← Book details  Kukan Kurciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 9

Sashe 6

 Kukan Kurciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka rayuwar tacigaba da gungurawa yayinda da Muzzaffar yashiga rayuwar Ameeda sosai, koda yaushe suna ma'kale da waya, ko kuma su haďu awani wajen dan bata so Nas yagane tana tare da wani, cikin hikima yake janye ra'ayinta daga barin shaye2, idanma tasan zasu haďu bata shan komai kwata2, yauma tana zaune aďakinta sai wayarta tafara ruri, takai hannu ta ďauka dan ganin sunan Muzzaffar, cikin muryarsa mai daďi ya ce, "assalamu alaiki beauty, saida tayi murmushi sannan ta ce, "wa'alaikassalam yayana, ykk?, ya aiki??.
    Alhmdllh wlhy, yanzuma gani ina shiri tashi daga aikin, kefa kina inane??, gabanta ne yafaďin dan batasan yazata cemasaba, tunda suka haďu baisan inane gidansuba kullum a hanya suke haďuwa ko gidan falmata, shi azatonsama nanne gidansu, yaďan yi gyaran murya yana faďin yadai beauty??? koba'kya gidane??.
    Ajiyar zuciya taja ta ce, "ina gida zakazo ne??, eh indai kina bu'katar ganina sainazo??, sassanyar dariya tayi aini kozaka kasance dani koda yaushe zanso haka, amma yanzu kaga kayi aiki kagaji dan haka kaje gida kayi wanka kaci abinci ka kwanta ka huta.
    Murmushi yayi tamkar yana gabanta, murya 'kasa2 ya ce, "ina gwauro yaga duk wanan gatan beauty!!?, dariya Ameeda tayi sosai, wlhy kanada abin dariya, yanzu dakanka kake kiran kakanka gwauro??.
     Shima dariyar yayi, to aii gsky ce beauty, kinga da inada mata da yanzu kafin na isa gida an haďamin ruwan wanka, idan nayi kuma ga abinci yana jirana, kilama saboda gata abani abaki, to amma yanzufa?, dole duk abinda nalissafo nizanma kaina.
          Ameeda ta gyara kwanciyarta to yayana kadage kayi auren mana musha biki, kaga idan kayi aure to koda yaushefa ina gidanka ina taya aunty na aiki da hira kafinkadawo.
     Tofa yafaďa yana murmushi, beauty to idan kuma kece kika zama matar tawafa???, ido tazaro da sauri kamar tana gabansa, tabďija yayana bar wananan zance kaji yanzu dai bari nabarka sai anjima,, kafin ya farga ta kashe wayar gaba ďaya, yayita kira amma akashe, daga baya saiya ha'kura yanufo gidan falmata kawai.
        A 'kofar gidan falmata yay fakin yasamu yaro ya ayka dan akira masa Ameeda, shigar yaron babu daďewa suka fito da falmata, saida ta gaisheshi sanan ta ce, "ai tana gida yauma batazo nan gidanba kwata2, cikin mamaki yake kallonta ya ce, "dama tanada wani gida bayan wannan??.
    Lah bata ta6a gaya makabane, ainan gidanane nikuma 'kawartace, kai ya girgiza to shikenan, dan ALLAH kozaki iya yimin kwatacen gidanne??, babu damuwa ai bawani nesa baneba, kwatance tashiga yimasa, ta ce, "damma inada ba'ko dana rakaka kawai.
   Babu damuwa yafaďa yana tada motar, bankwana yay mata yatafi.
    Yazo gaf dazai fita layin ya haďu da motar Nas, bin motar yayi da kallo harta shige wanan ai Naseer ne mikuma yakeyi anan anguwar??, kardai ďan isakan yaronnan yazo yayta 6ata 'ya'yan jama'a a garinnan??.
     Da yayi tunanin yabi bayansa saikuma yafasa ya hau babban titi yanufi gida, yama fasa zuwa gidansu Ameedan kenan.

