← Book details So Babbar Cuta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 8

Sashe 3

So Babbar Cuta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Safiya nayi Saleema ce cikin wata Sharaton purple maikyau tasaka mayafin ta da takalmi kwaras kwaras najiyota tana sakkowa daga upstair books ne da handout a hannun ta
Kan dining tai "Morning Abba and Mama "
"Morning Saleem hop u ar fyn?
I'm OK Abba. hamdan haka ake so yah school d'in ce?
Eh Abba itace ok wallahi nagaji jiya kwana karatu nayi gashi kuma morning lecture garemu
Ba komai Saleema wataran sai labari, remain one to two years fa, kafin lokacin kinyi aure konaga jikokina ko ba haka ba Maman yara?
Kai ta sunne tace Abba kajika nifa ko saurayi banda shi, OK zan nemo ko Raheem Jega nabaki ko?
Lah Abba sorry zan kawo amma kada aban Raheem tana magana tana dariya shima dariyar yai
Kujera taja itama, coffee da sandwich taci ta mik'e Abba natafi. Tom Allah ya kiyaye Ameen
Yaya Saleema bye" Sultan ne yace yanadaga bolcony dak'uwa tabashi tace kobaka fad'a ba yaro zandawo lafiya
Tana magana tana shiga mota, key taimata ta fice
Can department nasu, tana zuwa Didi Aneesa ta tarar a k'ofan class nasu, hannu tabata suka kashe, ya gida ya su Sultan?
Lafiya lou Didi ya kikaje gida?, lafiya lou
Haka ake so ai, Yauwa kinsan wai 'yan legal jiya sukayi graduation sun fito matsayin lowyer sosai na musu murna wallahi
Koh to ai saimun fisu qualification d'in ba d'aya ba. Hakane to ga Mrs Smile nan sai mu ware
Class kowa tashiga, aka fara lectures har aka gama, Saleema kenan komai nata cikin nutsuwa
Captaria sukayi, nan Dr Aliyu ya kirata suka sha hiran su, sosai yake burgeta gayen ya had'u matuqa
2:00 ta koma gida saboda yau za'a majalisa tasan Abba dole yace taje tunda tadawo da wuri
Qawarta ta d'akko saidata direta kana ta tafi gida. Sallama tai ba kowa cikin parlour kitchen tayi anan taga favourite nata d'an wake zuba wa tai tasaka yaji da kwai ta d'akko Haleeb sa'uud ta have sama, saidata jita tayi dam kafin tashiga wanka vest Iya gwiwa tasaka ta k'ure speed na AC tabi lafiyar gado
"Hello Deen ka shirya ne naga 4 takusa?
Haba guy tun yaushe gani kusa da Abba zamu biya Katanka wai ayi order na abinci
Ok nima nayi wanka zanje nataso agogo sarkin aiki, Plx kubiya shoprite kusiyo sweet kaji?
Bazani ba kai bazakaje ba sai mu?, afwaan Freind amma wataran kake cewa ninaje .to naji masifa sai mun had'u OK anjima
Nocking d'akin ta yayi, a magagin bacci tace come in. Kai Yaya Saleema baki tashi ba nifa na shirya Abba mu yake jira, amma dai kin kwafsa plx kiyi sauri
Kai kazo kaina kana magana Plx stay away from here, Amebua kawai, ko gama tashi banyi ba zaka tsareni da surutu
Yaya Saleema kice acikin bacci kawai kike, amma maganar tashi tun yaushe kuma, yi haquri ki mik'e kinji Babbar Yaya d'iya d'aya tamkar da dubu Barrister Saleema Abdulazeez mai Kwangila, yarinya sai aiki nagari da kwazo da nagarta da bin gaskiya
Washe baki tafara tana son taji yanamata wannan kirarin, to naji saici hanya zan shirya yanzu ka faanshi kanka talkative
