← Book details Matar Hariji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 25

Sashe 23

Matar Hariji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rufe masa baki tayi da sauri da nata yayi saurin tallafo kanta ita kuma tana qoqarin kwacewa Hajiya ta juyo saida gabanta ya fadi ganin yanda yake wani lumshe ido tayi saurin dauke kanta daga kansu ta fice da baya da baya.

Da sauri Hauwah ta tureshi ya kamota yana wani sauke numfashi yace “kinsan Allah kisan yanda zakiyi dani nazama fitinanne nima kullum sai nayi wanka a Texas saboda tunaninki" qwalqwal tayi zatayi masa kuka tace “sai kayi duk yanda zakayi dani kama kasheni ka huta ai dama nasan basona kakeyi ba..."

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Rufe mata baki yayi cikin dariyarsa yace “haba yarinya nikam ai kowa ma ya shaida Ina qaunarki tun kina qwailarki lkcn da kike tsoron bindira" duka ta fara kai masa ya kauce yana dariya yace “lkcn da akeyi miki adumbuli a bayan...." Toshe kunnenta tayi tace.

“Naji naji nace kaje kawai basai kayimin barbada ba" dariya yake sosai ya lakace Mata hanci yace “saida safe amarya ta ki kulamin da kanki kinji" daga masa kai tayi ya shafa kan babynsu yace “wannan shine raba gardama nasan yanzu idan kikaje garinku zasu qara yarda da cewa kowacce qwarya da abokin burminta wlh koda ban matsa nayi amfani da qarfin hukuma an bani keba idan lkcn zuwan Noor duniya yayi sai mun hadu kuma sai yazo kota wanne hali qila da sai anyi asarar rayuka ma akanshi shi daya tak sai a rasa rai sama da goma"

Juyawa yayi ya fice tabisa da kallo cikin sanyi jiki tare da zubawa yaron ido ita ba komai yake bata mamaki ba girman yaron amma wai ita ta haifesa a cikinta ya rayu harna watanni tara yanzu gashi yana rayuwa a duniyar da take rayuwa to wai ma ta Ina cikin ya shiga, a Ina yake zama a cikin nata?

Matsa cikinta ta farayi itadai bataji wani guri da yayi alamar wannan qaton yaron ya zauna ba, kuka ya fara ta murguda baki tace “yaro inma zakayi shiru gara kayi nagaji sai tsotse nono kakeyi bandama rainin hankali na ubanka Hajiya tace a baka madara yace aa saboda ba jikinsa kake jaba to Nima bazan bayar ba aiba dankai akayimin nonon ba lol Hauwah ananan da hali.

Komawa tayi tayi kwanciyarta ta juyawa yaron baya yanata kuka yana neman abinci, Hajiyace taji kukan yayi yawa ta shigo da sauri taga yanda yaron yake neman abinci ta matsa ta daukeshi tace “ni narasa wacce irin yarinya ce ke Hauwah waike yaushe gidadanci zai barki ne yaro sai kuka yakeyi yana neman abinci amma kinajinsa"

Turo baki tayi tace “toni Hajiya zafi nakeji wlh idan yanasha kamar lkcn da babansa ya farasha harma yafi haka zafi shifa jaririn nan har cizona yakeyi shikuwa Dadynsu baya cizona"

Wani takaici Hajiya ta hadiya tace “to yanzu akira miki mijin naki ki bashi kenan ko?" Sai yanzu ta fahimci wautarta tace “am imm nifa ba haka nake nufi ba Hajiya kawai dai kice ya daina cizona dan yaseen ya qara cizona saina mareshi"

Abin dariya yabawa Hajiya yau tana ganin ikon Allah daqyar ma aka samu ta yarda tabawa babyn nono wai ita kunya takeji yana namiji bazai gane Mata nononta ba saida taga ran Alh ya baci sannan ta karba ta bashi tana kuka wai an cuceta tasan sai babe yayi mata fada🤔

Itako Hajiya dama ta zama kakarta kowanne shirme ita ake dorawa, cikin kwanaki hudun da suka rage mata tayi kyau sosai binjintar da Lameer yakeyi abin har mamaki yake bawa kowa hatta ankon suna shine yayiwa kowa hadda yan uwanta da yaje ya fada musu haihuwar sukace zasuzo suna.

