← Book details Matar Hariji Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 25

Sashe 22

Matar Hariji Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma muka hanaka mukace saidai ka zauna dasu a haka to yaudai qarshen tukatukin tik mun gane abinda ka dade kanaji a ranka cin amanarka da qaninka uwa daya uba daya, cin amanarka da abokin qaninka, cin amanarka da mazan kwararo, abubuwan sun munana sun qazanta har takai anyi ciki da qaninka an liqa maka wanda Allah ya sani tun ranar dana fara ganin yaron nan Muftahu har kawo yanzu da binciken likitoci ya tabbatar da Fadwah itace jininka Muftahu ba naka bane na Muneef ne idan na kalleshi gabana faduwa yakeyi saboda tsananin kamarsu ta munana.

Download>>> Budurwar Mijina Complete Document

Abisa wannan dalilin yasa na yanke shawarar baku Fadwah ku riqe a hannunku shikuma wannan zai zauna a hannunmu alhmdllh naji dadin datse igiyoyin aurenka akanta.

Bullet ya shige ta gabanta a lkcn da aka harbi abokin barnar Tata qafa zaayi Mata aiki cikin satinnan idan taji sauqi ta gama iddarka zan daura musu aure suje su qarata su riqe shegen dansu a tsakaninsu..."

Wata zabura Hajiya tayi tace “aa Alh kadama ka fara iri me kyau akeson yayi yado a cikin zuri'a wannan mummunan irin bana fatan cigaba da wanzuwarsa cikin zuri'ata don Allah ka qyaleta ta koma Jalingo akwai Amina me tallan awara ta gidan Idi dillali wlh gara ka aura masa ita da wannan baqar kadarar Alh kada kace aa yarinyar tafi wannan tarbiyya"

Shidai Alh baice komai ba saima miqewa da yayi yace “Lameer ka rufe taron da addu'a ka dauki iyalinka ku wucce" gdy yayi masa ya rufe musu taron da addu'a sannan suka gaisa itadai Hauwah sai quqqunshe cikinta takeyi a haukanta bataso su gane cikin jikinta amma saiji tayi Hajiya tace.

“Ashe matar taka ma takusa haihuwa?" Shafa kansa yayi yace “eh wlh nan da wata uku insha Allahu banmasan ya abin zai kasance ba idan na gama karbar magani qarshen watannan nakeson wuccewa America na samu aiki a Flight Emirate kuma inason tafiya dasu"

Kallon Hauwah Hajiya tayi cikin kunya tace “idan ta amince sai kabarta anan idan ta haihu lfy sunyi arba'in saikazo ka tafi dasu..." Wani gumine yake karyowa Hauwah ya zuba mata ido tare dayin murmushin yaqe yace “karki damu Hajiya zan kaita gidansu ina ganin zatafi nutsuwa naga kamar ta tsorata daku"

Zulaiha ce ta matso jikin Hauwah tace “don Allah kiyi zamanki damu anan Hajiya tayi nadama kuma zata baki kulawa sosai"

Sakeyin qasa tayi da idonta Zainab ta matso tace “idan bazata zauna anan ba ni kabani kwangilar kula maka da ita...." Wata uwar harara daya zuba Mata tasata tsuke bakinta ya miqe yace “tashi muje duk yanda mukayi da ita zakuji"

Dama kamar akan qaya take ta miqe ta zari Jakarta ta fice murmushin nadama Hajiya tayi dakanta akan wannan makirar yarinyar tasa surukarta ta arziqi tana gudunta.

Yana driving din yana kallonta ita kuma ta kwantar da kanta a jikin sit har sukaje wani shopping Mall suka shiga ya rinqa lodar masu kayan baby har saida ta riqe hannunsa tace “don Allah ya isa haka babe komai munadashi fa ni wani abinma bansan amfaninsa ba" zame hannunta yayi yaci gabada abinda yakeyi Saida ya gama suka fita suka nufi gda.

Daqyar ya samu ya shawo kanta ta koma gurin Hajiya lkcn da zai tafi America shima saida yace Mata ai Muneef bayanan yana England ana kula da qafarsa data fara rubewa saboda Harbin da akayi masa.

