← Book details So Babbar Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 8

Sashe 1

So Babbar Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[11/11 8:03 pm] h@jiy@ Z@in@b ✍🏻💅🏻:

🔰🔶🔰 🔰🔶🔰
*SO Babbar Cuta*
🔰🔶🔰 🔶🔰🔶

*Tambarin NWA*

*Zainab Y Hussein*

*Editor by*
*Yar gayu mai dimple Adda Bena*

*Dedicated to Nafeesat Anker & Princess Hassy*

*Page 1-5*

*{{{ True life story}}}*

Garin Kano garine mai cike da jama'a da unguwanni masu yawa garine na kasuwanci da garine kuma na manyan Malamai da Attajirai cikin Attajiran garin ya had'a da Alhaji Raheem kwangila
Duk wanda yake harkar kwangila ko ta meye yasan Alhaji Raheem da aminin sa Alhaji Abdulazeez, wanda suka taso tare tundaga k'aramar Makaranta har kawo babbar da jami'a
Sun taso cikin aminci da k'aunar juna babu wanda yatab'a jin tsakanin su, kuma kowa zuciya d'aya yake zaune da d'an uwan sa
Tare suke harkar su ta kasuwanci da komai, Iyayen su suma sun kasance Aminan juna ne, suma Allah ya had'a jinin su
Lokaci d'aya sukayi aure, shi Alhaji Raheem a Maiduguri ya auro matar sa, macece kyakyawa da sanin yakamata gata da kirki da son jama'a kuma gata da ilimi na addini kowa natane
Alhaji Abdulazeez shi a Yola landa of beauty anan ya auro tasa, itama ta kasance bafulata nace usul tsantsar bafulatana gata da haske sosai, bata da makusa itama tanaji da ilimi kowanne b'angare
Yadda d'ayar keda kirki haka itama take dashi, kowacce dai dai tanada kirkin ta
Yadda mazajen su keda kirki kuma suke zumunci suma haka suke, Kaya wataran ma tare suke d'in ka musu, basuda kyashi kowacce tana kiyaye abinda zaije ya dawo
Alhaji Abdulazeez yaran sa tara maza hudu mata biyar, kuma a yanzu duk ya aurar dasu sai mazan, k'aramin d'ansa shine *Imam Deen* yana son sa matuk'a badan komai ba saidan kasancewarsa sunan Mahaifinsa ne da shi, kuma kaf yaran sa shine yayi kama dashi Illa fari da gashi daya d'ebo na mahaifiyar sa
Kuma gashi yaro kamili nutsatse bashida hayaniya, kuma ga zumunci da sanin yakamata
Alhaji Raheem yaran sa hud'u maza uku mace d'aya, macen itace ta uku tanada k'ani Sultan, *Saleema* kenan yarinya yar gata tanada kirki da hankali batada son hayaniya amma duk da haka batada kyaliya, tana girma ma kowa, ita Saleema yadda Maman ta take haka take kyakyawar gaske ce ga gashin nan na Shuwa Arab akanta kamar gori
Yaran kaf d'in su Kansu a had'e yake, bakajin kan kowa, kuma Makaranta dukkansu tare suke, Driver d'aya shine yake kaisu
Abban *Saleema* yana zaune a unguwar Matan fada, shida iyalansa
Abban *Deen*kuma suna zaune a Lamid'o crescent, kowa unguwar sa daban , amma Idan kagansu kace gida d'aya suke ma, tunda yaran wannan. suna wanccen gidan yaran wanccen gidan suna wannan
Deen da Sultan k'anin *Saleema* abokan junane, sosai tare suke yin komai nasu, ba boyewa juna sirrin juna, *Saleema* ta girmi Sultan da shekara d'aya da rabi amma Idan kaga yadda yake respecting nata kamar irin shekara goma ko biyar ta bashi
*Wannan kenan*

