← Book details So Babbar Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 8

Sashe 4

So Babbar Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Lokaci na tafiya, tsakanin Saleema da Deen sun tantance suna son juna, amma babu wanda yake nunawa wani kuma shima anasa b'angaren yana tausaya wa kansa nason wadda tafishi, kuma irin su Saleema sai manya
Babbar rashin kunya itace Yayar abokin sa, shi ya zaiyi bashida mafita zuciyar sa itace bata masa adalci ba, yanaji Saleema kamar itace rayuwar sa taya zai iya tunkarar ta ya furta mata kalmar So, lallai ya amince da ake cewa SO BABBAR CUTA, yakasa ci yakasa sha yakasa walwala duk akan zulumin meyasa So zaimasa haka? kuma wa zaigayawa yana son Saleema
Sultan ya lura yanada damuwa sosai, amma duk Iya tambayar daya masa yak'i gayamasa komai, har fad'a sukai akan haka amma yak'i, yace yanason Yaya Saleema ko me? Impossible sultan zai ce ya rainasa duk da ya girmi sultan, Saleema itace kusan sa'ar shi amma da Sultan yake shiri sosai
Yau da yamma wanka yayi akan zaije yaga Masoyiyar sa, ko yaji dad'i ya kwana biyu baisata Idon saba
Piltos yasaka sky blue yakawo hula da takalmi ga agogon sa sky blue suma, yayi kyau turare kala kala ya shafa kana ya d'akko motar sa pormatic ruwan zuma ya tafi sai Nasarawa matan fada
Lokacin dayaje har cikin gate yakai motar sa, yana murna sosai yafito yashiga cikin harabar gidan
Kamar zai shiga cikin gidan, kome ya tuna, Sai kawai yayi hanyar garden
Da turaren Yaya Saleema yafara sallama hot ice da kashab al uud, ya lura tana son wannan turaren mai k'amshin strawberry
Da tak'amarsa ya Shiga cak ya tsaya, Saleeman sa da wani yagani, hartana dariya sosai
Dr Aliyu ne yazo, tafitane kawai dan ya d'ebemata kewa amma badan wai tana wani komai akan saba
A hankali jikin sa ya saki, hannu ya dunk'ule yatafi cikin sassarfa zai make Dr, tasan kanayi to mai zakayi? wata zuciya ce tafada masa haka
Hawaye ya goge ya juya da gudu ya fita, sun bashi baya so su basu lura da wanzuwar wani awajen ba
Iska datake kad'a wa ita ta d'ebomata k'amshin turaren Deen nata so surprise Deen yazo waige waige tafara kozata gansa amma ko kyallin sa Bata gani ba
Sultan yana bolcony yaga duk wani action da movement na Aliyu ya fuskanci komai shiru yayi kawai
ganin ya fito da gudu yasaka ya kwalla masa kira DEEEN amma ina yarigada yashiga haryamata key
Jin sunan Deen da aka anbata, yasa ta tashi da gudu tafita k'uran motarsa tagani
Daidai lokacin Sultan ya k'araso, wani kallo ya watsamata baran dayaga Dr ya fito
Sultan lafiya Deen yazo naji k'amshin turaren sa, kuma..
Kuma me aike kika Kore...... Kome ya tuna saiyayi shiru kawai yashige gida da gudu ta bisa tamanta da wani Dr tanaso taji labarin Deen me akayi masa ko me ya faru

Kubiyo Autar Hajiya dai kuji yazata kaya, cikin So Babbar Cuta

autarhajiya.WordPress.com

🎶SO BABBAR CUTA🎶

®NWA

©Zainab Y Hussein
autarhajiya.WordPress.com
Dedicated to Nafeesat Anker & princess Hassy