Haka watannin suka yita turawa kulawa ta musamman Hajiya ke bawa surukarta Alh ma komai ya gani uwarsa wannan dalilin yasa ta saki jikinta tana boffidonta a hannun surukanta,

Ranar wata Laraba suna parlour Hajiya nayi Mata tsifar dogon gashinta tanata yimata surutu sunata dariya Hajiyan taji ta dauke wuta, shiru na dan lkc can kuma taga ta muskuta zata miqe Hajiya tayi saurin riqeta tace “menene Hauwah?" Qanqame qafar Hajiya tayi cikin fitar hayyaci tace “ci...cikina Hajiya wayyohh bayan...."

Kamata tayi suka shiga daki ta sake durqushewa jikinta yana karkarwa tana kuka kafin Hajiya ta nemo Mata hijjab me afkuwa ta afku yaron ya sawo kai tayi kanta da sauri kafinma tazo ya fado gabadaya Hajiya tasa hannu ta dauko yaron ta yanke masa cibiya.

A towel ta nadeshi ta dawo ta fara gyara Hauwah kafin wani lkc ta gama gyarasu tsaf sunkucecen yaron me masifar kama da ubansa yanata wawurar hannunsa da alamun abinci yake nema.

Kiran Alh tayi ta fada masa abinda yake faruwa ya turo musu likita tazo ta dubata tayi Mata dinki saboda qaruwar da tayi ta bata magunguna sannan Hajiya ta hada Mata shayi ta fara bata tanasha a hankali tana kallon yaron hawaye na zuba a idonta so qauna da tausayin iyayenta na qara narkar da zuciyarta.

Download>>> Macijine Complete Document

Nadamar watsin da tayi da iyayenta tana nuqurqusar zuciyarta ashe irin wahalar da Goggonta Tasha kenan ta kawota duniya amma ta zabi mijinta akanta wani kuka ya qwace mata ta kwantar da kanta a kafadar Hajiya daidai lkcn da Lameer ya kira wayarta.

Hajiya ce ta dauko ta daga ta miqa Mata ta miqe ta fice, ajiyar zuciya yayi yace “Yau Ina cikin farin cikin da bantabajin irinsa ba Hauwah nasan baby na baiyi kama dakeba dani yake kama saboda nasha wahala a daren da zan bakishi alhmdllh alhmdllh alhmdllh Hauwah don Allah ki shafamin kansa kiyimin kissing lips dinsa kafin nazo insha Allahu jibi zan taho" shassheqar kukanta yasashi yin shiru da kalamansa yace “meye kikeyiwa kuka?" Cikin shassheqa tace “yau... Yaushe zaka kaini gurin Goggona?" Dariya yayi sosai yace “sai yanzu kika tuna da ita da kikaji abinda akeji ko?".............

Zuciya ta aje tace “nidai ka kaini nagansu na roqi gafararsu wlh indai haka haihuwa take abban Fadwah bazan qaraba bazan sake haihuwa ba ni wannan ya isheni don Allah kada kacemin na qara haihuwa kaji?"

Numfashi ya sauke yace “kin tsorata da yawa babe ki kwantar da hankalinki ke bakisha wahala bama a sadaka kika samu haihuwarki" saurin katseshi tayi da cewa “au ahakan?" Dariya ta bashi sosai yace “eh mana insha Allahu Ina dawowa zan baki wani babyn kiyi maza ke haifamin dozen guda kinji" qit ta kashe wayarta saboda kalamansa kawai bata Mata zuciya suke.

Shigowa Hajiya tayi ita da Alh Alh ya dauki yaron yayi murmushi yace “masha Allahu yaro me kama da babansa Allah ya albarkaceka Muhammad Nurraddeen...." Dagowa tayi da sauri ta kalli Alh yayi murmushi yace “tun kafin Lameer ya tafi yacemin idan kin haihu nayiwa yaron huduba da sunan mahaifinki"

Sunkuyar dakai tayi wasu hawayen farin ciki suka zubo Mata ta zame qasa tana hawaye cikin rawar murya tanayi musu gdy Hajiya ta dagata tace “bamu zakiyiwa gdy ba Hauwah tsakaninki da mijinki ne kunfi kusa kuma sakayyar halacci halacci insha Allahu idan ya dawo har dani zamuje mukaiki ki daidaita da mahaifanki aure dai damu da mukaqi dama wadanda sukaso babu wanda ya iya hanashi saboda Allah ya riga yayisa"

Suna wannan mgnr Aunty Zulaiha da Aunty Zainab suka shigo suka zauna Suma anata hira dasu itadai bata cewa komai saboda ciwon da cikinta yake danyi Mata ciwo basu ankara ba saida sukaji ta fara kakarin amai sukayo kanta duka.

