← Book details Me Gadi Na Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 8

Sashe 1

Me Gadi Na Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[6/18, 3:13 PM] Chuchu👻: ✺ ✺
✺ME GADI NA✺
_(My Gate keeper)_
Page 001
☎️ +234 906 029 1568

Bismillahir rahmanir raheem

Tunda ta shigo Area ɗin gidansu take sakin Horn tana falfala gudu, tamkar wanda ƴan sanda suka biyo masu laifi.
A gaban ƙatoton mansion din gidan fari tar Gilasan windows ta ko'ina sai walwalin kalan sararin samaniya suke,lafcecen gida ne kamar an dasa shi a wajen bene hawa biyu ta sama ga kuma gidan ƙasa, an yayyaɓe gidan da adon furanni koraye shar shar.tabbas wannan gidan yafi kama da gidan mashahuran ƴan Boko masu Aljannun kuɗaɗe wanda sam basu san talauci ba.

Wani wawan birki ta riƙe a daidai gaban Gate din gidan me kama da na sarauta saboda yanda aka ƙawata dogon gate ɗin baƙi wuluk da kwalliyar Royals da zaiba-zaiban Golden.
Cigaba da sakin Horn takeyi irin mai tsawon nan da ke haddasa ma mai saurare faɗuwar gaba.

Baba Uwale mai shara, wacce ta fito daga BQ din gidan ta rako ɗan Uwanta Mahmud da ya kawo mata ziyara, taji Horn ɗin motar masifaffiyar gidan wato Ahlam, ai tuni ta nemi fita a hayyacinta nan take ta falla da gudu wajen Gate ɗin tana ƙwalla ma me gadin kira

“Tanimu... Tanimu, kazo ka buɗe Gate mun shiga uku” Tanimu kam ya ƙure a ɗaki sai shaƙar barcinsa yake.
Dukan ƙofar ta fara yi a firgice tana cigaba da kiran sunansa Ga Ahlam sai ƙara tsananta Horn ɗin motar takeyi.

Mahmud da ya ƙaraso bakin Gate ɗin ganin duk yanda ƴar uwarsa ta ruɗe bai tsaya wani jiran me gadi ba yasa hannu ya janye saƙatan gidan ya warware Gate ɗin, ai a bala'ance ta wawuro motar ɓuuuuu ta shigo gidan , kaɗan ya rage ta take masa yatsun ƙafa. Amma da yi ke namijin duniya ne ko girgiza baiyi ba balle wai yayi tsalle ya ja gefe, haka ya jira ta wuce ya koma yana maida Gate ɗin yanda yake.

Sai sannan ne Tanimu ya fito daga ɗakin yana miƙa yana kwarara hamma
“What kind of stupid man are you? Didn't you hear the fines? ”(Wannan wani irin Wawa lusarin mutum ne, sai kace ba'a biyanshi Albashinsa?)
Kalaman da suke fitowa a bakin Ahlam kenan daidai sanda ta ɓalle murfin motar cike da masifa ko tsayawa rufe kofar batayi ba ta tunkari Gate din da sauri.

shikuma Mahmud daidai yana maida Gate ɗin yana rufewa a nutsensa.

Kamar zararriya haka ta nufosu kallabin kanta ya kwance cikin jaraba da hargagi take tambayar Baba Uwale ina wawan can yake ehe... Where is that lunatic attendant where is he? Tana masifa gashin kanta na Zallan Fulani wanda ya kwance ya barbazu mata a gadon baya ya sa ta ta zama kamar damisa.
Daƙyar ta lalubo Baba tanimu wanda ya maƙale a bayan motar da ake fita masu cefane a ciki, aikuwa kamar mage da ɓera haka ta fizgo shi batayi wata wata ba, ta shararesa da mari. Ji kake fafassss!

Ɗif Baba tanimu ya daina gani “Kai wani irin sakaren mutum ne, ina ta Horn kaƙi kazo ka buɗe mun, what of if i am in a danger,is that how you will abundant me? shikenan sai dai in salwanta? Mtsewwwwww irresponsible nonentity, matsa ka Bani waje talo talon banza talo talon wofi.... ” ta wani wancakalar dashi a wajen bayan shaƙe masa kwalar riga da tayi kamar zata kashe shi.

