← Book details Matar Hariji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 25

Sashe 12

Matar Hariji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turo baki tayi tace “chabdi nidai aa bazan iya girki ba ni ko kunu ban taba damawa ba balle wannan jagwalgwalon naku na yan birni" murmushi yayi ya dauko tukunya sabuwa dal a cikin kitchen cabinet ya zuba ruwa ya dora ya goge hannunsa ya jata suka fito yace.

“Zauna Ina zuwa" baijira cewarta ba ya nufi downstairs din ya sauka ya nufi matattakalar da zata kaishi part din Mubaraka ya haura ya tarar da ita a tsaye da waya a hannunta tana yafa mayafi yace “ina Zaki?" Cikin kallo irin na tsantsar tuhuma tace.

“Zanje na tambayi tsohuwarka ne da saninta ka kawomin wannan kucakar karuwar taka gidana har kayi Mata bangare a cikinsa ka shige daki da ita sama da awa guda" Murmushinsa ya fadada yace

“Abinne yazo a bazata wlh shiyasa ban sanar dake ba kiyi hqr nasan nayi miki laifi duk da qila kinsamu lbrn dama Ina neman aure, Mmn Fadwah wannan yarinyar da kike gani matatace ta sunnah da aure yabani matsayinku daya a gurina babu wacce tafi wata sai wacce tafi kwantarmin da hankali"

Numfashi yaja yaci gaba da cewa “Mubaraka Hauwah yarinya ce qarama qanwar bayanki ta qarshe gaba daya bazata wucce saar Zainab qanwarki ta hudu ba, haka Allah ya nufa kuma ya qaddara batasan komai ba dani dake mune zamu sanar da ita idan mukayi Mata mugun karatu dashi zata tashi idan muka bata sahihin karatu da babu mugunta ko sonkai a cikinsa to shine zaita zagawa tsakaninmu alkhairi zai wanzu cikin zamantakewarmu ya bamu kyakkyawar alaqa da fahimtar juna wanda hakan zaiyi tasirin bibiyarmu har qarshen rayuwarmu....."

Daga masa hannu tayi tace “kayyy dakata munafukin Allah ta'ala kana nufin wadannan matsiyatan kalaman naka sune zasuyi tasiri a kaina? Hmmm wai qanwa wlh kayi tsararo Allah ya kiyasheni tabewa yin qanwa da wannan bagidajiyar yarinyar kaidai daka kwaso ta kware maka can Amma badani ba"

Yanda take mgnr tana nufoshi kamar zata dakeshi yasashi sakin baki yana kallon ikon Allah har ta iso gabanshi tace “wannan itace sakayyar halaccin da nayi maka ko Lameer kaje ka ajiye karuwa a Lagos sannan ka tashi dawowa ka dawomin da kishiya kishiyar ma wannan qazamar kucakar yarinyar da bazata taba wayewa ba a rayuwarta, to wlh saidai ka zaba koni ko ita nikam bazan taba zama da ita a matsayin kishiya ba Wai muna amsa suna daya gurin mijinmu.

Ka cuceni a abubuwa da yawa Lameer baka damu da saukemin haqqina ba wata da watanni kana qwarata kana barina da damuwar da banida me yimin maganinta saikai sannan yanzu ace kayi aure wannan ma ai cin fuskane da wulaqanci da wanne kuzarin zaka riqemu mu biyu har ka biyawa kowa buqatarta?"

Shafa sumarsa yayi yace “duk wannan ba damuwarki bace abinda ya shafeki kuma haqqi a gareki shine na sanar dake matsayin Hauwah a gurina kuma na sanar dake ruwa nane na kusanceta kullum ruwa nane na shekara ban kusanceta ba kamar yanda nakeyi miki wannan ba matsalarka bace, amma dai ki sani kuma kisa a ranki aurena da Hauwah yin Allah ne kuma ya qullu babu wanda ya Isa ya hanashi kamar yanda mahaifinta da danginta suka qi kuma suka qyale akayishi yaka duk wani dan baqin ciki zaiyi quncinsa ya qyalemu, idan kuma mutum yana ganin bazai iya hqra ba to ya hadiyi zuciya ya mutu kowa ya huta"