  Bayan kamar kwana biyu da faruwar hakan saisuka sake haďuwa da Naseer a anguwar, amma shi Nas baiga Muzzaffar ba, Muzzaffar ya ce, "Beauty dan ALLAH kinsan wancan guy ďinne??, cikin damuwa ta kalleshi ta ce, "miyasa kamini wanan tambayar ne??, saboda naga kina ganin shigowar motarsa kika kwantar da kujerar baya, kuma kin matu'kar shiga ruďani.
     Ajiyar zuciya taja tareda zubo da hawaye daga idanunta, ta ce, "karka damu dashi, a'a beauty dolene nadamu dashi dominkuwa nasansa nasan koshi waye, irikice take kallonsa cikin tsoro kuma, a ina kasansa dan ALLAH????.
    kansa ya maida ga titi yana faďin kifara sanar dani ala'karku sanan saina sanar dake nima,, cikin rawar baki tace shinefa saurayina danake gaya maka ďinnan, hazbinallahu wani'imar wakil yashiga ambata, arikice ya ce, "Ameeda yau inaso ki kaini ainahin gidanku.
     Nanma cikin tsoro take kallonsa ta ce, "badaga gidan namu mukeba yanzu,, kansa ya girgiza tareda yin fakin agefen titi, juyowa yayi sosai yana kallonta, Ameeda banan bane ainahin gidanku, nan gidan 'kawarkine falmata, amma idan kin bani dama yanzunnan zan kaiki ainahin gidanku inda mom & dad naki suke, yana gama faďa yatada motar.
     Gaba ďaya zufa ta wanke jikin Ameeda, tanajin kunyar 'karyar datayi masa gsky,, amma ba laifinta bane rayuwace tamaida ita haka.
    Tiryan2 yaringa bin hanya kamar yata6a zuwa babu indà ya tsaya sai'a 'kofar gidansu Ameeda, yajuyo yana kallonta beauty ga gidanku nan.................

Ku biyomu.

©2017

Hikayarmu!!!!!.
     abba gana
                 &
           bilyn Abdul.
[24/02 17:32] bilyn Abdul: KUKAN KURCIYA..........

NA
MUH'D ABBA GANA
        &
BILKISA IBRAHIM
  (☆bilyn Abdul☆)

