← Book details Marubuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 19

Sashe 9

Marubuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta shirya tsaf Aunty Hauwa, domin har tasa akwatin ta a mota ,sun fito harabar gidan ana bankwana jikin Salma a matukar mace da kasala
"Aunty har wata biyu."?
Abin da take ta fad'a ke nan tun jiya da take tayata shirya kaya
Anas ne ya ce .
"Ni fa Aunty har airport zan kai ki , saina dawo da motar ."
Aunty Hauwa ta ce .
"A'a rufa mini asiri inà ka iya wata mota , acan gun aiki zan barta kayi zaman ka ."
"Ni fa gaskiya Aunty zan raka ki ."
Ta sake fad'in.
"Anas muna da yawa fa ka barshi."
Ya shige gaban motar yana cewa.
"Ni dai sai naje har sai naga tashin ku."
Aunty Hauwa tai dariya da cewa .
"Tom ai shi ke nan."
"Tom ni zan koma ciki, Allah ya tsare Hauwa aje lafiya a dawo lafiya sai mun yi waya ."
Cewar hajjiya Aisha
Ta maida mata da cewa.
"Tom mommy nagode zan yi kewarku."
Kana tana murmushi da d'ago hannu hajjiya Aisha ta koma ciki

Falll hawaye idanun Salma ta kalli Aunty Hauwa.
"Haba Salma kuka zaki kuma , kar ki yi dan Allah."
Ta fara rarrasheta, Salma cikin kukan ta ce ."wallahi Aunty baza ki gane ba amma Allah ya dawo dake lafiya."
Kafin ta bata amsa Saida ta duba agogon hannunta kana ta ce .
"Yawwa Salma sai mun dawo, idan akwai wani abin ki kirani, idan mun je zan kiraki , sannan na tura miki dubu 30 a opay din ki."

Salma ta ce .
"Tom shi ke nan na gode Aunty."
Ta shige motar suka tafi tare da Anas tana musu bye-bye.

Su Hadiza suna tafiya suna hira har suka isa suna zuwa suka shiga ciki , kamar yadda ya bukaci su zauna kan wata tabarmar kaba ,nan suka zauna kana ya saka hularshi ya dauki carbi, sannan kasar dake gabanshi yasa hannu ya share samanta , sannan ya d'ago ya kalli Umma.
"Kwana biyu Mero, shekara da shekaru."
Umman Hadiza tai murmushi da cewa.
"Lafiya lau ai kasan mijina ya mutu, tom sai muka koma Kano."
Ya ce .
"Allah sarki mijinta ce baban Adam ."
Umma ta ce .
"Yawwa akwai abin da ke tafe damu."
Tasa hannu ta dunguri Hadiza alamun tai magana
"Ita ma wannan yarki ce , naga Kun yi gama wajen idanun."
Ya fad'a yana dariya
Umma cikin raha ta ce .
"Ehhhh."
"Tom yanzu me kuke so a yi ."?
Ya tambaya
Hadiza ta ce .
"Akwai wata da nake so a tabbar min tana raye kota mutu . Kuma a wanne hali take ciki."
Ya shafa saman kasar tashi yana cewa.
"Ya sunanta dana babanta , awanne gari take."

"Sunanta Salma Aminu, tana garin Kano karamar hukumar tarauni."

Ya rubuta Salma Aminu kan kasar tare da wani jagwalgwalon rubutu.
Jimm ya yi yana kallon kasar , daga bisani ya d'ago yana cewa.
"Sunanta Salma Aminu Waziri, wacce ake kira da Autar marubuta, kuma yanzu haka tana cikin garin Gombe."
"Cikin daula da wadata."

Da sauri Hadiza ta kalli Umma jin ya bayyana Salma, domin tabbas tuaninta , ya zama gaskiya
"Me kuke so a yi mata yanzu, ko kuna so ta dawo inda kuke ."?