Kamar damisa ta wuce fuuu zatayi hanyar shiga gidan, a rakuɓe cikin sanyin murya Baba Uwale ke tambayarta
“Ahlam lafiyar ki kuwa? "

Wani tsawa ta daka ma Baba tambaya “Gerrout!!!! " Tana firfito mata da duk luhu luhun Idonta kamar zata yanka mata mari.
Ai da sauri Baba Uwale taja gefe ta wuce cikin gidan da sauri tana yarfa masifa.
Sai sannan ƙawar Ahlam, wato Lailah ta fito a cikin motar hannunta riƙe da takardun amsa tambayoyin da akayi masu Gwaji a makaranta (Question papers).

A sanyaye tazo ta wucesu ba tare da ta cema kowa komai ba tana gyara Rolling din mayafin abayarta.

Cikin damuwa Baba Uwale ke tambayar Lailah "Ƴan nan me ke damun Ahlam ne wai? "

Rau rau Lailah tayi da ido kamar za tayi kuka "Baba jarabawan yau ne baiyi mana dadi ba shiyasa" A sanyaye ta wai ga ta kalli Baba me gadi "Baba ka yi hakuri, ran Kawata a ɓace yake shiyasa ta juye fushin a kanka"

Rausayar da kai Baba Uwale tayi "To Allah ya gyara... Tanimu ina yawan fada maka kullum ka ringa kasancewa a bakin aikin ka sai ka shige daki daga barci sai sauraran wancan lalataccen rediyon mai ƙaran tsiya"

Mahmud kam wanda har yanzu bai cema kowa komi ba saidai ya kalli wannan ya kalli wancan yana sauraron drama din da akeyi. ,Har saida Baba Uwale ta dafa masa hannu “To Mahmudu muje in raka ka ka tafi gida ko? Na gode...Na gode da ziyara ka gaida mutan gidan ko? Allah yayi maku Albarka"

Saida suka fito wajen gidan sannan Mahmud ya samu zarafin yin mata magana
"Innanmu wannan wata irin yarinya ce? Ta yaya kike iya jure jumurin zama da ita? "
"Hum ɗan nan kai dai Allah ya gyara, Ahlam akwai tambotsai, haka take amma ni dai dashike ina kiyaye mata gaskiya bata yin mun kuma ko tana sakarcin ta, ina kwaɓa mata zaka ga ta bari, kasan rayuwar yaran masu kudin nan sai ana lallabawa, Uwarta tarbiyyar Yahudu da nasara tayi mata"
Mahmud fashewa da dariya yayi yana maimaita yanda Baba Uwale tayi maganar "wai Yahudu da nasara akwai wani tarbiyyan Yahudu da nasara ne? "

"Eh mana, kana ganin yanda ta kwasa ma tsoho nan mari? Kuma da mamanta nanan bin bayanta zatayi ƙila ma tace ta kara mashi, farfesa ne kaɗai mutumin kirki a gidan nan ,in yana nan tofah ya dinga masu masifa kenan,to kasan su kuma manya basa rayuwa waje daya kullum daga yana Ingila sai yana wancan ƙasa bai ma Faye zama a habujan nan ba"

"To kai kaji, Allah ya gyara"

"Amin dai ku dai ku cigaba da girmama mutane kaji? "

"Mu su waye mu in muka wulakanta tsoho ai sai mu kara ke barbadewa, Innanmu ki koma gida haka nan ko? "

"To mahmuda Allah ya kiyaye hanya"

✺✺✺

"Ahlam you are so so insulate, halin ki bayi da kyau akan meye zaki kifa ma tsoho mari, idan jarabawa yayi maki zafi sai ki transforming anger dinki a kansa? Shi ina ruwansa? "

Ahlam da ta rasa tudun dafawa kawai sai ta fashe da kuka
"Lailah ki kyale ni Dallah in ji da abunda ya dameni, saida nace ma Daddy ni Civil law zanyi, ya tashi ya hada mun wannan wawan combination din, Civil and shari'a law, yanzu gashi aita mana Tambayoyin larabci da wasu na addini kalan mutum yaje ya samu carry over CGPA dinsa yayi ta kasa... Ni wallahi na tsani na Islamiyya dinnan"