Wani mugun tashin hankali ta tsinci kanta a ciki da bata taba tunanin Lameer zai sata a ciki ba tunda sukayi aure tsayin shekara uku baitaba daga muryarsa sama da tata ba sai akan wata mace macen ma wannan qazamar kucakar bafulatanar dako yar cikinsa inda yayi auren wuri batakai ba, lallai da aiki ja a gabanta dole ta tashi hankalinsa dana zuri'arsa, babban tashin hankalinta yanzu cikin da take dauke dashi na watanni biyu wanda a lissafe idan zaiyi lissafi watansu hudu rabon da wani harka ta auratayya ta shiga tsakaninsu sai kwanaki takwas daya wucce ranar da tayi masa tujarar nan, yanzu ta yaya zata fara liqa masa cikin kamar yanda ta liqa masa na Fadwah?..…………...

Karanta Littafin>>> Abban Sojoji Page 1-10 Hausa Novel

Miqewa yayi yace “kewai komai ma baki iya ba bakiga toilet a bathroom ba dazu da kikayi wanka zakicemin wani kashi kikeji" sakeyin raurau da ido tayi tace “ni wlh banga juji ba" ya lura itafa komai bata ganewa sai anyi mata gwari gwari hakan yasa ya kama hannunta suka shiga bandakin ya bude seet toilet din yace “ga gurinda akeyin kashi nan idan kika gama sai ki murda wannan ki zaro tissues ki goge saiki sake danna nan ruwa zai zubo saikisa sabulu ki wanke idan kin gama kuma ki danna nan zakiga ruwa yazo yayi flurshing"

Fita yayi yabarta a tsaye tana leqen cikin toilet din tana kallon ruwan ciki gare gare tace “to aini dazu a wannan randar na debi ruwan alwala"🤣

Har yaja qofar yace “ehh!" Tare da zaro ido yace “kika debi ruwan alwala anan?" Daga masa kai tayi tace “eh aradun Allah kuma ruwan dumine dashi danasashi a bakina har wani zaqi yakeyi" ai baisan sanda yayi qasa ba yace “kinsha fitsarina Hauwah kewai wacce irin shashashar yarinya ce bakiga inda nayi tawa alwalar ba" turo baki tayi tace “toni Ina ruwana bakaine kace nazo nayi alwala ba"

Takaici ne yasashi miqewa ya fice daga toilet din ita kuma tahau kan masan, memakon ta zauna aa saita tsuguna akai qafafunta nakan gurin zaman idan tayi kashin ya fada tsulum saita qyalqyale da dariya tace “danwake daya ya fada" haka harta gama tayi duk yanda yace.

Ta wanke hannunta ta fito baya cikin dakin hakan ya bata damar yin sallar magrib da Isha ta kwanta a qasan.

Ya turo qofar ya shigo ya hangeta a qasa ya matsa da sauri ya dagota yace “kekam baki gudun mgn kin mayi wanka kuwa?"

Kada masa Kai tayi ya dagata yace “ok muje kiyi wankan mu kwanta gobe litinin jirgin asuba zamu bi mu wucce Lagos" itadai batace masa komai ba ya dagota suka shiga bathroom din to yanzun ma a bataso tana zillewa shine yayi mata wanka ya fito da ita shima yayi suka kwanta bayqn yayi musu addu'a.

Kiran sallar farko akan kunnensa ya tashi yayi wanka ya tasheta ya fito Mata da wata doguwar rigar atamfa cikin kayan da ya bayar tunkan yatafi a dinka mata yasata ta sanya ya bata mayafi da takalmi da jaka ya koma yana kallonta tayi masifar kyau kamar ba itaba.

Murmushi yayi yace “dama kada kiyi shirmenki ki nuna kanki idan mun tafi banason qauyancinki ki ajiyeshi anan idan mun dawo kya dauka ki saka kinajina ko? Daga masa kai tayi ya fita ya hado musu tea ya bata tasha daqyar kasancewar asubace biyar ma bata qarasaba ya kama hannunta su fito zuwa qasan.

