← Book details Me Gadi Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 8

Sashe 8

Me Gadi Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Habawa!!! Ji tayi kamar ya watsa mata garwashin wuta .
Take anan ta tattare giran sama da qasa ta fara nuno shi da wayar hannun ta ,tana masa diban karan mahaukaciya daga sama zuwa qasa.
Cikin muryarta mai fizga mai sanyi amma sound dangerous ,tace "Me hakan ke nufi?🤨"
Watsa kyawawan yatsunsa yayi akan motar da yake goge mata ,ba ko alamar damuwa a tare dashi "Gaishe ki nake yi"
Hangame baki tayi shaqe da mamaki .
"Gaisuwa😎? Haka aka koya maka gaisuwa a garinku? See point of correction....Hajiya Ahlam ake kira na ba Ahlam ba ,and.....Ina kwana zaka na cewa ba wani Hi ba .ai ka gane ko?🤨"
Watsa hannunsa yayi freely cikin rashin damuwa "Oh pointed👌🏾Hajiya Ahlam"
Ji tayi kamar ya watsa mata wuta ,don haka ta sake hassala
"See karka 6ata mun lokaci i've zero tolerance to nonsense ,ban daukan raini.......meye ma sunanka?"
Cikin karsashi irin na en gayun mazan en boko yace "Mahmood"

Caɓe baki tayi ta mere hanci ta lalata sunansa ta hanyar cewa "Mamuda"
Dago mata dulu dulun sexy eyes dinsa yai ya kafeta da ido wanda yasa ta kautar da kai gefe da sauri batare da tasan dalilin hakan ba.
"Mahmoud" ya sake kiran sunansa da wani irin murya mai katse jijiyoyin jikin diya mace .

Zata sake magana saiga Lailah ta fito "hey babes mu tafi ko?" Qyam ta hadiye maganarta ganin gogeous ingarman namiji a gabansa ya tara muscle a damatsa kai da gani kasan akwai training ga kyau ga swaggs .yana sanye da nikkers da hoodie .gabadaya burkita mata tunani yayi nan take ,ita kuwa Ahlam na can na busy bodyn rashin mutunci
"Dallah shiga ka tuqa mu muje Ni ka ishe Ni da iyayi ,wai Ni a wani waje ne aka kwaso mun wannan ?"

Bai tankata ba ya juya yana bubbudawa yana tafiya shi a ganinsa normal ne amma a wajensu wani irin tafiyar manyan gayun nan yake wanda suka nitsu a cikin daloli ,tamkar wanda ana ce masa hey zai kyautan miliyan goma amma wai driver dinta ne .
Daga Ahlam har Lailah bin bayansa sukayi da kallo har ya kewaya wajen driver
Kana Ahlam ta katse shirun da cewa

"Mtsewwww shi wannan forming din nan menene? Wai yana yin big boy ne ko menene Ni na kasa ganewa?"

Laila da tayi kamar goluwa sauke murya tayi da sauri tana tambayar ta "babe waye wannan ? This is fine boy meeeensss"

"Mmtsew sabon driver na ne dallah😏gashi tun yanzu is getting out mu nerves wai fa kiran suna na yai gatsal yana wani ce mun Hi kamar tsaransa"

"Babe Allah yayi halitta a wajen nan ,gayen nan is vibing wallahi ,ki gode ma yayi adressing ɗinki da yaransu na en gayu not like sannu Malama..."

"Oh shut up☹️"

Tsuke baki tai tana murmushi gaba daya ta mace a kansa lokaci daya taji kamar ta fara sonsa . Zabura tai zata bishi wajen motar ta fincikota da sauri Are You mad? Meke damunki ne qawata ? Mushiga daga ciki oya mu koma plz relax now.....

Taja hannunta suka koma dakin da sauri tana tsoron kar ta hankade masu ajinsu.

Oum Aphnan
Chapter 8 · 0% Book details