tashi kenan. Ban jira komai ba na nufi gidansu. Kai tsaye
akinsa na bayyana nan ma wayam baya nan. Hakan bai sanyayar min guiwa ba na koma 6acewa sai
akin mahaifiyarsa gimbiya Suhaima. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke nan da nan fuskata ta wadatu da kawataccen murmushina. Badan komai ba sai dan ganin zumar rayuwata Muhsin. Yana kwance bisa wani lallausan kilishi wanda ke shimfi
e a faffa
a kuma kawataccen
akin. Yayi matashin kai da cinyar mahaifiyar tashi tana shafa kansa. farar mace mai farar zuciya.
Can na sami wuri na zauna gefen su ina kallon su kuma ina sauraron maganarsu gwanin sha'awa. Muhsin ya kalli mahaifiyarsa yace "yake ummana shin wai ni babu wata hanya za zan bi in samo maganin wannan lalurar dake damuna?" hawaye ne suka cicciko idon Suhaima, tayi saurin share su tun kafin su fito. Sannan ta kalli
an nata mafi soyuwa a cikin zuciyarta tace "koda akwai ta banida sani a kan ta Muhsin, ni kaina da ace na san wata hanya ta samun warakar ka wallahi da na bita na samo maka koda ko zan rasa rayuwata ne." da sauri Muhsin ya kai hannunsa ya rufe bakin ummansa "a'a mahaifiyata, da dai ki mutu kam gwara na tabbata dakiki in yi ta zama a haka har karshen rayuwata." Suhaima ta koma share hawaye tace "kawai dai babu ne
ana amma wlh da babu abinda zai hana ni binta, Muhsin ina son ganin cikar burin nan naka, ina son ganin ka zama cikakken *MARUBUCI* Amma ban san ta yadda hakan zai kasance ba."
Wata kasalalliyar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace "inaga hakan ba zai ta6a yuwuwa bane, inaga ba zan ta6a zama bane wannan shi ne dalilin da yasa Allah ya toshe min kwakwalwa. Amma kam ina son Rubutu Ummana."
Ba umman Muhsin ba ni kaina saida hawayen tausayinsa suka zubo mini. Ta rungume shi cikeda so da tausayinsa "zaka zama
ana, insha Allahu wata rana zaka zama." gaba
aya
a da uwar kuka suke yi wannan shine abinda ya kara zaburar da zuciyata kuka nake sosai ina tunani shin ta wace hanya zan iya taimakon Muhsin? Tabbas ya kamata ya zama amma ta yaya?.
6acewa nayi daga
akin gimbiya na bayyana gidanmu. A wannan lokacin na gama yanke hukunci babu tsoro ko fargaba a tattareda ni. Na tabbata wannan ita ce damata ta samun abinda nake so daga gare su. Ganin babu kowa a mazaunin mai kama da fada yasa na kutsa kaina izuwa
akin baba Malam na shiga da sallama.
Yana kishingi
e bisa abin sallarsa ya amsa mini sallamar fuskarshi na kallon wani wurin daban. Hakan ya tabbatar mini cewa har yanzu mahaifina fushi yake dani. Na tsuguna
an nesa ka
an da inda yake zaune. Nace "dan Allah baba kayi hakuri, ka sani sarai bana kaunar duk wani abu da zai zo ya 6ata min ranku kaida ummyna." nayi shiru ko zai ce wani abu amma baba bai ce komai ba. Hakan yasa na kara
orawa. "Baba dan Allah ina rokon wata alfarma daga gare ka, na yarda da za6in ku zan auri Haiman zan kuma so shi. Amma ni kuma ina bukatar ku cika mini burina kafin wannan auren." sai a lokaci baba ya
ago ya kalle ni fuskarsa
auke da murmushi "dama nace ko canja min ke aka yi ne? Domin ni a nawa sanin Na'eema na bata tsallake umarnina balle ta kai ga bijire mini." "ai har abada ba zan ta6a bijirewa umarninka ba baba." na koma fa
a cike da biyayya da nuna ya isa da ni. Mahaifina ya ji da
in wannan maganar dan sai da ya tashi daga kishingi
en da yake ya zauna yana fuskanta ta. Na saci kallon fuskarshi sai na ganta
auke da murmushi nima murmushin nayi bakina
auke da addu'ar Allah ya taimake ni yasa yau in sami nasara kan mahaifina.
Babana ya katse mini tunani da tambaya. "Mene ne wannan burin naki da kike son cikawa kafin aurenki da Haiman Na'eema?" duk yadda naji na dake d'azu sai da nayi jim ka
an ina tunanin makomar abinda zan fa
a. Na sake jin muryar baba yana fa
in kar kiji tsoron fa
a min ko mene ne ya' ta, tabbas zan yi miki adalci. Na lura babana ya kagu yaji mene ne burina wanda cika min shi zai sa in kar6i auren mijin da nayi ikirarin bana son sa.
Kaina na sunkuye a kasa na fara magana. "baba, nasan matsayin saninka da yawan shekarunka mawuyacin abune ace bakada masaniya a kan maganin lalurar nan ta Muhsin da na da
e ina gaya muku. Baba ka dubi Allah da girmansa, ka dubi darajar Ma'aiki (s.a.w) sannan ka dubi daraja da karfin soyayya ka taimake ni in dai har kanada masaniya akan abinda nake tambayar ka baba ka gaya mini. Kar kaji shayin sanar min ko mene ne, idan har na samawa Muhsin waraka ya sami cikar burinsa ta dalilina to zuciyata zata sami nutsuwa zan kuma yi alfahari da soyayyata domin na taimaki wanda nake so. Sannan cikin kwanciyar hankali zan amshi auren za6in ku."
Shirun da naji babana yayi ne yasa na
ago kaina dan ganin makomar magana ta. Ai kuwa abinda naci karo da shi ya yi matukar Razana ni ya kuma tashi hankalina...
*Nasmat*
[23/1 17:53] Yar Mutan Arkillah:
*MARUBUCI...*
*Soyayyar Mutum da Aljan...* kagaggen labari.
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________