Bai fada Mata ba saboda sanin haukanta hana kowa sakat zatayi musamman yanzu da take a fusace saboda ance saita rinqa bawa danta nono har cewa tayi ai an tsaneta ne don anga bata da kowa.

Ana gobe suna da kansa ya tura da mota cikin saa kuwa Baffa bayanan ya maqarfi yakai shanu kasuwa kuma yanayin sati bai dawo ba aikuwa su Inna Jumme su lantana da babbar yayar Hauwah ladiyo da qawarta Lahira suka dungumo suna birni.

Wayyohh murna gurin Hauwah taga na gda tama manta da rakinta da takewa mutanen gidan da ance tazo parlour tayi baqi yan barka sai tace ai dinki akayi Mata tana miqewa farkewa zaiyi,

Tuni ta take ta rugo a guje ta rungume Inna Jumme tanata dariya sai kuma kuka tana dube dube ganin bata hango kowa ba tace “Inna Ina Goggo da Baffa"

Shafa fuskarta Inna tayi tace “yaushe Ina aka tabayin haka autar wuro goggonki bata zuwa sunan danki ai Baffa kuwa baya gari yana Maqarfi" gefe tayi ta riqe qugu ta zube a qasa ta kama kuka rarrashin duniya taqi yin shiru saida aka Kira Lameer yana yan awaki ya tafi siyan abin hakika aka fada masa sarqa me rikicin gangan ta rikice fah.

Babu shiri ya basu kudin ragunan daya siya aka sanya masa a mota suka tafi Salees yanata yimasa tsiya yayi murmushi yace “bakasan yanda nakeji bane nasan tabata akayi kuma bari muje kaji yanzu idan bani dinba ko waye zaizo bazatayi shiru ba yini zatayi tana kuka"

Dariya sosai Salees yayi yace “wannan raino naka bansan yaushe zai qare ba kayi rainon yaya kayi rainon uwar yaya" shidai bai qara cewa komai ba har suka isa gdan ya qyale Salees da sauke ragunan ya shige ciki ya hangota can qarshen dakin ta hade kai da gwiwa tanata kukanta.

Matsawa yayi ya riqota tanajinsa ta sake rushewa da kuka tace “ni ka daina tabani nama daina sonka na daina kulaka kullum kai babu ruwanka da damuwata to wlh babu ruwana da danka nima Gwaggona da Baffana nakeson gani shine kace kada a tahomin dasu ko?"

Ta fada tare da kafesa da jajayen idanunta fuskarta harta tasa abinka da farar fata yayi murmushi kawai ya sanya hanunsa ya dagata cak ya nufi dakinta da ita tana zamewa tana cewa ka sakeni banaso ni banaso kowama ya tafi banason ganinsa Gwaggona nakeson gani"

Bai direta ba saida yakaita har dakin ya sauketa a gadon ta miqe zata fice yayi saurin cafkota ya kulle qofar ya mayar da ita ya kwantar ya kwanta a jikinta yayi qasa da muryarsa yace “ke bansan yaushe zakiyi hankali ba kema fa uwace yanzu haka Zaki rinqa yimin idan natafi dake American?"

Ajiyar zuciya tayi tace “ni bazani ba Gwaggona kawai nakeson gani" kwantar da kansa yayi a kafadarta yace “yanzu kuma shine saikin tashi hankalin kowa a gidannan kina gani su Inna ko ruwa sun kasa shs daga zuwansu kin fara nuna musu halinki wato kinaso suje suce har yanzu bakiyi wayo ba a birnin ko?"