Wata motor ce k'irar Accord sabon yayi naga ta shigo layin, gidan su *Saleema*, a hankali sai kace mai tausayin k'asa ko tayar motar sa, naga yana driving
Har zan wuce nace sainaga Waye wannan gayen ko wace?
Sannu a hankali naga tayi parking a k'ofar gidan su Saleema, bai shiga gate d'in gidan ba anan ya tsaya
K'afar sa d'aya ya fito da ita, wow masha Allah tab lallai dama ance daga k'afa zuwa farce ake gane tsaftar maza shi wannan zan iya cewa 100% ne
K'afarsa kawai abin kallo ne, takalmi ne buffalo bak'i mai d'an yatsa ak'afarsa, dogwayen 'yan yatsun sa na k'afa suka k'arawa takalmin nasa kyau
K'afar sa ja maikyau, farcen sa farare k'al, a around suke, abin sha'awa
Fitowar sa itace tasaka ni saurin kallon waye wannan? *Imam Deen* kenan yaro matashi da baifi shekara 23 ba, yadi ne milk colour ajikin sa sharara dan ga singlet dayasaka fara k'al ta bayyana ajikin sa
ba hula akan sa, sai gashin sa da yasha gyara yana kyalli irin na Fulani Yola
Wayar sace a hannun sa sai tab duka suna rik'e, waya yake dan naga earpiece akunnan sa
Sultan gani nazo, plx kayi sauri we don't have enough time da zamuje Munjibir park mu dawo a time d'in da muke so kaji?
Maganar dana saurara kenan lokacin dana k'arasa wajan sa
Daga d'aya b'angaren naji yace *Deen* I'm coming right now, Yaya *Saleema* tasani aiki, amma ganin fitowa
Ok! ina jira, yana gama fad'a kamar da gayya ya juyo yana wani yatsine fuska
Gayu nace, Allah yayi Hallita *Deen* kyau sai kace mace, Lallai Allah shikeda Ikon sa
Kai yake kad'awa maybe wak'a yake saurara naga bakin sa na motsi

@ut@r h@jiy@👱🏻‍♀💅🏻✍🏻

[12/11 12:27 pm] Z33 @ut@r h@jiy@🐒✍🏻💅🏻:

🔰🔶🔰. 🔰🔶🔰
*So Babbar Cuta*
🔰🔶🔰. 🔰🔶🔰

*Tambarin ®NWA*

*©Zainab Y Hussein*

*Wannan Labarin da gaske ya faru, saidai k'arin da akayi, like their parents ba sukai haka a kud'i, ba dan qarawa labarin armashi akasaka, da wasu gurare da yawa aciki karine irin na marubuci, fatan angane, za'a kuma fahimta*