Sabarta Alh yayi yasata a mota Hajiya ta shiga da jaririn sai asibiti suna zuwa sukayi Mata Allurai suka bata wasu magunguna sannan suka juyo gda, sunata zuba mata sannu suna zuwa dama isha tayi aka ciro gadon baby aka sanyashi a ciki aka kwantar dashi itama ta kwanta Hajiya me jika cewa tayi saidai su kwanta a dakinta bazaayi mata nesa da jikanta ba.

Fadwah ita ke kusan yini tanawa yaron wasa wata shaquwa ta shiga tsakaninta da jaririn ba kamar Muftahu ba da basa jituwa ko kadan ita kuwa Mubaraka ta koma dangin mahaifinta Jalingo inda Alh ya shiga ya fita Muneef da Hajiya ma basu sani ba aka qullah shirin aurenta da Muneef din.

Kwanan Hauwah uku da haihuwa Lameer ya diro cike da shauqi bai bari kowa ya ganshi ba ya shige dakin da lallaba ya sanya hannu zai dauke baben data rungume take feeding nashi tayi sauri qanqame abunta tare da bude idonta, murmushi yayi Mata yace “mata sunyi da rigima ta qare ohhhh Hauwah rikicin ki yawa gareshi kuka wiwi ke banasonki naqi baki baby to yaudai ga babenki dana baki a hannunki"

Sunkuyar dakai tayi cike da kunya tana wasa da sumar yaron ta fulanin na gaske wacce ya debo gurin uwarsa amma komansa har fatarsa na ubansa ne hannu yasa ya daukeshi yayi masa addu'a sosai sannan ya rungumeshi a jikinsa yanajin ninkin qaunar yaron da uwarsa na mamayar zuciyarsa.

Kwantar dashi yayi ya zuba masa ido kawai yana kallon buwaya ta ubangiji sumar yaronce kadai ta uwarsa amma hatta farcensa irin nasane a hankali yace “Allah daya"

Kwantawa yayi a jikinta ya sanya hannunsa ya shafo nononta yace “inason taya babyna shan madara sweet abani" turo baki tayi tace “ni ka tashi ka tafi saura kadan na mutu yaseen da nasan haka haihuwa take da babu abinda zaisa nasaka kayimin ciki"

Yanda take mgnr da qumajinta ya bashi nishadi yace “kuma gwarne nakeson kiyi kafin kiyi arba'in na baki wani ko?" Tureshi tayi ya koma gefe yana dariya Hajiya ta shigo yanayin data gansu ya bata kunya sosai har zatayi mgn taji tsoron amsar da lameer zai bata don yafita wauta.

Miqewa yayi ya dauki Fadwah ya fita bai jima ba ya dawo dauke da wani babban akwati ya ajiye Mata a gabanta yace ki bude ki gani abinda baiyi miki ba ki ajiyeshi gobe saina canzo miki yanzu nidai kuyimin guri a dakinnan na kwanta bacci nakeji"

Hajiya dake fitowa daga bathroom tace “badai dakin nan ba kaje gurin maigadi ku kwana tare tunda ka manta hanyar gdanka, sosa qeyarsa yayi yace “aa ba haka bane Hajiya kawai so nakeyi mu kwanta tare Noor dinmu a tsakiya nasan baccin zaiyimin dadi sosai..."

Daquwa tayi masa tare da jifansa da pillon hannunta tace “zaka tashi ka fice mana a daki ko saina Kira Alhajinka yazo ya fitar dakai" miqewa yayi yace “ya zanyi tunda baa qaunata" sunkuyawa yayi daidai fuskar Hauwah yayi kissing nata yace “kin samu daurin gindi lkcnki ne Allah ya kaimu lkcn da Zaki shigo hannuna saina....."
Chapter 22 · 0% Book details