← Book details  Kukan Kurciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 9

Sashe 3

 Kukan Kurciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

   ke k'aramar 'yar iska har kin isa nabaki umurni ki bijire? kodan kinga ina lallabakine??.
    Ameeda tayi masa kallon sama da k'asa ta ce, "To Nas kai ubanane dabazan bijirema umar ninkaba, kaima kasan idan har na ce, "bazanyi abu ba, to bazanyi d'inba", dan haka ka saurara mini, ina sauran 'yammatan naka kad'auki d'aya acikinsu mana ta rakaka.
   Nas ya finciko Ameeda cikin xafin nama ya had'eta da bango, cizo ta galla masa ahannu, da sauri ya saketa, ta nunashi da hannu kai Nas kasan nasha fad'a maka, duk iskancinka kadaina gigin tab'amin jiki, wlhy kashiga hankalinka, idan har bazaka iya fad'a min magana daga nesaba to ka saurara, niba 'yar iska bace kajiko!!.
    tana gama fad'a ta fice, atsakar gida ta tarar da falmata itada bad suna hira, kallo d'aya tamusu ta d'auke kai tana tsaki, daga nesa ta ce, "falmata nawuce gida saida safe.
   Falmata ta ce, "kai Ameeda bazaki kwanan anan bane??, ko yau bazakije club bane?.
   Ameeda ta yatsine fuska tana fad'in bazanjeba, inaso naje gida dan nafad'ama iya cewa zan dawo dawuri.
   To shikenan saida safe, falmata tafad'a.
   Bad ya ce, "Ameeda abin ko gaisuwa?,.
   "O, sorry ban kula dakai bane ykk?".
   Ya ce, "lfy lau, ya garin.
  Gaba tayi abinta ba tare da ta amsashiba.
   Bad yamaida kallonsa ga falmata, wai ita wannan k'awar taki miye damuwarta, kodai Nas ne ya b'ata mata rai??.
   Falmata ta ce, "k'ila hakane amma dama tun d'azu ranta ab'ace yake, shine dalilin dayasama ta d'au caji.
   Bad ya ce, "wlhy dani nakeson yarinyar can datuni na shak'ama shegiya koken, nayi abinda zanyi, narasa mike damun Nas da har yarinyarnan tafi k'arfinsa.
    Hummm kajika dawata magana, tunda bataso yazaiyi, wlhy nakula Ameeda bata buk'atar wannan harkar, dan ALLAH ku barta, indai dan ALLAH yakesonta to ya aureta kawai, amma indai ta wannan hanyarne bazai tab'a samun Ameeda yanda yakesoba.
   Habawa falmata bakisan Nas bane kawai, na tabbata wataran sai yakaiga samun nasara, kedai kisa idanu kisha kallo kawai.
   Dariya kawai falmata tayi dan tasan hakan bamai yuwuwa bane, tasan tasha cin kud'in Nas akan yanaso ta shawo masa kan Ameeda ta yarda dashi, amma takasa.

Aban garen Ameeda kuwa tana fita ta samu adaidaita ta hau, sai gida, sallama tayi tare da shiga cikin gidan babu kowa a tsakar gida, d'akin iya tanufa, amma babu kowa, saita wuce d'akinta kaiwai.
   Tacire kaya ta kwanta, babu dad'ewa ta fada duniyar tunani, tabbas indai tana tareda Nas bata tunanin zata shiryu, lokaci yayi dazata nisanta kanta dasu Nas, to amma iyayentama suna taka rawar gani wajen lalacewarta, kenan suma dolene ta nisancesu?, to inta bijire musu ta tafi ina zata?, a kano tatashi tayi wayo harta mallaki hankalin kanta, itadai batasan wasu 'yan uwansu dasuke nesaba, to miye mafita??.
   Zata cigaba da zama dasune?, kokuwa zata kama gabanta domin daidaita rayuwarta?, kullum shekarunta k'ara ja suke, tanaso tayi aure ta haifi yara, amma bata fata Nas yazama mijinta uban 'ya'yanta, wace hanya yakamata tabi domin gujewa auren Naseer??.
  Tajuya kwanciyarta zuwa rubda ciki, wayarta tad'anyi k'ara alamar shigowar sak'o, ahankali takai hannu ta d'auka, Nas ne yaturo mata sak'o.
    Ta ajiye wayar batareda sha'awar duba sak'onba, sai kuma ta d'auka ta duba.
     Ga abinda ke ciki....
   Hy babyna
Plz kiyi hak'uri da abinda nayi miki, nayi miki alk'awarin bazan sakeba, amma dan ALLAH kiyi hak'uri ki halarci birthday party  d'inan, dan wlhy duk cikin 'yammatan kece mai kala, kin fisu aji, kuma kece nake burin ki zama uwar 'ya'yana, dan nasan zasuyi alfahari dake a matsayin uwarsu.
   Saina jiki.
  I luv u my dear.
      Naki NAS!!!.