Eh nidai kiyi sauri Plx! Kai nace to ashafan lafiya
Fita yai, itakuma daga gado ta diro sai toilet, wanka tai, da sauri tafito tafara shiryawa ba wata makeup tayi ba powder da lipstick sai mascara ita tasaka
Shadda orange doguwan riga tasa sai mayafi da takalmi ash color sarqa da d'an kunne na gold ta zuba, ta kawo turaren fogg tasa ga humrah sosai tayi kyau
Qasa ta sakko already har Yaya Na'eem da Ya Sameer sin shirya, wow lil sis kinyi kyau kamar ranar bikin ki
Tnx broth oya lets take selfie, nan suka sha pictures nasu, Sultan yace wallahi Yaya Saleema k'arshe ce ke, inason wannan wankan shiyasa nak'iyin budurwa saina zab'a
Kinga Idan naga kinsaka photo a Insta ana liking wow murna nakeyi sosai nace kaga manyan Barisster dariya kowa yasaka
Ya Na'eem da yaran sa ya tawo, Saleema ita ta d'auke shi suka fita
Dukkansu yayunta sunyi aure suna zaune a Abuja d'aya yana aiki a CNB d'ayan kuma a wani company ne
Matayen su duk family nasu ne, a Maiduguri aka aurosu sunada kirki sosai
Saleema itake driving a wata arniyar Camry sai su ya Sameer awata daban
Majalisa dai wani wajene a cikin sharad'a k'aton fili ne anzahayeshi cikin sa kuma anyi runfa ansaka tiles ga kusan rabin wajan ne aka k'awata shi ga garden aciki wajan abin sha'awa different flowers dasu akayi ado awajan anan duk weekend yaran gidajen suke zama wajan 4 za'aje amma basa dawowa sai 9 ko 10 wataran kuma anan za'ayi wuni
Hira da abinci akeci masu karatu wasu anan ma zasu baje suyi iyayen kuma hiran su akan harkar su suke
Yaran wasu suma hiran su suke, anan kowa za'aji damuwar sa, kuma insha Allah za'ayi masa magani
Get d'in aka wangale musu, suka shiga inda aka tanada dan ajiye motoci anan Saleema tayi parking
Suna shiga Deen ne ya taso yace kaga Banker da kansa, wato ku sai ending na months ake ganin ku wallahi Yaya aikin ya karb'eka kasaka harna hango ni cikin personal office ina shan coffee ina juya kujera ga System gabana ina tura mail wa wani branch d'in
Dariya suka saka, Ya Sameer yace Soon ne fa Deen Allah ya kaimu Indai kayi k'ok'ari kafito da good result ai muna tare
Wallahi kuwa Yaya, wani kuma yaringa zuwa muna basu bashin banki
Lallai kace kawai duk k'arshen wata mu taimaka musakamuku kud'i masu kauri
Ai Bank Idan ba yan kasuwa wallahi ba inda zai kai, mune Idon ku, nan suka fara fad'an nasu Sultan Business dama yake karanta so kowa saiyana fadar important na aikin sa
Tana daga baya take jiyo wata husky voice indai ta canka wannan shine Deen tunda shine yake accounting a gidan
D'agowar da zasuyi daga ita harshi, shi dariya yake itakuma murmushin hiran take Idon su ya had'u gu guda
Wata irin fad'uwar gaba sukaji tare daga ita harshi, saurin d'auke Idon ta tayi, wani magnet ne taji yanason fizgarta akan wannan yaron
Da hannu ya nunata yace Sultan Yaya Saleema abih?, itace mana wai baka San taba?
Wallahi ban San taba, ina yini ya gida da karatu? fyn tace tayi gaba abinta
Bayanta yabi da kallo yace OMG Allah kaban irin wannan amatsayin matar sunnah ta aure Ameen

