← Book details  Kukan Kurciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 9

Sashe 2

 Kukan Kurciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

    sallama tayi ta shige ciki, Suka rungume juna cikin farin ciki, falmata tace kai Ameeda wlhy yau kinyi k'yau, ga idanunki yau dai-dai suke.
    Ameeda tayi dariya ta ajiye jakar ta  a saman kujere, ta warware gyalen data nad'e akanta shima ta ajiye, ta kwanta.
     Falmata ta ce, "badai barciba Ameeda??, Ameeda tad'an yatsine fuska, ta ce, "barci tsiya nakeji, ga yunwa ya takurani yakamata abani abinci.
    Falmata ta ce, "to mizakici? Asiyo miki, kinsandai ni ba girki nakeyiba.
    Ameeda ta harari falmata tana fad'in ai ba abin kirki kikayiba.
    Falmata tayi dariya kawai, dan kullum Ameeda tana bata shawara akan tadage ta iya girki, saboda wataran dole subar shashancin nan suyi aure.
     Babu dad'ewa aka kawo musu  abinci, suka zauna sukaci suka k'oshi, Ameeda ta kalli falmata ta ce, "wai babu komai yau agidan ne??.
    Falmata ta harareta, dan tasan kayan maye take nufi, ta ce, "plz Ameeda karki sha komai, ke wai bakya zama sai abuge, yakamata yau d ki dan huta, gashima zanyi bak'i daga abuja, shi yasama na ce, "kizo da wuri, danki tayani gyaran gida.
      Ameeda ta ce, kice dai kawai kin maidani 'yar aiki, amma wane irin bak'ine maza ko mata, idan mazane kema kinsan bazan zau.......
     Falmata tayi saurin katseta sannu ustaziya, nibansan randa zaki wayeba Ameeda, kishigo harka sosai dan ki wuce wajen, kifita daga tarkon talauci, ki fidda iyayenki.
    Ameeda ta had'e fuska tareda d'agawa falmata hannu, "kinsan nasha gargadinki akan wannan maganar, wallahi dana tara dukiya da kudin banza gwara na mutu acikin talauci, tamik'e a fusace taja gyalenta da jakka.
     Da sauri falmata ta tareta tana bata hak'uri, akan bazata sakeba, dak'yar tashawo kan Ameeda ta hak'ura ta zauna.
     Ameeda taje ma'ajiyar kayan mayensu takwaso kwalabe uku  tadawo tazauna, dan sune kad'ai zasu gusar mata da b'acin ran da falmata tasakata, ta tsani kace mata tayi tarayya dana miji, haka tadinga korawa harsuka kare, tamik'e zata k'aro wasu, falmata tayi saurin tareta tana fad'in ya isa haka.
    Ameeda ta ce, "d'aya kawai zan k'ara, falmata ta ce, "A'a, bazaki k'araba wlhy uku fa kika sha, nan dai falmata tayita lallab'ar ta, harta hak'ura tashige bedroom ta kwanta.
    Falmata tabita da kallo tana girgiza kai, tana mamakin yanda Ameeda take caja kanta da kayan maye, amma bata yadda ta aikata wani fasikanci ba, zata iya cewa bata tab'a had'uwa da mutum irin Ameeda ba, dan sunsha yin fad'a akan hakan, koda yake tasan tunda Naseer ya gagara tursasa Ameeda  dole kowama ya kasa.
   Dan idan har Naseer yasaka ido a kan mace tofa dolene tashiga tarkonsa, amma Ameeda ta gagareshi, yayi dai nasarar koya mata shaye-shaye, da zuwa club, amma sauran bad'ala ya gagara.

WACECE FALMATA???

Falmata 'yar asalin barno ce,  ita cikakkiyar babarbariya ce.
    Falmata yarinyar kirkice mai ilimi da addini, mahaifiyarta ta rasu wajen haihuwarta, daganan kakarta ta reneta tsawon shekara bakwai daga baya Allah ya karbi abunsa.
    Bayan rasuwar kakarta sai aka dawo da ita gidan mahaifinta, daga nan falmata tashiga tsananin rayuwa, dan matar babanta tana gallaza mata, bata sonta ko kad'an, amma agaban mahaifinta ta kan nuna mata tsantsar so da tausayawa.
    Wannan yasa mahaifinta yakasa fahimtar halin da falmata take ciki, gallazawar tayi yawa, dan har takai abinci yana gagarar ta agidan, wannan yayi matuk'ar tasiri wajen lalace warta, daga baya  ta gudu zuwa garin kano, anan tahad'u da badaru abokin Naseer.
    Shiya siya mata gida, yake mata komai data buk'ata kamar matarsa.

  takaitaccen labarinta ....................