Shiru tayi batace masa komai ba yayi murmushi yace “banason shirmenki wannan ni dakene zan kaiki kije kiyi sati a gurin Gwaggonki kafin mu tafi amma sai kinyi hankali idan bakiyi hankali ba bazakije ba"

Saurin qaqalo dariya tayi tace “namayi daga yau bazan qara ba" kissing dinta yayi yace “yawwa kin bawa Noor abincinsa kuwa?" Qasa tayi da kanta yayi murmushi yace “baki basa ba ko?" Daga Kai tayi yayi murmushi ya fita ya karbo yaron ya miqa mata ya saita mata kansa ta kalleshi ta kalli yaron tace “kamarku daya dashi"

Murmushi yayi yace “ba abinda na tambayeki ba kenan ki bawa dana nono nagani" noqe kafada tayi tace “kaje zan bashi ni basai ka...." Wani kallo da yake mata yasata hadiye mgnr ya sanya hannunsa ya zuge zip din rigar ya sanyawa yaron nono ya kama da sauri.

Qara tayi saboda zafin da taji, yayi murmushi yace “kokefa amma danki na cikinki ki rinqa yimasa horon yunwa" hawaye takeyi tace “ni kaje banason surutu" miqewa yayi yace “babu komai na gode" ficewa yayi yaci gaba da harkokinsa bai samu zama ba sai da gama da baqinsa sannan ya wucce gdansu yayi wanka ya kwanta.

Wayarta ya kira tana gani taqi dagawa yayi dariya itafa a dole laifi yayi mata yasata ta bawa danta nono, yananan kwance yanata tunanin wautarta da rikicinta yanata dariya har bacci ya daukeshi.

Tun asuba daya fita bai dawo gdanba gidansu ya tafi ya shiga gurin mahaifinsa suka gaisa yayi masa addu'ar Allah ya raya musu Muhammad Nuraddeen sai lkcn su Inna sukaji ashe Ardo akayiwa takwara sukayita murna kuwa basu taba zataba.

Shagalin suna sosai akayi ranar su Inna sunga ikon Allah yanda aka rinqa girmamasu a gidan abin ya tsaya musu a rai musamman Hajiya data rasa inda zata ajiyesu komai nasu na dabanne me jego ta shiga ta fita an kece raini anyi hotuna na uban ubansu.

Washegarin suna su Inna sukace sufa tafiya zasuyi sosai Lameer da Hajiya sukaso su bari su qara kwana biyu amma sukaqi hakanan suka hada musu goma ta arziqi Hauwah na kuka suka tafi suka barta kan cewa sai tazo kawo musu Baffa.

Sake bada mota yayi da kudi me yawa da kayan sawa atamfofi da lasina yace akaisu har gda, aikuwa yasha ruwan albarka suna tafiya a gaban Hajiya ya sunkuceta yana juyawa da ita itakam Hajiya ta gaji da ganin rashin kunyar Lameer saboda haka ta nufi cikin gda ta barsa da ita tasan indai Hauwah ce ba qarewa zasuyi qlau ba balle yanzu da take ganin yan uwanta sun tafi sun barta...............

Direta yayi ya Kama hannunta suka shiga ciki ya zaunar da ita a kujera yace “meye na damuwar nan da yan kwanaki kema zakije kiyi sati guda"murmushi tayi ta saki ranta suka fara hirarsu kafin ya tashi ya fice.

Haka kwanaki sukayita tafiya Noor yanata girmansa gwanin sha'awa kyakkyawa dashi son kowa Lameer yana bata kulawa sosai lkcn da tayi arba'in kamar zai saceta haka yakeji saboda qauna a ranar yazo wai yazo ya dauketa ita kuma Hajiya ta kafe akan bazai dauketa ba sai sunje Rugar Sambajo sun dawo, dolece kawai tasa ya hqr saboda bayason tsayawa yana jayayya da Hajiyan amma a matse yake da iyalinsa.
Chapter 23 · 0% Book details