← Book details Matar Hariji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 25

Sashe 4

Matar Hariji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya sunanki?" haɗiye kukanta tayi tace "Jiddoh Arɗo Jibir" iska ya furzar ya miƙe yace "ok gobe kizonan idan kin ɗauko nonon ki kawo min zan siya zan taho da likita yayi miki allura kinsan cizo kare dafine dashi ƙafarki zata iya ruɓewa idan baayi miki allura ba, na nawane nonon dasu Idin suka shanye miki"

Shiru tayi kamar bazatayi mgn ba ta fara haɗe kayanta bayan ta gama ta miƙe zata tafi ya riƙe hijjab dinta fuskarsa murtuk ya zaro dubu biyu ya bata yace "ki ajiyemin canji na gobe zan karba kada Goggo ta dakarmin ke" ƙememe taƙi karɓar kudin wai dukanta zaayi nononta na jaka huɗu da rabi ne.

Kama gefen kallabinta yayi ya ɗaure mata dubu daya ya bata ɗaya a hannunta yace "kice da goggo wani ne ya siyi nono babu canji shine yace gobe kibashi na rabin jakar"

Dariya tayi tace "aradun Allah kaɗo kanada wayo sosai zaka tai dani burni na ƙaro wayo?"

dariya ta bashi ya shiga motarsa ya kunna tana tsaye har yayi kwana zai tafi ta bude baki tace "Kaɗo" juyowa yayi ya tsaya wai kaɗo sai kuma yayi murmushi ya daga mata hannu itama ta daga masa hannu ta juya ta tafi, yabi bayanta da kallo yana ajiyar zuciya a hankali yace "Hauwa'u kulu Maijiddah.

Figar motar yayi a guje ya fice daga lungun tundaga wannan lkc ya kasance kullum shine yake siye nononta idan ta dauko idan kuma zaiyi tafiya bazaizo ba to yakan bawa manajan gdan gonarsa kudin ya rinƙa bata kullum hakanne ya wanzar da shaƙuwa me ƙarfi tsakaninsu.

ASALIN LABARIN

___________Tananan zaune a wannan guri har duhun magaruba ya fara sawo kai ta miƙe a hankali ta fara fita daga saƙaƙiyar har ta fito titi sosai ta fara tafiya cikin rashin kuzari har ta isa rugarsu takuwa yi saa Allah bai haɗata da ƴan dumbule ba don ta lura nononta da Allah ya wadatata dasu suna mugun jan hankalin maza duk da cewa kullum cikin taresu takeyi da hannunta kasancewar ba bra suke sanyawa ba haka suke yawo da abunsu a tsaye cako cako wannan dalilin yasa kullum take taresu saboda kunya takeji taga sunyi cokal cokal dinnan.

Isarta gda kenan taga gilmawar wata baqar LAND GRUSSER ta bayan bukkokinsu a guje hakanan taji gabanta ya fadi tanason ganin waye a ciki amma babu dama da alamun na cikin ma a fusace yake.

Ƙwafa tayi ta shiga gdan nasu taja tayi turus ganin ƴan gidan nasu gabaɗaya tun daga kan baffansu har zuwa kakansu mahaifin baffansu kowa yayi cirko cirko suntada gemu da alamun wani abune mara daɗi ya hwaru batasan hawa ba balle sauka taji an fincikota tsakiyar filin da mutane sama da talatin sukayiwa da'ira wanda ko gutsuttsurata akayi ƙila wani bazai samu ba anyi cilli da ita an hau bugunta ta ko'ina suna haki kamar waɗanda aka sanyasu dole.

Itakuwa baiwar Allah Jiddoh sai ihu takeyi tana roƙonsu su bar dukanta zata mutu amma babu wanda yaji tausayinta ya ƙyaleta ita kuwa goggo tashi tayi tabar gurin saboda tanayin mgn kanta zaa dawo ace tayi rashin kunya.

Basu bar jibgar Jiddoh ba saida sukaga ta daina numfashi sannan kowa ya koma gefe yayi duru duru suna kallon kallo wannan yana faɗin kaine ka daketa a makasa wannsn yana faɗin aa kaine, baffane ya ƙuta yace "yo ba gwara a kashetan ba a huta da wannan abin kunyar da ta janyo mamu, wai ni Arɗo Jibo nine Kaɗo ya iya tarar cikin idona yace yanason irin mutum daga gareni wannan wanne irin tozarci ne Jiddoh tajamin a duniya"...............