*Dedicated to Nafeesat Anker & Princess Hassy*

*Page 6-10*

*Deen* kenan, yayi makarantar sa a Musa Iliyasu, ta islamiyya kuma a gwadabe maitasa dayake dukkan su Makaranta d'aya suke
*Saleema* itace kad'ai makarantar ta ta banbanta data kowa
Yayi sauka ta Al Qur'an da kuma sauran littatafai na addini
Bayan k'are makarantar sa yaci gaba a Jami'ar Bayero University Kano, inda yake karantar accounting yana level 200 a yanzu, yana da k'ok'ari sosai
Baya wasa da karatun sa, kullum cikin research yake, ya kware a fannin computer sosai, yana cikin BUK amma yana taking lecture a Kazaure Informatics dake yankin Jigawa Dutse
Bashida buri daya wuce ya ganshi a matsayin Banker, karatun sa yake cikin kwanciyar hankali da kwarewa
Wani lokacin yayun sa dariya suke masa akan wai Marketer zaizama ba wani abu ba yadena Boxing akan shi zaizama accounter
Murmushi yake yace ko security aka bashi kafin yazama accounter yana so
Tare da Sultan suke karatu, amma shi yana karantar Business ne, amma dai tare suke
K'aran bud'e gate din gidan itace tasaka shi juyawa, Sultan ne shima cikin suit ash colour sai takalmi Cover yaci neck til yayi kyau kan nan yasha gyara
Dariya yasa ki yanadaga cikin motar, wow Maza kayi kyau, kaganka kamar wani manager Lallai ka k'ara tsokanoni akan nak'ara k'aimi wajan ganin nazama Banker Malam
Hannu suka tafa, yace dama tsokanarka nakeson guy, yah mutafi koh
Ok let's go, amma fa ka shanyani nayi wajan 30 minutes inaji ran ka fah
Kaidai bari *Yaya Saleema* tasani aikin wanke motor, nayi nayi tace wallahi ni zanyi, bayanda zanyi
Huum, Lallai Yaya Saleema kasan fa wallahi ni bazan gane taba, Bata zuwa ko'ina amma?
Eh to kusan haka, kasan low take karanta so batada lokacin kowa Idan kaga ta zauna hira nine ko Autar hajiya wata cousin sister d'in mu
Itama dan tanada kirki ne, ta maida wannan karatun kamar farilla like u guy
Sultan ni kuma babu abinda natsana Sama da Lawyer wallahi bana sonsu dazaka yadda kabata shawara data canja course, dan baikamace taba
Tab kasan yadda take son course d'in kuwa?, Abba da kansa yake bata hop akan haka ganin shita zab'a, tana level 300 zata canja impossible, badai *Yaya Saleema* ba
Kai ita kuma ta tsani Banker kodan rashin enough time da basuda dashi wajan kula da zumunci matayen su yaran su addinin su, always busy ita shiyasa bata so
Nakamata examples akan ba haka suke ba, ganin dai haka ake musu, tak'i yadda
Waih ita halin ta sai ita, hhhh wallahi kuwa, nikam zanso ganin ta ranar dataje gida bana nan naje FUD wajan Dr A'eesh, amma ta iya girki dan abincin ta mukaci wallahi. Haba? zan maka karya
Ok, naji basaika zubamun wannan Idan naka ba, kamar zakayi kuka ko kana neman....... duka ya kaimasa ahaka suka isa munjibur park party akayi inviting nasu na 'yan Northwest University abokin sune yai graduation
Kirrr wayar sa tafara ringing, kamar ya share saiya duba oh babban oga ne Sultan
Abba kake nufi? Eh Huum shine oga kuma?, to Waye tsaya na d'aga
[12/11 12:55 pm] Z33 @ut@r h@jiy@🐒✍🏻💅🏻: "Hello Abba"
"Hello Son ina kake naga shiru bangan kaba?
" Abba wato ina *BICHI*, jiya naji Mom na magana itada Mama wai *Ya Hajja* batada lafiya d'azu da safe kuma *STYLICH* tamun waya shine muka tafi nida Sultan
Ok *IMAMU* Allah damun daku lafiya agaida ita da Hajiya kafin muzo, OK Abba, amma Plx wannan IMAMUN bansan shi sai abokaina sunji dan Allah
To *IMAM DEEN* haka kake so nace?
Eh Abba, yauwa yanzu kai magana, sallama sukai yana saka masa albarka
Hoo da Abba yasan nan muka tawo aiba kanta, shiyasaka nace muna Bichi, mushiga
Wajene aka keb'e maikyau anan abokan su suke, kowa hannu yafara bawa *Deen* gayen ya had'u matik'a
Kallo kansa ya koma, baran da sukaga yana basarwa ba'a damu ba, shi waya yake yi da Auntyn sa, akan maganar bikin wata cousin nasu Ummulkhairi da za'ayi akan gudummawar me za'a bayar
Yammata kowacce shawagi tafara tana son kula sa amma ba fuska ya iya jan class guy d'in, shi dai baya kula yammata badan komai ba saidon shi baya da ra'ayin aure yanzu kuma karatun sa bai buk'atar haushi ni, Idan kuma kaganshi cikin family nasa bakace Deen bane yana bajewa ayi hira aci waina da rake
Sultan dariya ce tasa, ganin yadda dramar take kasance wa, haka suka zauna drinks suka sha ba'a gama ba sukayi sallama suka juya
Sultan dai saidaya bawa wata number na Deen ganin yadda ada take gayu amma ganin sa yasaka ta hauka cewa
Basu tsaya koina ba, sai gida sultan ya ajiye shima ya juya lokaci yayi nisa 8:00 so gara ya koma Abba zai iya fad'a

@ut@r h@jiy@💅🏻🐒

🔰🔶🔰. 🔰🔶🔰
So Babbar Cuta
🔶🔰🔶. 🔰🔶🔰

Tambarin ®NWA

Zainab Y Hussein

Dedicated to Nafeesat Anker &Princess Hassy

Page 11-15
Chapter 1 · 0% Book details