Sashe 7
Marubuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun asuba da Salma ta tashi bata koma ba , saboda irin tarin shauki da farin cikin da take ciki .
Wayarta ta dauka tare da yiwa Sir Sadiq Abubakar magana.
Nan suka gaisa ta gabatar masa da kanta, nan take ya fahimci wacce Aunty Hauwa tai masa magana akan ta ne .
Ta yi matukar farin cikin yadda shima ya karfafa mata gwiwa da yabon kokarinta sosai.
Haka ta cike form din shiga wannan kungiyar ta Lafazi writer's Association, kana ya sata cikin muhimman group na marubuta, ciki kuwa harda Bakandamiya reading club.
Ta samu kanta cikin matukar farin ciki sosai a wannan yanayi
Hakan yasa babu 'bata lokaci ta fara rubuta littafin ta na farko mai suna "FATIMA DA ZARAH."
Lokacin da take tunanin sunanta Salma Aminu Waziri , tai tunanin kawowa kanta matsala, hakan yasa ta canza sunanta zuwa Autar marubuta 💚
Haka har gari ya fara wayewa , Aunty Hauwa ta fara shirin fita , sai hankalin Salma ya tashi kuma , ganin cewa Anas yana nan kuma baza ta iya sanarwa da Aunty Hauwa wannan lamarin ba .
Hakan yasa bayan ta tafi , Salma ta rufe dakinta ta cigaba da abin dake gabanta .
Bayan wasu kwanaki......
Anan kuwa Masha Allah biki ya yi biki , Amarya Karima saidai mu ce Allah san ya alheri ya kawo na yan baya , lokacin da aka zo tafiya da Amarya su Husna an sha kuka , hatta shima Umar ya yi wannan kuka sakamakon yadda yake yawan tunanin Salma babu labarinta .
Bayan wani lokaci.
Hadiza ce kwance kamar kullm , sai dai a wannan lokacin tana bangaren Karima.
Datarta a kunne ta ga sako ya shigo daga cikin group dinta .
"Dan Allah Fatima da zarah daga page 5 zuwa inda aka tsaya."
Bayan ta karanta sakon tai shiru tare da tunanin ina tasan wannan Littafin Fatima da zarah.
Karima ce ta shigo ta katse ta da fad'in.
"Hadiza kin bar karamar wayarki dakin Mama ana ta kira ."
Hakan yasa ta tashi ta nufi cann , ita ma Karima wayarta ta dauka kai tsaye ta nufi WhatsApp, sakon kanwar ta Husna ta bude kana ta kunna voice din.
"Haba Aunty, to a gaida Yaya Adam din, kar dai garin karanta novels aje a kona masa girki.
Kuma Aunty har yau ina ta jira baki turan Littafin kanwar Yaya Adam din ba ."
Iya kar voice din ke nan .
Karima tai murmushi tare da maida mata da cewa.
"Ke yarinyar nan wallahi ki kiyaye ni ,wato wayar mommy kike dauka,kinga idan baba ya gano ki babu ruwana, sannan kuma rabu da littattafan Hadiza duk ba dadi na fita a channel da group din ta ma, akwai wata sabuwar marubuciya Autar marubuta zan turo miki link din group din ta."
Tana gama voice din ta tura mata, ganin Husna bata online yasa Karima kashe data
Duk su Aunty Hauwa suna falo, ana ta hira , Salma indai ba Aunty Hauwa bace ta dawo samm bata sakin jiki kamar haka .
"Gaskiya Salma kina kokari sosai wannan Littafin da kike rubuta wa Allah ya kara Basira."
Hajjiya Aisha ta ce .
"Amin summa Amin."
Anas yayi murmushi, Salma ta kauda kai ko kallonshi batai ba
"Aunty Hauwa gobe shekarar Umma 5 da rasuwa."
Cewar Anas
Aunty Hauwa ta ce .
"Haka ne ,ya akai baka manta ba , ai na zata ni ka dai nake lissafin."
Kafin ya kuma cewa komai Salma ta ce .
"Wa ce Umman."?
Anas ya bata amsa da fad'in.
