← Book details  Kukan Kurciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 9

Sashe 4

 Kukan Kurciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Itako Ameeda tunda suka koma gidan falmata tafaďa duniyar tunani kokađan fuskar saurayin dasukayi karo takasa 6ace mata, duk wani motsinta yana kan tuna fuskarshi,, har falmata saida talura da damuwarta, kusada ita tazo tazauna, cikin sigar lallashi ta ce, "haba Ameeda wai saiyaushe zakibar sakama kanki damuwa akan abinda bake kika ďorama kankiba???,, yakamatafa ki zubar dakomai agefe kiji daďin rayuwarki, dagafa duniya sai kaduna,, watarana bazamuyi abinda mukeyi yanzuba.
    Murmushi Ameeda tayi tana mai kallon fuskar falmata ta ce, "falmata ai bazamuyima ALLAH wayauba,, nida ke duk bamusan ranar da mala"ikan mutuwa zaizo kanmuba, wlhy ina matu'kar shiga cikin damuwa da halin danake ciki.
   Sai kuma wani SABON AL'AMAREE (littafin bilyn Abdul) dayake shirin faruwa agidanmu, amma bansan taya zan fassara shiba, ayau kuma na'kara gamo dawani abinda ya tsayamin zuciya acikin asibiti.
   Falmata ta gyara zamanta sosai,Ameeda miye yake shirin faruwa agidan naku?, miye kuma kikayi gamo dashi a asibitin??, shiru Ameeda tayi saikuma zuwa can ta nisa hannun falmata takama tana faďin karki damu zan sanar miki amma bayanzuba,, a asibiti kuwa mutumin damukayi karo da junane ďazu yaketa yimini gizo a idanu, bansan miyasaba nakasa mantawa da fuskarsa da kuma irin kallon kurillar dayake mini.
     Dariya sosai falmata tashigayi har Ameeda tafara jin haushi ta ce, "k kuma miya baki dariya daga cikin maganganuna???.
    Falmata ta tsagaita da dariyar tana bama Ameeda ha'kuri, wlhy 'kawata ganinayi kamar kin kamu da soyayyane?, tsaki Ameeda tayi ta ce, "kefa falmata watasa'in kanki a cunkushe yake wlhy,, wlhy abinda nakeji gameda mutumin ďazu yafi 'karfin soyayya, wani abu daban nakeji gameda shi, kinsan ban ta6a soyayyaba kuma har yanzu baga wanda zanyi soyayya dashiba.
    Falmata ta langa6e kai gefe kenan yaudarar Nas kikeyi??, tsakai sosai Ameeda tayi, "o, da ke atunaninki son Nas nakeyi?, to idanma kina tunanin haka kibari wlhy banta6a jin onason Nas azuciyataba,, k ahalin yanzuma jinake na 'kara tsanarsa da duk wasu halayensa.
    To shikenan Ameeda ALLAH yajishemu al'kairi, Ameeda ta ce, "amin 'yar uwa.
   Gaba ďaya yinin yau haka tayishi sukuku kuma cikin ikon ALLAH batasha komaiba har dare, agidan falmata takwana dan kwata2 bata sha'awar komawa gidan,, koda sukaje club  da daddare batasha komaiba, bakuma tayi rawaba, gefe tasamu ta zauna abinta, kowa yasan budurwar Nas ce dan haka babu wanda ya matsa mata, dan sunsan halinsa sarai, kuma yana dawowa labari zai kai masa, ba'karamin aikinsa bane yakashe mutum.