Tsaki tayi tana fad'in shasha sha ai wlhy duk dad'in bakinka babu inda zanje, kuma ni bana fatan kazama mijina, dan 'ya'yana bazasuyi alfahari dakaiba a matsayin ubansu.
  Taja tsaki tareda wurgar da wayar saman katifar ta.

Iya talek'o tana fad'in Ameeda sai yanzu??.
   Ameeda ta tashi zaune wlhy kuwa iya, amma nad'an dad'e da dawowa na lek'a d'akinki bak'ya nan.
  Eh naje  gidan malam D'anladi, matarsace ta haihu d'azu.
   Ayya ALLAH yaraya, mi'aka samu.
   Mace ta haifa tanana sarga d'ed'iya, iya tafad'a tana washe baki.
   Ameeda ta ce, "masha ALLAH.
  Kinci abinci ko, iya ta tambayi Ameeda??.
   Eh, kawai Ameeda ta ce, "mata.
  To aii shikenan, kinga bari naje nacinye wanda na ajiye miki dama wlhy bai isheniba.
    Ameeda ta girgiza kai kawai, danjin furicin iya abu, ta shafa cikinta tare da fadin  a cikin ranta wlhy yuwa nakeji ba k'aramaba, dan tun safe rabonta da abinci.
   Kud'i ta d'auka tafice, wajen wani mai shayi taje tasiyo soyayyar indome da kwai, da shayi, tazo taci takoshi, sannan tasamu sa'ida.

WASHE GARI
   tunda safe tashirya tabar gidan, dan tasan Nas zai iya zuwa yasa su iya su tursasata zuwa Abuja.
   Itako wlhy bazata jeba, gidan wata aunty ta tatafi, tawuni acan sai dare tadawo.

   ko hutawa batayiba iya abu ta shaida mata zuwan Nas, wai haryabasu kud'i, amma ransa ya b'aci daya tarar bata nan.
   Baki Ameeda ta tab'e ta ce, "matsalarsa ce kuma wannan, nidai tunda nace bazaniba ai dole a sauraramini.
   Tamik'e tashige d'aki tana mita...................

Ku biyomu!!.