Page1⃣9⃣&2⃣0⃣

.........Bayan an yayyafama Ameeda ruwa ta farfaďo, ya Muzzaffar ya zaunar da ita, ruwa dady ya mi'ka mata tasha tana hawaye, cikin kuka ta ce, "ya suwaye waďannan dan ALLAH???.
     karki damu 'kanwata ashirye muke damu sanar dake komai, dan haka ki kwantar da hakalinki.
    Dubanta ta maida gasu iya abu dake durkushe sunata rawar jiki harda kuka, ahankali ta matsa kusadasu tana faďi iya miyake faruwane agidabnan??, shin kunsansu ne?? Idan kun sansu suwaye su??.
    Babu wanda yabata amsa acikinsu saima rawar jikinsu dake 'karuwa, ta ďauke kai daga garesu ta maida kan Nas dake tsaye shima tamkar gunki daka gansa kasan arikice yake, jira kawai yake yasami hanyar dazai arce amma babu dama, dan tuni polis sun dunkare 'kofar gidan.
    Waya daddy yayi tareda faďin kushigo ku kwashesu dan yanzu zamu koma abuja acan zamuyi komai daya dace.
   Okey sir suka faďa suna ďirarowa cikin gidan tamkar tururuwa, tamau aka dam'ke iya abu da malam dauda da Naseer aka yayibesu sai mota, 'kofar gidan cike yake da al'ummar annabi sai kallo da dariya akema su iya abu, su mutane azatonsu wajen kwaďayin 'yarsu ta auri mai kuďi suka kwaso wanda yafi 'karfinsu, mota aka cimimiyasu suna kuka da ro'kon ayi hakuri babu wanda ya sauraresu saima wani ďansanda daya kwalama iya abu bakin bindiga a 'kafa, tako daddage ta kwala ihu.
      Acikin gidan kuwa tuni Ameeda ta ruďe tana kwasar kuka dakyar suka lalla6ata tayi shiru, momy ta ce, "idan kinada wani abin bu'kata ki ďauka dan daga nan har abada bazaki sake zuwa gidanan ba, cikin mamaki Ameeda take kallonta amma babu damar tambaya dan tana tsoron kar itama asaka 'yan sanda cimimiyar ta yanzunan.
    Kayanta ta haďo dady yakama hannunta haba baby indai sutturace abinda kike bukata kawai to kibarta mu tafi komai kike bu'kata zamu yimiki da izinin ALLAH kinji.
     Kai ta jinjina tareda ajiye jakkar kayan ta ďauki ďan abinda ba'a rasaba suka fice, har yanzu mutane suna tsaytsaye a kofar gidan dan su iya abu ana motar 'yan sanda, suna shiga motar polis suka take musu baya sai abuja garin naira.
        Koda suka iso 'yan sanda wucewa sukayi dasu iya abu polistion sukuma suka wuce gida.
     Aljannar duniya ameeda tafaďa azuciyarta, gaba ďaya tazama 'yar 'kyauye, taga gida tamkar baza'a mutuba, saida momy takamata ta zaunar sannan, mizzaffar sai dariya yake mata, tana kallonsa amma tayi burus dashi tanabin ko ina da kallo, ruwa 'yan aikingidan suka kawo musu tareda kayan motsa baki, ďaya acikin 'yan aikin ta rissina tana faďin momy akawo abincine??.
   Momy ta girgiza mata kai, a'a magajiya abarsa saimunyi wanka sanan, to hajiya afito lafiya.
   Muzzaffar yami'ke yana faďin kunga nayi nana.
   Momy ta ce, "to saura kuma ka kwanta barci, kanayin wanka kazo kaci abinci, karki damu momyna kibani minti talatin.
   Kai ta ďaga masa tana dariya, saida ya haye samansa sanan ta kama hannun Ameeda tana murmushi babyna zomuje kiyi wanka kinji, itadai ameeda tamkar makaho da ďan jagora haka takebin momy har zuwa ďakinta.
    Yasalam ameeda tafaďa azuciyarta, bedroom ďin yatafi da imaninta wani abin kallo sai a bathroom tamkar wajen cin abinci, bayin ya haďu, itadai haka tayi wanka tafito, saimada momy tanuna mata yanda zatayi sanan.
    Bayan futowarta momy ma tashiga wankan, bayan ta nuna mata kanayan kwaliya dakuma kayan sawa data ajiye mata akan gado.
   Tashirya tsaf cikin jar doguwar rigar mai adon fararen duwatsu abinka ga fara tayi mata ďas kamar dan ita akayi.
    Momy ma tafito tashirya, sukayi sallar la'asar dan tama ďan shige lokacinta.
    Afalo suka tarar da ya Muzzaffar da dady suna jiransu a dinning.
     Momy tazauna kusada dady, itama ya Muzzaffar ya nuna mata kusadashi, babu musu taje tazauna, aka haďama kowa abinci agabansa sanan sukai bismillah suka hau ci.
    Itadai ameeda akunyace takecin abincin har saida daddy yay mata magana, babyna kodai dakaina zan baki abincinnan dai?, hannu tasa tarufe fuska tana dariya a'a dady zanci da kaina.
     To yakamata kam, kisaki jikinki baby nan gidankune, bakida inda yafinan kinji, dummm taji kanta yayi, wai ita wane irin ruďani ake shirin sakatane??, tagaza gane wanan rikitaccen al'amarin??, ya Muzzaffar ya ta6ata, taďago tana kallonsa da ido yay mata alamar taci, ďan murmushin ya'ke tayi tacigaba dacin abincin.
   Su momy suna kallonsu.

Dahaka dai suka gama cin abincin suka tashi, dady ya haye samansa sukuma suka zauna suna 'yar hira, wadda duk anayine dan ameeda tasaki jikinta.
     Momy taje ďakin daddy, ta ce, "Alhaji nifa yau tareda baby zan kwana nayimaka yaji, yay murmushi a'a hajiya ainima ban yardaba saidai tazonan mukwana tare, murmushi momy tayi ta ce, "to inaga hakan zaifi sau'ki kam.
    Ranar agado ďaya ta kwana da momy da dady, sukasakata tsakkiya, (araina nace kai 'yan boko sai abarsu, wananan gandamemiyar budurwar za'a kwana gado ďaya da ita in bandadai.........baridai nayi shiru, ALLAH yashiryemu).............

Ku biyomu.
Chapter 6 · 0% Book details