← Book details So Babbar Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 8

Sashe 5

So Babbar Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Sultan yana fita gida yai, kansa ya d'auki charge yarasa yadda zaiyi, shima sunson saka shi cikin matsala tunda dukkan su jinin sane bazai Iya ganin d'aya yan acikin matsala ba ya zauna dole saiya shiga damuwa shima
D'akin sa tafi shower ya sakarwa kansa ya dad'e yana tunanin mafita amma ina yakasa hangowa haryanzu baiga hasken hanyar warware matsalan ba
Yaya Saleema ko zata mutu bazata iya furta cewa tanason Deen ba, Deen shima yaji yagani da idonsa kunya da nauyi da kuma ganin kamar Saleema tafi k'arfin sa shima bazai iya furta Kalmar SO gareta ba ya za'ayi kenan
Haka ya fito tareda alwalar sa ya jima yana Addu'a, kafin yatashi yatafi d'akin Yaya Saleema
Itada Mama yagansu ta d'ora kanta a cinyar Mama. Yauwa Sultan zo narasa gane kan Saleema kwana biyu tazama wata iri, yanzu magana nake mata akan meke damunta amma tak'i, nayi nayi da ita zo kai kozata gaya maka
Tsugunawa yai, akan rug dake cikin d'akin, hannunta ya kamo yace Mama nima na tambayeta tak'i gayan, amma ni ina tunanin ko exam d'in da tayine taci CO shine take damuwa kada mugani dan naji ance tafito
Da sauri ta tashi tana murgud'a baki tace Lallai yaro CO yayi hannun riga da Saleema, wuce nan fever ke damuna amma Idan naci CO aina banu
Ko Mama ta Idan Autarki taci CO aiba kanta, kut wace yar Autar amma kin yanken ina zaune dan kin ganki jikin Mama shine zakici Auta
Matsama ni tashi daga kanta, wallahi bazan tashi ba, kalle shi wani gardi dashi, kafin me ta ware sun fara hayaniya can kuma Sai hira Mama tashi tai ta barsu taiwa kowa asubah tagari
Yana sane yace mata haka, danta ware gashi Allah yabashi sa'a damuwa ta tafi, shima mik'ewa yayi Yaya Saleema da alheri zan gudu inason yin karatu kinsan exam next week inajin campus zan koma ma, naga Idan ina nan bazaki barni nayi wani abin kirki ba
Aikin ki ya ishan ma. Allah bazan saka ba, Plx Ka taimakan ka zauna rashinka wani gib'i ne arayuwa kaji
Tom, amma Idan naganki cikin damuwa na tambaye ki baki gayan ba, saina tafi
Naji na yadda, sallama sukai itakuma ta janyo bargo tashiga ciki tafara sana'ar wato tunanin Deen
1:30 na dare Deen ya farka, wayar sa ya duba yaga time, lallai yayi bacci. Text din da aka turo, ya duba Sultan ne, da sauri ya karanta, baki ya washe yafara copying numbers d'in yana alhamdulillah
Dialling number yafara, tunani yai to yace mata me?, kuma dare yai, anya zata kulashi kuwa
"Hello" waye cikin dare haka?, maganarta ita tadawo dashi daga duniyar tunanin daya shiga
Ajiyar zuciya ya sauke, cikin kasala da fargaba yace Yaya Saleema nine
Kaiwa?
Deen mana nabugo na gaidaki bansan dare yayi ba, Sai danayi dialling number sannan naga time sorry for disturb
A kwance take amma tanajin yace Deen, saita mik'e zaune fuskarta ta fad'a d'a da murmushi haryanajin sautin murmushin cikin ransa
Ok Deen ya gari, kwana biyu lafiya dai? bata nuna komai ba, Illa basarwa data fara
Wallahi banjin dad'i amma now I'm OK, ya kike Yaya Saleema ya karatu?
"Karatu fyn, yanaka?"
Haka ake so, accounting kake karanta koh? Itace tamasa tambayar
"Eh Yaya inason course d'in sosai tun ina Yaro nakeda burin karanta gashi Allah ya cikamun burina
Koh nikam na tsani aikin bank ko d'aya bai burgeni, dan Yaya Na'eem bayadda zanyi kuma dan kafin nawani girma yayi karatun sa dabazan barshi ba
Zuciyarsa ce yaji tanason kwacewa Yaya Saleema batason mai aikin Bank, Babbar magana
Kanajina koh ni ko aure zanyi bazan auri Banker ba"
Tari ne Yakama shi dababu shiri, kenan Yaya Saleema bazata aureshiba koda yaga yamata
Ina mafita?, babu wata zuciyar tace
Deen sannu kana mura ne? A'a yazo ne tarin kawai
Ni kuma Yaya Saleema banason lowyer saboda sharrin su, ga ha'inci da cin zali, ga k'arya ga rashin gaskiyar su, ni koda zanyi aure ban auran lowyer
Eyee me kace?, lowyer bashida duk abinda ka fad'i yanzu nishinake karanta fa kuma kusan karashe ne yanzu
Kai Yaya Saleema lowyer, da girman ki, lallai ni zan Iya canja course indai wadda nakeson aura bata so, kodan nafaranta mata
Kinga bye ni nafara jin tsoran ki ma, yana magana yana dariya ciki ciki yaji dadin hira da Sweetyn sa, ga muryarta mai sanyi
Deen tsaya kada kayi hanging nata, Kasan me?
Nidai banji bye asubah tagari a hankali ya furta I LOVE U

@ut@r h@jiy@

🎶SO BABBAR CUTA🎶

®NWA

©Zainab Y Hussein

Dedicated to Nafeesat Anker nd Princess Hassy

autarhajiya.WordPress.com

3⃣6⃣to4⃣0⃣
Chapter 5 · 0% Book details