Ku biyomu.

©2017

Hikayarmu!!!.
Abba gana
            &
     Bily
[11/02 12:08] bilyn Abdul: KUKAN KURCIYA......

                NA
MUH'D ABBA GANA
                &
BILKISA IBRAHIM
   {☆bilyn Abdul☆}

Page9⃣&🔟

Ameeda ta juya ta sake juyawa akan 'yar yololiyar katifarta, gaba ďaya kanta akulle yake tama rasa irin tunanin dazatayi, da sauri ta mi'ke zaune tajawo jakarta ta hannu, kwalaben sirob taďakko guda uku taďan rintse ido tana mai ba'kin cikin yanda rayuwa da sakacin iyaye ya jefata, afusace tashiga 6alle marafan kwalaben kamar wadda ta tuna wani abu, jiki na rawa tashiga tuttula maganin abakinta kamar mai shan ruwa, kafin mu farga ta shanye kwalabenan ukku gaba ďaya,, abba ya girgiza kai yana jan numfashi da sauri,, tabbas yanajin tausayin halin da ameeda take ciki,, nikam kunsan mace da rauni saida nayi kuka.
    Tana gama sha ta 6ingire awajen tahau barci,, muma sai muka fito guywa a sanyaye.
   Ameeda bata farkaba sai bayan magriba, ta mi'ke zumbur tana kallon kanta kamar wadda aka sake, takai dubanta ga agogo, ido ta zaro dan ganin yanda lokaci yatafi idan zata iya tunawa tun 'karfe tara na safe take barcinnan, ta furta na shiga uku babu azahar bare la'asar, da hanzari tafice daga ďakin iya abu ce kawai atsakar gidan take tatar koko, ta shiga washe baki yauwa ameedan baba kin tashi??, kinga zoki 'karasa min tatar nan dama nagaji wlhy, ďan 'karamin tsaki ameeda taja ta wuce batarda tabi takan iya abu ba bareta  tanka mata, iya abu ta ta6e baki 'yar kwaya tanaji ina magana tamin shiru kai ALLAH yawadaranki Ameeda, kai kawai na girgiza ina faďin ohni abba wanan wace irin rayuwace akeyi agidanan???, naďanja tsaki domin babu mai bani amsa tunda bily yau bata nan nikaďai nazo ďaukar muku rahoto.
   Ina nan zaune saiga ameeda tafito daga bayi da'alama wanka tayi, ruwa ta ďiba abuta tayi alwala, ďaki tanufa batareda takula habaicin da iya abu take mataba,, sallolin da'ake binta tashiga ramawa, tadaďe tana addu'a da ro'kon ALLAH ya shiryata tadena mugayen halayen datake aikatawa, dakuma ro'kon ALLAH yabata miji nagari mai sonta da gsky, ta shafa sanan tafito waje.
    Zuwa sanan iya abu tagama tatar kokon tana zaune tana walfar tuwo abinta, ameeda taja kujera 'yar tsugunno ta zauna agefen iya abu,, tana kallonta amma ta share tacigaba da cin tuwonta, ameeda taďan murmusa dan tasan tana fushine akan abunda tayi mata ďazu, cikin taushin murya ta ce, "iya ina nawa tuwon??, saida iya abu ta haďiye laumar tuwonta jikake kutttttt sanan ta harari ameeda cikin masifa ta ce, "ban dafa dakeba,, murmushi ameeda tayi ta ce, "babu damuwa iya, taďanyi shiru zuwa wani lokaci saikuma taja numfashi tareda faďin iya dan ALLAH inada tambaya??, iya tai mata banza bata tankaba.
   Ameeda tacigaba da faďin iya wai ina 'yan uwanmu ne??, gaban iya abu yafaďi duuuuum arikice taďago tana kallon ameeda data tsura mata idanu, sai fidda numfashi take da'kyar ga gumi yafara bin sassan jikinta kamar wadda tahaďi kwaďo,, Ameeda ta ce, "iya yayadai ko tambayata ta 6ata miki raine??, da sauri iya abu take girgiza kai saikace 'kadangaruwa, tashiga kame2 A'a ameeda babu komai tambayarki bata 6atamin raiba, miye abin 6acin rai awanan tambayar kawaidai naji xancen nakine abazata shiyyasa......  ameeda tayi saurin 'katseta to iya kibani amasa mana ina danginmu suke?, kuma mu 'yan asalin wane garine??, inane tushenmu na asali??, cikin sar'kewar harshe ta ce, "kibari ba yanzuba watarana zan faďa miki, to waima miye dalilin wanan tambayar???.
   Ameeda tagyara zama tana faďin babu komai iya,, kawaidai ina son sanine, ina kuma mamakin tunda nataso bamu ta6a zuwa wani gari danufin ziyarar danginmuba, sai nan kano kawai nasani,, ahankali kuma nafara fahimtar bawata dagantaka mai 'karfi tsakaninmu da 'yan uwanmu nan kano, musamman idan nayi la'akari da irin halin danake ciki basu ta6a nuna damuwarsuba bare su tsawatar mini.
   Jikin iya abu sai rawa yakeyi kamar mai jin sanyi, Ameeda tana kula da'ita, tana mamakin yanda iya abu tashiga wani hali daga tambaya.
   Lalai akwai alamomin tambayoyi akan iyayen nata,, akwai wani 6oyayyan abu gameda tarihinta,, lokaci yayi dazatasan mi iyayenta suke 6oye mata, lokaci yayi dazatasan inda danginsu suke, lokaci yayi dazata nisanta kanta ga iyayennata, tasan duk tsiya bazata rasa wanda zai ri'keta acikin dangin nasuba harta samu mijin aure,, tayi al'kawarin koda a'kauye dangin iyayenta suke zata zauna dasu kuma tasamu miji acikinsu tayi aure,, tagaji da wanan tam6elen datakeyi, tasan kuma indai tana gaban iyayenta bazata ta6a daidaita rayuwartaba,, ta mi'ke batareda ta tanka irin lallashin da iya abu take mataba akan taci tuwon data zubo mata,, gyale taja akan igiya tafice abinta......................