"Ahhhhhh."
Cewar Hadiza
"Kawai dai ina so a hanata sukuni , kuma wannan rubutun ta dena yi , a makantar da ita kuma a kuturtar da ita ."
"Makanta da kuturta ko."?
Ya fad'a
Hadiza ta ce.
"Eh."

Ya shafa kan kasar tashi , sannan ya ce .
"Zaku kawo kofaton jaki guda daya , da kuma idonsa guda daya."

Hadiza ta kalli Umma

Ina cigiyar book dina na DAJIN MUTUWA 😭😭

Autar marubuta
07040805269
WhatsApp only

https://whatsapp.com/channel/0029VasuzYr6rsR0bxO94J1I
*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️

Kaggagen labari ne ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~

Autar marubuta ce
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 21&22

Tunda Salma tai alwalar magariba ta shiga daki ta kulle, duk da cewa tunda Anas ya tafi raka Aunty Hauwa bata sake jin motsinsa ba
Wajen karfe 8 taji ana kwankwasa mata kofa .
"Waye ."?
Suwaiba dake tsaye kofar dakin ta ce .
"Ni ce nan hajjiya ce take kiranki a falo."
Salma ta ce .
"Tom gani nan ."
Ta tashi tasa hijabiinta kana ta fita zuwa falon , tana zaune ta harde a kujera, ganin wannan yanayi yasa Salma ta durkusa a kasa tana cewa.
"Gani hajjiya."
D'ago kai ta yi , sannan ta ce .
"Ki tattare kayanki a wannan daren kibar gidan nan ."
Dasssss
Zuciyar Salma ta bayar
"Mommy ina zani kuma."?
Cikin tashin hankali Salma tai maganar
"Ki tafi duk inda zaki je mana, wannan gidan daga ni sai my son dan kuwa na sashi a kasuwa , gobe da safe muma zamu tashi ."
Jin hakan ya sake sa Salma cikin tashin hankali
"Assalamualaikum."
Anas ya shigo rike da wayoyi guda biyu a hannunsa, guri ya samu ya zauna yana cewa.
"Mommy kin ganni sai yanzu ko, ai yanzu ma sun je, har airport naje ."
Hajjiya Aisha da duk hankalinta ke kan hannun Anas ta ce .
"Ya nake ganin kamar wayar Hauwa kuma."
Salma ta kalli hannunsa
"Eh mommy wayar ta ce wallahi, sam'bad'ota nayi , wannan wayar ta kai dubu dari biyu da hamsin , nasan tun a jirgi zata neme ta, sai sun sauka ta ga babu ita ."

"Innalillahi."
Salma ta fad'a a fili ba tare da tasan sautinta ya fito ba
"Wannan yarinyar me take yi anan ne."?
Anas ya tambayi hajjiya Aisha
"Na ce ta kwaso kayanta tabar gidan nan , shi ne take mini gaddama da futsara."Mommy ta ba shi amsa

