← Book details  Kukan Kurciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 9

Sashe 7

 Kukan Kurciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Washe gari bayan sun kammala breakfast suka nufi polistion, itadai duk abinda ake ameeda binsu kawai take da kallo cikin mamaki, tarasa gane kan wannan lamari, har yanzu bata fahinci inda suka dosaba, gashi kowa ya'ki bata damar tambaya, dahakadai suka 'karasa, tunda suka shiga 'yansanda suke 'kamewa daddy, watodai afahimtar ta daddy ďansanda ne kuma babba, shiyyasa yaja rundunar 'yansanda har kano suka yayibosu, towai misuka yimusu?, mi iyayenta sukai misu ne?, komadai miye ai yanzu zata gani, wani 'kayataccen office suka isa, mutummin dake saman kujerarsa ya mi'ke tareda sarama daddy, daddy yay masa umarni daya zauna, suma duk suka zazzauna asaman kujerun da aka 'kawata office ďin dasu domin saukar ba'ki, wanda suka tarar a office ďin yakira waya taraeda bada izinin shigowa dasu iya abu.
    Babu daďewa aka shigo dasu kallo ďaya ameeda tayi musu hankalinta yatashi, daka gansu kasan sunci ďan karen duka, duk raunuka ajikinsu, dareďaya sunyi wujiga2 kamar waďanda suka shekara akulle.
   Gaban dady da momy suka zube suna kuka da ro'konsa gafara, alhaji dan girman ALLAH kayi mana rai wlhy ka 'kara barinmu awajennan kashemu zasuyi, wlhy munyi nadamar abinda muka aikata, kuma ashirye myke mu faďa muku gskyar lamari, dan ALLAH kace karsu kashemu.......dakatar dasu dady yayi tahanyar ďaga musu hannu, ruf suka rufe bakinsu tamkar ruwa yacinyesu, office ďin yay tsit, dady yay gyaran murya tareda faďin musa ai inaga kawai zamu tafi dasu gidan dan kes ďin nagidane, dama nabari kakawosu nanne dansu dan nasan kai tsaye bazasu amsa laifinsuba sai sunji wuya, musa D.P.O yace babu damuwa sir bari nasa akai makasu, ai tun daren jiya suka faďi laifinsu kuma sunce basu kaďai bane suma sakasu akayi.
   Dady yajinjin kai ya ce, "shiyyasa nace zamu je gida dasu dansu nuna mana waďanda suka sakasu ďin dady yafaďa yana mi'kewa.
   'Kara cimimiyar su iya abu akayi zuwa wani haďaďďen gida shima babu nisa da gidan  dady, dady ne yafara shiga, da wata dattijuwa yafara karo, dakaganta kasan ba 'karamar masifaffiya bace, dan ko sallamar dady acinkushe ta amsa masa kuma cikin yanayin masifa, doguwace fara 'kya'ky'kyawa, tahaďu sosai dan tafi momy 'kyau nesa ba kusaba, daddy yazauna yana faďin ya gidan??, ta yatsine fuska tareda ta6e baki, yaukuma mafarkinmu akayi da sassafen nan??, ďan murmushi kawai daddy yayi dama sainayi mafarkinki nake zuwa ganinki, ba jiya dasafe nabar gidanba, nanma baki ta ta6e ai nasan idan kana gidan 'yar gold mantawa kake da kwa da komai, yanzuma da safennan sayeed yayo waya wai yana bu'katar kuďi, dady ya haďe fuska wane kuďi kuma yake bu'kata? Kofa sati uku banyi da tura masa dubu ďari biyarba, shin kuďin abincine??, bare ace suyakeci? Haba alhaji yanzu dan ALLAH dan yace yanason katura masa kuďi saiya zama abin faďa, sukenanfa ALLAH yabaka su biyu dukiyarnan fa tamkar tasuce tunda idan kamutu sune zasu gada, bare kace za'aci da ha'kkin 'yar gold, murmushi dady yasaki tareda gyara zama nibama wannan yakawoniba hassana, ta watsa masa kallon rainin hankali to da wacce kazo??, kodami kazo ashirye nake dakai alhaji ta'kare maganar cikin 'kufula.