Ku biyomu!!

©2017

Hikayarmu!!!!!!!
abba gana
             &
      bilyn Abdul
[11/02 20:11] Abba Gana: KUKAN KURUCIYA....

            NA
MUH'D ABBA GANA
               &
BILKISA IBRAHIM {Bily}
   (Mrs Abdus'salam)

Page7⃣&8⃣

Sai yamma can Ameeda ta tashi daga nannauyan barcin daya d'auketa, takai dubanta ga agogon dake manne a d'akin falmata, 5:56pm ta zaro idanu tareda fad'in nashiga uku ni Ameeda ko sallar azahar banyiba, ta zabura daga gadon tana maida numfashi, bandaki tashige tayi wanka tareda yin alwala.
   D'akin tadawo tafara ramuwar sallah.
   Bata bar wajenba har saida tayi sallar isha'i, tun tana kabbaran farko  takeji ana buga k'ofa bayan ta kammala ta saka kayan falmata sannan ta bud'e d'akin tafito.
    Tayi turus dan ganin Naseer zaune, shima ayatsine yake kallonta yanata wani mazurai.
   Ta daure ta ce, "sannu da zuwa.
   Harara ya watsa mata taredajan tsaki, ya ce, " 'yar rainin hankali, shine kika wani kulle d'aki, anata bugawa kinyi banza da mutane.
    Ameeda tad'an tab'e baki kayi hakuri ina sallah ne.
   A'a d'awafi kikeyi, tun karfe 1 narana nake zarya agidannan falmata ta ce, "mini kina d'aki kwance, dan iskanci inata buga miki kinki ki bud'e.
   Lah wlhy barci nakeyi, kwata-kwata banjikaba, kaima kasan danaji zan bud'e aii.
   Harara ya zabga mata, yau kika fara shiga d'aki ki kulle ayita bugawa kiki bud'ewa, zaki kawomin wani tsarin banza.
   ka yi hak'uri, yanzu mike tafe dakai??
   Saida ya kurb'i giya sannan ya ce, "nazone dama nafad'a miki gobenefa zuwa abuja d'innan, dan haka ki kwana da shiri, dan kinada matuk'ar muhimmanci awajen faty d'inanan, kinsan dai yanda nake da ANAS, baikuma dace ace babu baby na awajen birthday d'insaba.
    Ameeda tad'an murgud'a baki, nidai tun ranar nagaya maka bazan jeba, dan haka kabar zancennan kawai, banaso yakawo mana b'acin rai, tafad'a tana mik'ewa, ni bari na wuce gida dare yanayi.
Chapter 2 · 0% Book details