Cikin hassala ya mike tsaye tare da fad'in.
"Zaki tashi ko kuwa yar mutumarrr..."
Da sauri Salma ta nufi daki ta fara had'a kaya tana zu ba wa a cikin jaka , tasa laptop da wayarta , hijabi kala biyu kawai tasa sai wasu dogayen riguna guda biyu, sai ga Anas ya shigo , firgita ta yi da gudu ta dauki jakar ta fice , haka ya biyo bayanta har waje .
"Ke garin nan ma zaki bari yau din nan kuwa, muje bakin titi."
Cikin tsoro 🥺 ta bishi , bakin titi yaje ya tsaya tare da ita , ammma babu wata mota da take tsayawa ,ganin ya gaji yasa ya tsayar da irin babbar motar nan wacce take cike da shanu .
"Yaa mai gida dan Allah kara mini wanna yarinyar mana ka sauketa duk inda ka tsaya."
Ya mika masa wasu kudade .
"Ni fa Bauchi na nufa kai tsaye."Cewar mai tuka babbar motar
"Ehh ba matsala ga wannan kasa mai."
Ya karba Salma ta fashe da kuka , haka ta hau gaban wannan mota daga ita sai mai tuki sai shanu ga dare yayi, kana ya tuka motar suka tafi
Kuka Salma ta ringa fasawa a wannan lokacin, sai dai bai ce da ita komai ba kawai taba yake sha abinsa .
Haka suka tafi kwana tafiya, wajejen karfe 5 na asuba wannan mutum ya karasa Jahar Bauchi, sauke ta kawai ya yi yanufi cikin kasuwa.
Cikin tashin hankali Salma tana kuka ta rasa meke mata dadi, ta fara tafiya har ta fara gano gidaje
Wani kofar gida kawai ta samu ta zauna, babu abin da take so illar a halin yanzu ta koma gida, sai dai rashin kudi, samm ta manta da kudin da Aunty Hauwa ta ce ta tura mata .
Kiran sallar asuba aka fara , sai dai sai kuka take Salma domin babu inda ta sani , ana cikin haka sai ga wani saurayi ya fito daga kofar gidn da take zaune, bai ce da ita komai ba , kawai ya wuce masallaci yana tafiya yana waigenta , dawowa ya yi saboda yana tunanin zata shiga gida tai masa sata.
"Ke me kike yi anan ne tashi ki bar mini kofar gida." Ya fad'a cikin masifa
Mikewa tai Salma cikin kuka tana magana tana hardewa .
"Dan Allah ka taimaka mini wallahi nasha bakar wahala, babu wanda na sani anan , daga Gombe nake , tun daga Kano nake haduwa da jarabawa babu yadda zan yi ka taimaka mini."
Ta kai kasa tana kuka, tausayin ta yaji ya rufe ta sosai , hakan yasa ya ce .
"Tom shi ke nan, zan taimaka miki da kyakykyawan zuciya, amma indai kika cutar dani ko matata bazan yafe miki."
Ya nufi ciki Salma ta bishi suna shiga matarshi tana alwala
"Baby lafiya."
Abin da matar tashi ta ce ke nan tana kallon Salma.
"Fatima ga wannan, ki bata daki idan na dawo zan miki bayani ."
Kana yayi sauri ya juya , kamar yadda ya ce , ta bawa Salma daki, ta fito ta yi alwala tana yin sallah bacci ya dauketa a gurin .

Wajen karfe 11 na safe Hadiza tana zaune falon Karima tana daura dan kwali ga dukkan alamu fita zatai domin ga Jakarta nan a gefe .
"Hmm amaryar sultan."
Karima ta fad'a tana kalloonta .
"Aunty Karima da Allah ki bani jan, janbaki nasa."
Inji Hadiza
Karima ta ce .
"Ki je ki dauko mana yana ciki, ki zo ki turan WhatsApp."
Hadiza ta mike da nufin dauko janbaki tana cewa.
"Wayar na jakata ai ki dauka ki tura Aunty."
Karima ta jawo jakar tare da zugeta, kana tasa hannu a ciki

Dasssss dauuu
Abin da Karima taji a zuciyarta, sakamakon cin karo da abu aleda
"Ido da kofato."
Cewar Karima tsoro ya kamata sosai , domin duk a tunanin ta idon mutum ne
Da gudu ta fad'a uwar daki tana cewa.
"Idon mutum a jakarki àljanu Hadiza."
Cikin matukar tsoro
Dariya Hadiza ta sheke da ita tana cewa
"Kai Aunty, wanne irin idon mutum, idon jaki ne fa."

"Me zaki dashi."?
Ba tare da kwanciyar hankali ba ta sake tambaya
Ajiyar zuciya Hadiza tai tare da aje janbakin tana cewa.
"Gaskiya Aunty bana so na fad'a miki, saboda karki fadawa Yaya Adam ya kashe ni."
Karima ta ce .
"Babu abin da zan fad'a masa."
Chapter 9 · 0% Book details