@ut@r h@jiy@

🎶SO Babbar Cuta🎶

®NWA

Zainab Y Hussein

2 Nafeesat Anker & Princess Hassy

2⃣1⃣ to2⃣5⃣

Deen idon sa ya runtse ya lashi leb'e azuciyar sa yace kadara guda a gidan su Sultan
Taci sunan ta Saleema, tafiyar tama abar kallo ce, ga wani bak'i a kusa da hancinta
Deen lafiya, kalli ko kallo bata maka na arziqi ba, zaka d'ora wa kanka jagwal
Tafiya yai yana sak'a abubuwa da dama, duk abinda yake Sultan na kallon sa, shiru yamasa dai
Saleema itama dai azuciyar ta cewa take Deen, Allah yayi hallita anan, Abba ya haifi d'a da kyau
Kan dadduma ta zauna bayan gaishe gaishe aka fara tsinko kayan fruits ana wankewa yara wasu ball suka fara ita Tab d'inta ce a hannun ta wani website take dubawa na Low hankalin ta yayi can kan abinda take sai dai jefi jefi tana d'agowa tana kallon wani waje
Ba kowane a wajan ba illa Deen dayake aikinsa kan system, shima a fakaice kallon ta yake yana wani murmushi
Kiran Magreeb akayi, so kowa tashi yayi akayi alwala, Deen shine liman so kowa bayan yabi, aka tada jam'i
Itace mace kad'ai wannan karan, ita d'aya ce abaya, tana bin bayan su
Karatun sa dataji yadda yake k'ak'ale ga tajweed gaba d'aya ya tafi da Imanin ta, har aka tafi ruku'u bataji ba saidaga can. sallama tai tafara istigfar Allah ya taimaka ta tana baya bawanda ya ganta
Ana idarwa yafara jero Addu'oi, ciki harda fatan samun irin Yaya Saleemat, ya iya Addu'a tace a mind nata
Abinci aka fito dashi, nan Saleema ta tashi, plate ta ajiyewa kowa agaban sa lokacin datazo gaban sa a hankali ta ajiye ido hudu suka had'a, fuska tai ta wuce shikuma murmushi yayi
Haka ta zubawa kowa, datazo gaban sa, loda masa tayi, asanyaye yace Yaya Saleemat yayi yawa banci da yawa plz hav d'in sa ma is ok
Husky voice, kusan k'amewa tai, amma daurewa tayi tace ok nazata kaima irin Sultan ne naga abokin Kane kuma sai hali yazo d'aya abota ke dank'o
Eh Hakane amma wallahi Yaya Saleemat ni ban iya cin abinci mai yawa dadai fresh milk kikace so inashanta sosai
Ok bara a rage, yauwa Yaya Saleema
Shi wanann Saleemat yaji ana cewa koko fi'ili ne? saiwani Saleemat yake ban tana magane cikin zuciyar ta
Basu suka tashi ba, sai da akayi Sallah ta Isha'i da adduoi sannan kowa yakama gaban sa
Waigawa sukai atare lokacin da kowannen su zai Shiga motor, hannu ya d'aga mata itama haka
Washe gari 9 a gidan su Sultan taiwa Deen dan kawai yaga Saleema jiya da ita ya kwana, yana jin wani abu akan ta amma baisan komeye ba
Lokacin daya shiga tafito zuwa school gaidata yai, a hankali ta amsa ta wuce, Sultan daya biyota yana baya yaga kallon da Deen kebin Saleema dashi, shi dariya abin ke bashi Deen da juya yi
Bata kalle saba harta fita, duk da zuciyar ta na d'okin hakan, jiya da muryar sa ta kwana arai
Ko dataje school, kusan rabin tunanin ta akan Deen tayi, Illa basarwa data ke
Kusan kullum Deen yana hanyar zuwa gidan, ita hartafi shi d'okin yazo, a taga take tsayawa tayi ta kallon sa tana hangen dariyar sa mai ban sha'awa

3 weeks later
Chapter 3 · 0% Book details