Haka rayuwar tacigaba da gudu da sauri,, babu abinda yacanja daga rayuwar ameeda saima kara ta6ar6arewa da yakeyi,, dan Nas yadawo mata dawani sabon salon na shaye2, gidansu kuwa ji ake da'ita yanzu su iya basa mata faďa bare duka, duk abinda takeso shi ake mata, ita lamarin nasu har mamaki yake bata matu'ka.
   Yauma haka taci kwalliya cikin doguwar riga ba'ka saidai daka ganta kasan abinda tasha bai gama sakintaba, haka tafito tana ďan dafe bango ayayin dataji zata faďi, cikin ikon ALLAH harta iso titi, tana tsaye domin jiran babur ko mota saiga wata dalleliyar mota tadawo da baya har zuwa gabanta dan da harya wuce.
    Ahankali aka zuge gilas ďin motar 'kya'ky'kywan saurayin ranarne ya bayyana, atsorace Ameeda taja baya tana tangaďi, yabuďe motar dasauri yafito, sorry yafaďa yana matsowa kusada ita, ta ce, "malam lafiya kuwa??, murmushi yasaki mai 'kayatarwa ya ce, "lafiya 'kalao 'yammata, ina zuwa haka??.
    Tai saurin dafe bangon wani shago danjin tana niyyar faďuwa, ina ruwanka da inda zani nikam banason yawan shishshigi gsky,, amamakinta saitaga yayi murmushi tareda haďe hannuwansa a waje guda yana faďin sorry madam, amin afuwa natsaya ne narage miki hanya naga kina bu'katar hakan,, harararsa tayi tana wani lumshe idanu irinna 'yan maye, to idan banasofa?, sai incigaba da ro'konki harki amince kishiga motata beauty.
   Murmushi tayi saboda jindaďin sunan daya kirata dashi, ta ce, "to muje ALLAH dai yasa karka sayar mini dakai,, buďe mata motar yay tashiga yana faďin ai ko sayar da kai nakeyi bazan saida na beauty ba irinki, dariya tayi tana faďin maza akwai daďin baki.
   Tada motar yay sukabar titin batareda yayi maganaba.
  Yajuyo yaďan kalleta yayinda sukayi nisa, beauty ina muka nufane??, taďan gyara zamanta ta ce, "muje zan rin'ka nuna maka hanya, okey yafaďa yana murmushi,, lafiya lau ta nuna masa hanya harzuwa gidan falmata yayi mamaki kwarai da gsk, azatonsa yanda take abigennan bazata iya komaiba, tafito tana masa godiya, ya ce, "yanzu nan haka zamu rabu ko number bazaki baniba??, taďan ta6e baki haba malam daga haďuwa yau saina ďauki no ďina nabaka??, ya murmusa A'a beauty kindai manta yauce haďuwarmu ta biyu fa, aikuwa na cancanta abani, kinga idan kinbani number ki duk sanda kika bu'kaci zuwa wani waje sainazo nakaiki, kinga kinsamu direba daga sama kenan.
    Dariya sosai tayi tareda mi'ka masa wayarta tana faďin sarkin wayo gashi kaďauka, yauwa ngd sosai yafaďa yana kar6ar wayar tata mai 'kyawun gsk, number sa yasaka sanan yakira tata yay save ďin tasa atata sanan yayitata atashi,, sallama sukayi yaja motar yatafi suna ďagama juna hannu, itama saita shige gidan falmata tana murmushi, jinta take cikin wani farinciki mara musaltuwa.............

Ku biyomu.

©2017

Hikayarmu!!!!!!.
abba gana
           &
     bilyn Abdul
[16/02 11:48] bilyn Abdul: KUKAN KIRCIYA........