      Kallon k kika sani yay mata sanan yaďauki wayarsa yay kira, kushigo kawai yace ya kashe, tami'ke tsaye afusace, wakuma ka kawomin har cikin gida, kaifa nakula kullum rainin hankalinka 'kara yawa yake, wlhy Alhaji har yanzu ina nan amatsayin hassanata daka sani, babu abinda yarage ahalina.............maganar ta kakare mata ama'koshi dan ganin masu shigowa, saikuma jikinta ya hau rawa dataga su iya abu, gabanta sai dukan tara2 yakeyi, tadaka musu tsawa kai kukuma daga ina? gayyar tsiya arna a idi, babu wanda ya kulata saima neman gurin zama dasukayi, Nasir ne 'karshen shigowa falon, ta gwalalo idanu tareda faďin Nasir kaikuma daga ina?, ina kasamo waďannan kara da kiyashin? Gaba ďaya aruďe take maganar, baice mata komaiba yanemi guri shima yazauna.
   Dady ya kalleta ya ce, "hassana yakamata kizauna, da'karfi tace bazan zauna ďinba munafuki, to wannan gayyar dakayomin ta micece??, tsawa dady yadaka mata tareda faďin karki zauna ďin, ai zaki zauna da tsiya, ana cikin haka saiga wani dattijo shima yashigo, shimaďin arazane yake bin mutanen falon da kallo, yanan tsaye wata tsohuwa tashigo tareda wani dabaikai su dady girmaba, saikuma mata su uku sumadai da'alama akwai dangan taka tsakaninsu da dady dan naga kama, sudai nakula kowa hankalinsa akwance yake.
   Duk guri suka nema suka zauna, hajiya hassana ce kawai a tsaye, da'alama tana samun hanya arcewa zatayi waje, saikuma dattijon nan dayaketa zufa da rawar jiki, sai kulmawa su iya abu idanu yakeyi, falon yay shiru babu abinda ake sai kallon kallo musamman ma Ameeda da kanta yake shirin tarwatsewa saboda mamaki wanan irin taron dangi haka duk na miye??.....maganar dady ce ta 'katseta, sallama yay musu tareda godiyar halartar kiransa dasukayi, kowa ya amsa.
   Tsohuwar nan ta kalli dady tareda faďin Hamza ina kasamo wannan yarinyar??, ta nuna ameeda, naga ita kaďaice ba'kon ido afalonnan gashi? kuma ina jin wani abu gameda ita""..
   Dady yace mama ai akantane akai wannan taron, insha ALLAHU yanzu zamu fiddaku aduhu.
    Kallonsa ya maida gasu iya abu ya ce, "abu munason jin wani abu daga bakinki keda malam dauda, malam dauda yay saurin 'kar6e maganar da faďin wlhy alhaji banida laifi kona sisin kwabo, kaga wanan munafukar ya nuna iya abu, to duk wani kulli ita tasanshi tareda hajiya matarka da alhaji Tasi'u yayanka da matarsa, saikuma abokanka uku da 'kanwarka matarka hajiya sadiya, saikuma Nasir kanin matarka, duk wani bayani abakin waďannan mutanen dana lissafa zaka sameshi dan sune suka kulla abinsu, nima saboda hakane aka danneni da asiri nakasa ta6uka komai arayuwata.
   Dady ya ce, "malam dauda su waye abokannawa??, malam dauda ya ce, "alhaji safiyanu da marigayi alhaji lawan da alhaji mansur......atsorace dady yake kallonsa saikuma yazaro waya da sauri batarda yayi maganaba ya hau kiransu ďaya bayan ďaya da bu'katar son ganinsu, cikin minti goma sha biyar suka iso kusan atare, ba abunda sukayi zaton ganiba kenan dan haka dasuka shigo duk sai suka rikice bayan sun gama bin falon da kallo, dady ya ce, "kuzauna mana, amnafa kuyi ha'kuri bansanar daku dalilin kiranba.
    Tsohuwa ta katse musu zance da faďin wai mike faruwane, nifa sai "kara rikitar dani kukeyi da sakani aduhu,, kiyi hakuri mama yanzu zaki fahimci komai, abu bismillah...ina kika samu wannan ďiyar??????.
     Ďagowa tayi tana kallon ameeda, muryarta na rawa ta ce, "hajiya ce tabani.......................

Ku biyomu.

©2017

Hikayarmu!!!!!!!.
   abba gana
        bilyn Abdul
[04/03 10:46] bilyn Abdul: KUKAN KURCIYA.........

                NA
MUH'D ABBA GANA
                 &
BILKISA IBRAHIM
   (☆bilyn Abdul☆)

Page23&24
Chapter 7 · 0% Book details