Kuka sosai Baffa yakeyi yana kwaso kwashewar albarkar duniya yana jibgawa Jiddoh dake kwance a qasa magashiyan rai a hannun Allah.

Goggo dake bayan danga tana hangen halin da ƴqr tata take ciki ta share hawaye ta koma ta zauna tana tunanin ko meye yasa baffa yake tsangwamar ɗiyar tata tilo wadda duk cikin ƴaƴansa babu meyi masa biyayya kamarta.

Allah ya sani har ranta itama bataji zata iya bawa kaɗo auren ɗaya ɗayar ɗiyar tata ba amma wannan dukan yayi yawa dole ne tasan abinyi saboda ta lura rayuwar Jiddoh ake nema a rugar tasu, da wanne zataji da auren dolen da ake shirin yi mata da ɗan shaye shaye ko kuwa da mangarin da akeyi mata ko kuwa da mugayen alkaba'ain da akeyi mata?

Bata koma cikin gdanba saida kowa ya fashe sannan ta shiga ta tarar da jummai akan Jiddoh tanayi mata surkullensu na fulani tana shafa mata ruwa a fuskarta.

Miƙa tayi tare da jan zuciya suka miƙar da ita zaune ta zauna tana bude idonta daya kumbura saboda bugu tana kallonsu gwaggo da Inna Jumme tana matsar kwallah ta buɗe bakinta daqyar tace.

"Meye nayiwa Su Moddibo da Arɗo suke buguna wlh bansan komai da nayi musu ba wayyoh bayana Gwaggo wayyoh ƙuguna zani mutu wayyoh kaico...." tana mgnr ne cikin zubar hawaye kamata sukayi suka shiga da ita bukkarsu Inna Jumme ta ɗora sanwar ruwan zafi ta dawo ta zauna kusa da ita tace.

"Kema Jiddoh bakyaji kinsani cewa a wannan rugar tamu bamu bawa kaɗo aure meye yakaiki soyayya da kaɗo kaɗon ma maƙiyi irin jinin sarkin noma Mudansir na alƙalawa kinsan har abada babu jituwa tsakaninmu da irin sarkin noma nikam saidai hande jiddoh wai har kika turoshi shikuma ya ɗauko tsayi kamar daren mutuwa yazo wai yana neman izinin aurenki"

Kallonsu takeyi da rashin fahimta tace "ni bani bace ɓatan burtali yayi ya shigo jejinmu amma ni ban saneshi ba aradun Allah..."

Buge mata baki tayi tace "kusun uwarki ya kawoshi bakece kika faɗi mashi sunanki Hauwa ba yar gidar Arɗo jibo ko kuwa ƙarya yayi miki to nidai shawari zan baki in kinƙi kisha wahala garama ki nemai inda kuke haɗuwa ki hwaɗi masa yabi tsawanyarsa daban kibi taki saboda mudai ko mazan rugarmu sun qare bamu daukan subarjo kamarki mu bawa kaɗo kaɗon ma jinin Sarkin noma"

Miƙewa Inna jumme tayi taje ta juye ruwan zafin ta surka tazo ta kamata ta kaita makewayi ta rinƙa gasa mata jiki ita kuma tana kuka tana ciccijewa tana rufe ƙirjinta a cewarta da tsirarar nono gara ta gindi.🙈

__________Shigar dare Lameer yayi cikin garin saboda yana tafiya yana hutawa kasantuwar irin suyar da zuciyarsa takeyi masa tunda yake a rayuwarsa bai taba ganin wulaƙanci irin wanda yau ya fuskanta a rugar sambajo ba.

Ikon Allah ne kawai ya kawoshi gdan yana shiga baibi takan komai ba ya haye samansa ya cire kayansa ya faɗa bathroom ya sakarwa kansa ruwan sanyi duk da sanyin damunar da yake garin badon komai ba saidon ya samu sauqin abinda yake masa tuƙuƙi a ƙalbinsa amma ina kamar turi ma haka yaji.