2⃣6⃣to3⃣0⃣

Da wani mahaukacin gudu ya k'arasa gida, horn yake da k'arfi har saidaya tsorata gate man d'in nasu, da sauri yazo ya bud'e
Ko gama parking baiyi ba, yafito da sauri, d'akin sa yayi, Allah yasa ba kowa a parlour d'in bare a tambaye shi.
D'akin sa yai kansa ya dafe wani d'aci yakeji a mak'ogwaran sa, ga kansa yai wani iri, kuka yasaka yace why Yaya Saleema bakisan yadda sonki yayimun yawa cikin zuciyata ba Yaya Saleema baki gane ina sonki ba, Plx Yaya Saleema ki karb'i soyayya ta dan Allah I can't do wth out U sweety Saleema
Kansa yake bugawa jikin gadon d'akin sa, alwala yatashi yayi yafara Sallah Allah yakamasa mafita
Itama a can mantawa tai da wani Dr tabi bayan sultan a upstairs ta janyo rigan sa
Sultan menene ko wani abu kukayi da Deen d'in?, fada mun kaji plx broth
Huum nifa bansan komai akai ba, da budurwar sa yayi fad'a awaya shine yayi fushi
Hannun ta yana jikin Sultan batasan lokacin data cire a hankali ba, tafara tafiya a slow kuncinta yafara zubar da hawaye budurwa ! Deen bakasan ina sonka ba, zaka kaiwa wata kanka
Gado ta fad'a, tasaki wani marayan kuka, naji kunya SO bakamun adalci ba yakasa naso wanda baya ra'ayi na, baya muradina baya son ganina ma sai kuka
Kayan jikin ta tafara cirewa tana wulli dashi tana kuka da k'arfi, cikin haka Sultan ya shigo da sauri ya rik'o hannun ta Yaya Saleema lafiya wani abu akayi miki?
Cika ni, kada ka k'ara tab'ani so kuke ku kasheni, zuciyata gab take da kamuwa da ciwo fita kaban waje
Noo Yaya kina mun magana a baibai bansan inda zancen ki ya dosa ba, ni burina kullum naga Yaya Saleema cikin farin ciki
Plx talk to me whats going up?, jikinta ne ya saki dab'as ta zauna akan Sofa ta saka kanta tsakanin cinyoyin ta, to mezatace tace tanason Deen impossible
Kai ta d'ago tace Deen.... Ohps Sultan Idan kaji damuwa ta dariya zaka mun so gara kawai abar maganar, kamun Addu'a kaji k'anina
A'a Yaya Saleema ki fad'an, ko mene insha Allah zan tayaki fighting akan komai, ko mutum ne ma oya tell me
Ido ta zuba masa nayan Mintuna kafin tace Sultan I need privacy plx mayi magana anjima
Baison takuramata fita yai, azuciyar sa yace fyn nd good Suna son juna, dama haka nake son Ji,Deen anshiga tarkon love Yaya Saleema ma ma haka
Baccin wahala ne ya kamata, anan ta kwanta har wajana isha'i kafin Mama ta bugamata k'ofa akan ta tashi ta dawo
Toilet ta shiga alwala tai, tafara jero sallolin ta, Addu'a tayi ta tawajan 30 minutes, sannan ta sauka k'asa
Kan Dining ta gansu, cikin sanyin jiki ta k'arasa wajan Abban ta
Saleema ya dai?, naga wani iri ko bakida lafiya kowani abu ke damun ki?
Jikin sa ta lafe tace Abba banjin dad'i, kawai wani iri Jikina zuciyata kamar zafi take
Ayya sannu Saleema ta, ko kinci wani abu ne, ko kin saka damuwa ne ko karatun ne?
Kallon Sultan tai daya tsaya yana sauraran maganar su
Karatun ne inaji Abba yake sakata damuwa kasan stress Idan yaima mutum yawa yana forcing problem, ki rage karatun Yaya Saleema kinayin kad'an kinji
Kasa cewa komai tayi, illa gyara zama da tayi, Jollof ce akayi tanason ta sosai amma me? k'amshin ta kawai taji, taji bazata iya ci ba, kiwi milk ta tashi ta d'akko tafara sha
Sunsan halinta narashin son abinci shiyasa basu wani damu ba, sultan kawai yace Yaya Saleema kidaure kici wani abun zama haka bashi zaiyi miki maganin komai ba
Sultan kafiya magana, zanci fa ko anjima
Kwana wajan 3 Saleema batasaka Deen a Idon ta ba, hankalin ta ya tashi sosai, dan har yafara tab'a karatun ta batacikin nutsuwa ko d'aya Deen yadena zuwa me kenan?
Shima acan b'angaren sa hankalin sa a tashe yazata zai iya jure rashin ganin Sweety Saleema amma ina sai yanzu dabaya ganin ta yayi releasing cewa lallai yana sonta da yawa
She's d only one, d beautiful lady, busty, pinky charming eyes baby, dayake so. I love u chocolate Saleema haka yayita sunbatu kala kala
Kansa ya dafe yace I'm really going to miss u baby Saleema, love is wounderful, u ar d only gal I love since I became a mature, but I don't have any option other than to leave u, my hrt is crying seriously, my eyes ar dripping tears for only u Yaya Saleema.
I hav lost my self looking for u Saleemat, what hav I became for u?, kuka yake sosai saboda wani irin zazzafar k'aunarta da yaji lokaci d'aya
Namiji har Namiji amma gashi so yamaidashi rago, Mace tamkar maza like Saleema SO yamaidata raguwa Lallai SO ni kaina na jinjina maka
Duk abinda yake yi da kalmomin daya fad'a, kaf cikin kunnan Sultan daya zo duba shi
Da baya ya koma, test na number ta wayar Yaya Saleema yamasa kana yaqara masa wani akan ya yake Yaya Saleema nacewa kwana biyu ya kirata su gaisa
Yaji shigowar message so, baiyi tunanin yanada amfani ba ya kyale shi anan bacci yatafi dashi da littafi a hannun sa yana k'ok'arin zama fuskar Yaya Saleema

@ut@r h@jiy@

🎶SO BABBAR CUTA🎶

®NWA

©Zainab Y Hussein

Dedicated to Nafeesa Anker & Princess Hassy

autarhajiya.WordPress.com

3⃣1⃣to3⃣5⃣
Chapter 4 · 0% Book details