Lailah da itama taji jiki a jarabawan yau din samun gefen tafkeken gadonta da yasha shimfidun alfarma tayi ta zauna "Kinga Ahlam dani dake fa duk jarabawan nan ta yi mana zafi amma ne yasa ke ba zaki iya ringa rike fushinki ba? "

"Aike gwara ke kina da Arabic background ni da ba a kasar nan nayi primary da secondary ba ta ina xan iya amsa wainnan hard questions din? Karki manta i'm from Spain hausan ma yanzu nake koya talkless of Arabic"

"Yes haka ne, ni gwara ni da sauƙi but Ahlam gskiya baki kyauta ba, kawai mu je ki ba ma baban nan haƙuri ya isa fa ya haife ki yayi jika ma dake, ke baki jin wani iri? Duk mai aikin dake karkashinki sai kin tozarta shi a ƙarshe ki koreshi, ko don kinga dady basa nan? To wallahi takan mutumin nan sai ki kasa cin jarabawan ma gaba ɗaya... "

Sosai jikin Ahlam ya ɗanyi sanyi don haka ta ja siririn tsaki "Ok zan tura masa da dubu dari anjima ta account Nasan zai haƙuri"

"Ahlam No! Kudi yana siyan komai amma banda mutunci, go and beg him , Ok? "

Ahlam a sanyaye ta Mike ta dauko kallabinta da tayi jifa dashi a kan gado ta Daura a saman tulgujejen gashin kanta ta dauki wayarta suka fito harabar gidan

"Baba tanimu... Baba... " Hadiye miyau din bakinta tayi sakamakon ganinsa rike da jakan ghana must go Baba Uwale na rarrashinsa amma ya tubure sam sai ya tafi.

Dafe kai Ahlam tayi "Wash Allah na, Baba kuna da saurin fushi, you want to quit your Job saboda na mareka? Mari fa kadai, Turawa ba kalan cin kashin da bama yi masu suna liƙe... "

"Turawa ki kace shi kuma hausa /Fulani ne is a great taboo ko a Musulunci ƙarami ya zagi babba talkless of Mari" Lailah ta bata amsa a fusace.

Sanyi da murya Ahlam tayi "To Baba tanimu kayi haƙuri ka gafarta mun ba zan kara ba wallahi jarabawan nan ne yayi mun wuya shiyasa... "

✺ *KASUWAR TALLA TA HAJA* ✺
*BAKIN. MALLAKA , FARIN JININ SAMARI , KIRANYE , FARRAKA MIJIN DA MATA , DA YARDAN ALLAH*💥💥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

Assalamu Alaikum warahmatullah🙌🙌🙌

Fatan kowa na cikin koshin lpy Allah kasa haka ameen

Ina masoya kuma mabiya Buxuwa empire🐪🐪🔥🔥🔥 08126535394 , 08139762831

Ina manyan mata masu fama da matsala na yau da gobe a cikin gidajen su ...

💥 Ina yammatan mu masu son a ce yau sun bar gaban iyayen amma abun yaci tura

💥 Ina macen da takeson yau ace ta zamto na gaban goshin me gidan ta amma yan matan yanxu sun hana mata sukuni.

💥 Ina macen da takeso kwanciyar hankali a cikin gidanta amma abun ya faskara

💥 Ina mata , yammata , zaurawa masu fama da matsala ta iska ( Aljannu👹👹👹👹👹👹) wanda ya hana maka sukuni da kai da iyalinka , ko yammata da yagana masu samari ,ko mijin aure wannan yazo gobe bashi zai dawo ba , kaii akwai wacce zakaga bata taba saurayin ba...

Kuma kina zaune bayan kinsan *Hajiya safiyya (Buxuwa empire)* 08126535394 , 08139762831 Dodon wa 'innnan ne , wacce ta fiki damuwa tazo kuma matsala ta kau da yardar Allah...
Chapter 1 · 0% Book details