Fitowa yayi ya zauna a saman resting chair din ya dafe kansa yana furzar da iska me zafi cikin ƙunar zuciya, zabura yayi ya miƙe ya fara safa da marwa yana tunanin mataki na gaba maganganun Arɗo Jibo suna dawo masa inda yake cewa "kai kaɗo dubeni nan ni ba ɗan iska bane mu ba asararru bane ba rakiya mukayowa bayin Allah duniya ba idanma kana tunanin haɗa zuri'a dani to ka daina aradun Allah dana baka auren ɗiyata Jiddoh ƙwamma ni tsireta na cinye namanta"

wannan Kalami sun daki zuciyar Lameer fiye da dukan dorina sosai suke zaga masa a kwanyarsa kuma suka sashi cikin tunani da son sanin meye dalilin da yasa Arɗo Jibo yayi wannan furucin tare da ƙara ɗaura ɗambar neman auren Jiddoh.

"Kuma munyiwa Jiddoh miji dama mun daɗe da samun lbrn kaine kake hure mata kunne har kanayi mata juyen nono kana janta ku shiga duhun dawa kasata ta fito innininta ta baka kasha..." "meye innini ya tambayi kansa tare da miƙewa ya buɗe ƙofar ya shiga kitchen ɗin dake saman ya dafa tea ya dawo parlourn nasa ya zauna ya tusa kofin a gaba ya kasa shan ko kurɓa daya saboda Hauwah kawai yake gani a idonsa dukan kansa yayi tare da tambayar kansa wai yaushe ya shiga wannan cakwakiyar rayuwar ne wacce ƙaddara ta kaishi Alƙalawa har ya ƙarasa Rugar Sambajo ya haɗu da Jiddoh ya fara yimata wannan son na mutuwa da rayuwa................

__________📝Wannan rana bacci ya gagari Lameer kwana yayi yana tufka da warwara zuciyarsa tana guri biyu kaso tamanin yanaga Hauwah kaso ashirin yana gurin Mubaraka.

Wayewar garin kamar danshi akayita ya shirya tun shidda na safe ya zauna yana kallon tagar da take nuna mishi lkc yana sauke numfashi lkc zuwa lkc yanakai idonsa ga agogo har bakwai ta cika ya miqe ya dauki key din motarsa ya dauki wayoyinsa ya sauko qasan.

A tsakiyar parlourn sukayi clear da matar gdan ta fito daga kitchen dauke da cup a hannunta ta tsaya turus tana kallonsa cike da tsoro a hankali tace “Lameer yaushe ka dawo?"

Shafa sumarsa yayi yace “na shigo naji dakinki a kulle da alamun kinyi bacci shiyasa ban tasheki ba ya kike ya baby Fadwah" iska ta furzar cike da godewa Allah don tasan shima ya fada ne saboda ya kare kansa amma baije ba dakinta a bude ya kwana suna sha'aninsu ita da Muneef amma a fili sai tace.

"Ayyah sannu ya hanya"

Yana tafe yake bata amsa har yakai bakin qofar ta tabe baki qasan maqoshi tace “a tafe kamar namijin qwarai tsautsayi auren me dandaqaqqen azzakari"

Tunaninta baiji me tace ba shikuma yajita sarai saboda Allah yayi masa baiwar jin sauti kamar maciji a zuci kawai zakayi magana ya kasa jinka, ajiyar zuciya yayi ya fita ya shiga motarsa zuciyarsa babu dadi yanaso Allah ya nuna masa ranar da zaiyiwa Mubaraka cin kaca wanda zata daina caba mishi mgn har irin haka amma ya kasa samun wannan damar.

Office dinsa ya fara zuwa ya zauna zuciyarsa cunkushe da tunani damuwar daya kwana da ita ta danne damuwar da Mubaraka take tunanin ta cusa masa, ya kasa hassala komai a gurin aikin sai juya biro da kallon takarda kawai da yakeyi.

Miqewa yayi kamar Wanda aka tsikara ya fara hada takardunsa yana zubawa a jaka wadanda zai bari kuma ya mayar dasu loccar ya dauki kayansa ya fice.
Chapter 4 · 0% Book details