          NA
MUH'D ABBA GANA
                 &
BILKISA IBRAHIM
  {☆Bilyn Abdul☆}

Page1⃣1⃣&1⃣2⃣

Babu daďe tadawo hannunta ri'ke da ledar indome, sanda tadawo iya abu ta tashi dan haka tashige ďakinta itama, tana tunane2 yanda iya abu ta ruďe lallai awai wata magana a'kasa,, amma zatayi 'ko'kari tonota insha ALLAHU.
   Hakadai tacigaba da tura indomi ďin badan tana mata daďiba, bayan tagama ci tafita wanko hannunta,, harta kai gab da 'kofa zata shige saitayi saurin jan birki danjin ana magana 'kasa2 a ďakin iya abu, ta matsa ahankali gefen 'kofar baba taji yana magana cikin ruďewa.
   Abu!! data tanbayeki mikika cemata??.
   Why malam bance mata komaiba saboda matu'kar razana da maganar ta sakani, iya abuce ke magana cikin rawar murya.
  Baba ya ce, "lallai wannan magana takai arazana, to wai ya akayima wananan yariyar harta iya wanan magana??, kodai Nasuru ne ya kitsa mata hakan??.
   Kai malam kaima kasan nasuru bazai faďaba, dan yanama abuja, nasan Nasuru bazaiyi irin wannan kato6ararba.
                   Baba ya sauke numfashi tareda yarce gumin daya wanke masa fuska, ahankali ya furta lallai idan mukayi sakaki tofa allura zata tono garma..........da sauri iya abu ta katseshi haba malam daina yimana wanan fatan mana, ai har abada babu mai tono mana daďaďďen sirrinmu, wanda dagamu sai ALLAH saikuma hajiya.
   Baba ya jinjina kai, to ALLAH ya tabbatar mana zainabu.
     Tunda Ameeda ta'iso wajen tsaye take kamar gunki, zuface keta ambaliya adukkan sassan jikinta, maganganun su iya abu sun rikita mata kwakwalwa, tarasa yanda zata fassara zancen nasu dan ta fahimta.
    Da sauri tashige ďaki danjin motsin babanta zai fito, ta faďa saman katifarta tana fidda numfashi, afili ta furta wanne irin 6oyayyen sirrine su baba basa son nasani, minene ma'anar allura zata tono garma idan sukayi sakaki???, miyasa suke zargin kuma Nas shiyya sakata wanana tambayar???? Shin wai miya haďa Nas ma da sirrinsu??, kodai Nas yasan wani abu gameda family ďinsu ne???,, tadafekai tana jijjigashi kamar mai shirin hawa bori, hawaye suka fara silalowa akumatunta, itakam tana kallon rayuwa a baibai, lallai akwai mayan 'kalubale dake bibiyar rayuwarta ta baďini data zahiri,, yanzu tawace hanya yakamata tabi domin binciko boyayyen sirrin iyayen natane dasuke 6oye mata akan aslinsu da tushensu???, da sauri kanta yake sarawa kamar zai faďo 'kasa.
    Jakkarta ta raruma tafara zazzagewa amma bataga abinda take nemaba, ta koma cikin kayanta, cikin sa'a tayi tozali da kwalbar sirob guda uku, da hanzari take 6alle murafan  ta juye maganin abakinta, ta yarda kwalaben gefe dan bai ishetaba, kwalaben ďazu ta đauka tana 'kara kalacewa anan barci yay gaba da ita.

WASHE GARI.
      Da'kyar taiya tashi tayi sallah tayi wanka tana cikin shafa mai kiran falmata yashigo ta ďauka murya aďashe tana faďin falmata ykk??.
   Lfy lao Ameeda kema ykk?, ina lfya, dama sonake kizo kirakani wani waje dan ALLAH, okey babu damuwa dama shirin zuwa gidanki nakeyi,, to shikenan ina saurarenki.
          Bayan wani ďan lokaci tafito saye cikin atanfa zani da riga ta yafa mayafi, atsakar gida taga iya ta gaisheta sanan ta ce, "zanje gidan falmata saina dawo.
    Cikin rawar jiki iya tace to saikin dawo Ameedan baba, batabi takantaba tafice daga gidan.
     Koda taje sai suka nufi inda zasu, gidan wata 'kawarsu sukaje sukai mata  ALLAH yasanya Alkairi, dan tayi aurene itamadai irinsu ce ALLAH ne yay mata gyaďar dogo tasamu miji tayi aure.
     Daga nan asibiti suka nufa domin yin dubiya, bayan sungama dubiya suka fito, arikice Ameeda taďago domin ji tayi karo da mutum lokaci ďaya suka ďago suna kallon juna, ahankali tafurta yi ha'kuri dan ALLAH.
    Ko motsi baiyiba saboda shiga wani matsanancin ruďani, kallonta yakeyi ko 'kyafta ido bayayi, falmata taja hannunta suka bar gurin................

Ku biyomu.

©2017

Hikayarmu!!!!!!.
abba gana
           &
       bilyn Abdul
[19/02 13:21] bilyn Abdul: KUKAN KURCIYA.......

            NA
MUH'D ABBA GANA
                  &
BILKISA IBRAHIM
   (☆bilyn Abdul☆)

Assalamu alaikum.
muna mi'ko gaisuwa da fatan alkairi gareku masoyanmu aduk inda kuke,, kuyi ha'kuri dabaku pages ďai2 damukeyi kullum, littafin namu gajeren labarine,, insha ALLAHU muna gab da kammalashi,, mungode da 'kaunarku garemu,,, luv u oll. 

Page1⃣7⃣&1⃣8⃣
Chapter 4 · 0% Book details