.......har suka tsaida adai2ta sahu suka shiga yana kallonsu, da hanzari ya tsaida wata shima ya hau, ya ce, "mai adai2ta wancan matan zamubi, to mai babur yafaďa, haka sukaita binsu Ameeda lungu da sa'ko har 'kofar gidan falmata, daga ďan nesa dasu suka tsaya, saida yaga inda suka shiga sannan yace mu juya kawai, mai adai2ta ya juya kan babur ďinsa suka koma.
    Koda suka koma asibitin bai iya shigaba sai kawai ya shiga motarsa ya fice, wani ďan matsakaicin gida yaiso, fakin yayi, cikin hanzari yashiga gidan, agurguje ya haďa 'yan kayansa kala biyu aďan 'karamin  akwati,  ya ďakko zuwa mota, komawa yayi ya kulle gidan sannan yadawo yayma motar key yafice daga anguwar,, babban titi yahau yarin'ka sharara gudu(araina na ce, "waishi wanan mike damunsane????).
    Hanyar kaduna yanufa daga kaduna yaďau hanyar abuja, 'karfe uku a abuja tayi masa saboda uban gudun dayayta shararawa ahanya, wata haďaďďiyar anguwa yashiga woow!! Nafaďa azuciyata lallai anguwar tahaďu masu karatu, hon yayi a'kofar wani 'katon gate, dagudu mai gadi yabuďe masa ya danna hancin motar ciki yana ďagawa mai gadi hannu, a yalwatacciyar harabar gidan yayi fakin ya sakko daga motar yana mi'ka dafaďin Alhmdullh, ya lankwasa yatsunsa sukayi 'kara sannan ya shiga cikin ainhin gidan.
   Da sallama yashiga 'katon falon daya tsaru da kayan more rayu babu kowa sai ac daketa faman aikinsa, tv falon ma tanata 6a6atu, ya wuce abinsa zuwa ciki,, nanma wani falonne tsararre annan ya tarar da mutanen gidan, dagu wasu yara 'kyawawa kansu ďaya sukazo suna faďin uncle oyoyo,, yataresu cikin farinciki tareda ďagasu ďai2 yana sumbatar kumatunsu, suma yabasu nashi suka sumbata, gaban wata matsakaiciyar dattijuwa yaje ya tsugunna yana gaisheta, ta amsa fuskarta ďauke da murmushi Muzzaffar ďina lafiya kuwa naganka agida kuma yau ba weekend ba??.
    Kansa yashafa yana murmushi, wlhy kuwa momy hakanan naji ina marmarin ganinku shiyyasa nataho,, kumani wlhy zaman kano ďinnan ya isheni sonake adawo dani nan kusadaku.
    Murmushi dattijuwar tayi tana tashi zaune daga kishingiďar datayi karka damu Muzzaffar insha ALLAHU kwanannan zaka dawo abuja da aiki, dan har nayima kawunka maganama, yauwa momcyna yafaďa yana kwantar da kansa gefen kafaďarta,, momy ta shafa kansa to kaga tashi kaje ďakinka kayi wanka saikazo kaci abinci ko??, dama kamar nasani nasaka hama ta gyara maka ďakinka,, fuska yaďan yatsine kai momy banace 'kazamar yarinyarnan tadaina shigar mini ďaki bane??, da'kuwa momy tayi masa kaci gidanku muzaffar bana hanaka wanan halinbane??, yaďan shagwa6e fuska tareda hađe hannayensa biyu yana faďin sorry momy bazan sakeba.
    Yauwa ďan albarka jekayi wankan kaji.
   Ďakinsa yanufa wanda ya tsaru shima komai na ďakin farine tas, na ce, "lallai kanada tsafta malam,, dan 'kazami baya maida komai nasa fari haka, ďakin sai tashin 'kamshi yakeyi, ya cire kayan jikinsa ya ďaura farin tawul yanufi bayi,, komai na bayinma farine tas masha ALLAH, babu 6ata lokaci ya salla wankansa yafito ya shirya cikin wando fari iya gwuywa da pink ďin riga 'karama, ya gyara sumarsa tareda feshe jikinsa da turare sanan yadawo falon.
    Dinning yanufa wanda aka cika taf da kayan abinci saikace zasuci su goma, 'yan yaran ďazu sukazo suka haye saman kujerun dinning ďin suna faďin uncle muma zamuci, murmushi yayi musu tareda jan hancinsu to my dota's, dakansa yazuba musu sukaci suka 'koshi bayan sun kammala suka dawo falon kusada momy suka zauna, suna nan zaune suna 'yar hira har aka kira sallar la'asar, tashi yayi yanufi masallaci suma su momy suka nufi ďaki domin gabatar da tasu sallar.

Bayan yadawo kai 'tsaye ďakin momy yanufa tana zaune saman sallaya tana lazumi yawuce bakin gadonta ya kwanta saida ta idar sanan ya ce, "momy ina yini?, lafiya lao muzzaffar ya gajiyar tafiya??, to Alhamdllh momy,, masha ALLAH ai haka akesonji.
     Ya ce, "momy nifa wani abun mamaki nagano a kano yau, da sauri momy ta ce, "wane iri muzzaffar?, kasa yasakko ya zauna kusada ita, wlhy momy natafi zan shiga asibiti sainayi gamo dawata budurwa mai tsananin kama dake kamar antsaga kara an karya.
    Arazane momy ta ce, "muzzaffar da gsk kakeyi kokuwa wasa??, yaďan jinjina kai wlhy momy da gsk kinsandai ban ta6a kawo miki makamanciyar wanan maganarba, ta matso kusadashi cikin zumuďi ta ce,, "kasan daga ina take??, kai ya sake girgizawa A'a momy amma dai naga inda suka shiga itada 'kawarta,, masha ALLAHU yarona kayi "kyan kai,  gobe idan ALLAH yakaimu zamu juya kano.
    Da sauri ya ce, "A'a momy bama saikinjeba kibari nagama bibiyar yarinyar, idan naďan ga wani abu gameda sirrinta saimuje harda dady, kinga babu dađi kiyi tafiya yanzu dady bai saniba ko???, shikenan muzzaffar kaima kakawo hanzari maikyau momy tafaďa cikin raunin murya.
    Labarai masu daďi yayta kwakwaloma momy danta saki jikinta, yansan yanzu saita burkice musu, dama kwanan suka samo kanta da'kyar akan wannan matsalar, saida yaga tasaki jikinta sanan yatashi yafice daga ďakin, daga nan addu'oi mamy tacigaba dayi ALLAH yatabbar musu da farincikin dasuka rasa na shekar masu yawa,, ALLAH yakawo musu'karshen wannan damuwa tasu. (Muka ce, "amin momy, dukda bamusan wacce irin damuwace ta dabai bayekuba).
Chapter 3 · 0% Book details