Ya saki hannunta yace “ki jirani anan bari nayiwa yar uwarki sallama" batace qala ba ta nemi guri ta zauna shikuma ya haura saman ya kwankwasa dakin Mubaraka, ta miqe zumbur shima farkan nata ya miqe tace “mun shiga uku gashinan wlh shine bugun qofarsa ne"

Cikin kadawar ciki Muneef yace “yanzu ya zamuyi" kafin tabashi amsa ya tashi ya shige bayan manyan labulen ta qasa ya kwanta luf, ta sauke ajiyar zuciya ta bude masa qofar tana miqa ya shigo dakin yana rarraba ido yace “na tasheki ko? Zamu wucce Lagos shiyasa nayi miki transfer kudi a account dinki nasan zasu isheki duk da ba dadewa zamuyi ba"

Kallonsa takeyi sake da baki kafin tayi mgn ya juya yace “Ina Fadwah ne ko tana gdan Hajiya" nan ma bata bashi amsa ba ya sauka yace da Jiddoh taso mu tafi kinga har rana ta fara fitowa"

Suna fita drivensa yaja suka tafi yakaisu airport to dayake yayi mata federal warning yadan samu sauqin shirmenta kuma dadin dadawa taga babu fuska hakanan duk da tsoron da take ciki na hawa jirgin ta haqura saidai qanqameshi da tayi jirgin ya tashi ita kuma ta kama bacci a jikinsa.

Lkcn da suka isa Lagos din tanata sharar baccinta ya sabata a kafadarsa har mota yasata a ciki suka nufi Quarters din tasu saida driven ya shiga har ciki sannan ya tsaya a daidai qofar bangarensa ya bude ya fito itama ta tashi yace ta fito ta fito suka shiga ciki.

Wayyohhhh Allah nan Hauwah taga qarshen haduwa bawai fin sauran gidajen da tashiga kayan qawa yayi ba aa saidai kawai yafisu tsaruwa ga wasu manyan hotunansa guda biyu da yayiwa parlourn ado dasu sai nata Suma guda biyu daya dauketa wata rana a bakin qoramar da suke zama suna fira farkon haduwarsu.

An wanke hoton ya fito sosai kamar a kirata ta amsa, kallonsa tayi shima ita yake kallo yayi murmushi yace “kina mamaki ne?" Daga masa kai tayi ya fadada fara'arsa ya matso gabanta ya dago fuskarta ya sauke Mata lebbansa biyu yace “to ki daina yanzu wasan zai fara, yanzu zamu fara sabuwar rayuwa dagani saike, ki dauka bakida kowa sanin nima zan dauka banida kowa sai ke kadai"

__________

Qasa tayi da kanta cike da kunya ya sanya hannunsa ya dagata cak ya bude wani daki ya shiga da ita ya kwantar da ita yace “ki kwanta bari naje na nemo mana abinda zamuci" juyawa yayi ya fita bai jima ba ya dawo.

Ledoji ne a hannunsa ya ajiye ya matsa ya dagota yace “tashi kici abinci sai kiyi baccin" tashi tayi ta sauko ya bude farfesun bindin saniya da kunun gyada sai wani hadadden cake, da kansa ya rinqa ciyar da ita Saida ya tabbatar ta qoshi sannan ya tashi ya fice.

Office dinsa ya wucce bai shigo gidan ba sai biyar na yamma abincin rana na aikowa yayi aka kawo mata, yanda ya tafi ya barta haka ya dawo ya tarar da ita tana zaune a falon ya zuba mata ido yana kada kai a ransa yace “ita komai bata iyaba"

Matsawa yayi ya kamo hannunta ta miqe firgigit tace “sannu da dawowa" murmushi yayi yace “yawwa amma bakiyi wanka ba meye yasa?" Shiru tayi saida ya qara cewa magana nakeyi miki ko babu halin amsawa?" Kada kanta tayi tace “ai baka nunamin bayin ba ni kuma bansan inda yakeba"
Chapter 12 · 0% Book details