"Mahaifiyar Aunty Hauwa ke nan , mutuniyar kirki."
Jin hakan yasa ta kalli hajjiya Aisha
"Dama ba tare suka rasu da su Daddy ba ."?
Salma ta tambayi Aunty Hauwa
"A'a ba tare bane Salma, su Baba da mijina ko shekara basi ba , sun yi accident ne ."😭
Ta karasa maganar tana kuka
"Haba Hauwa'u ki yi hakuri mana , ai addu'a ita ce komai." Cewar hajjiya Aisha
Salma ta ce .
"Haka ne, dan Allah Aunty ki yi hakuri Allah ya kara haske a kabarinsu ."..
Umman Salma ce zaune tana sauraran redio, kwana biyu kamar yadda take jin wata tasha da Salma ke saurara ita take saurara tunda Salma tabar gida.
Domin ana karanta littattafan Hausa kala kala na marubuta da dama , har akan gayyato wasu daga cikin marubutan, a dai dai wannan lokacin Malam Aminu ya shigo yana daddafa bango Umar ya rikeshi .
Da sauri ta tashi tana fad'in.
"Innalillahi Umar lafiya."?
Umar ya maida mata da fad'in.
"Wallahi Umma faduwa ya yi."
Ta sake fad'in.
"Subahanallahi." Ta fara kokarin kawo tabarma
"Mun gode Autar marubuta Allah ya kara Basira da daukaka."
"Gaskiya Fatima da zarah wannan Littafin ya yi Allah yasa a gama lafiya."
"Ikon Allah Fatima da zarah muna jiran cigaba, Allah ya sa afi haka."
Irin yadda Salma take karanta comments ke nan abin yana faranta mata sosai .
"Gaskiya Umma na samu kudi a wannan Littafin."
Cewar Hadiza
"Dubu 29 fa yanxu haka,kuma ba a gama siye ba nasan."
Karima dake yankan alaiyahu tai murmushi
"Tom ai ina miki addu'a Hadiza."
Cewar Ummanta
Ajiyar zuciya dai Karima tai cikin zuciyarta tana cewa.
"Allah ya shirya."
Wani dassss Salma taji a ranta ganin update din wani Littafi mai suna "Aure dadi ."
A cikin group din ta
Na
Hadiza RM
Abin data gani ke nan , zuciyarta taji tana mata zafi ganin irin yadda Hadiza ta sake kwarewa a shashanci da rubuta batsa babu ko kunya ko tsoron Allah.
Goge posting din tai tare da rubuta, "duk wacce ta sake turo irin wannan zan cire ta."
Kana ta fito daga group din tana mamaki. Cikin ikon Allah ta kammala Fatima da zarah harta fara wani Littafi mai suna .
"HIJIRA."
Anan kuwa gama cirewa Malam Aminu karin jini ke nan.
Matarshi dake zaune cikin damuwa ya kallah yana cewa.
"Yau baki kunna redion taki ba ."
Murmushi tai kafin ta ce .
"Hmm Malam ke nan, ai bana takura ma ba kana bacci ma Alaji Yusuf ya zo , ya ce zai dawo ."
Umar ne ya shigo yana dariya yana bude hakora gaban baban nashi ya zauna yana cewa.
"Baba yanzu aka aikon da sako a waya , wannan aikin na company da nake nema an dauke ni ."
Ya koma ya kalli Umma cikin farin ciki.
"Alhamdulillah , Alhamdulillah Umar Allah mun gode maka."
Umman Salma ta fad'a
Cikin karfin hali Malam Aminu ya nuna farin cikin sa matukar gaske , tare da yiwa Umar tarin nasihohi da fatan alheri, sannan Umar ya shirya domin tafiya gidansu Dawaki, da wannan babban zance mai dadi .
Autar marubuta
https://chat.whatsapp.com/G3YMYAHnKG4DiU7ZeuwDGk
*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️
Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️
A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>
Ku yi mini subscribe 🥰🥂🙏 Something big is coming....😌
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 17&18
Salma sai dai mu ce Alhamdulillah, domin tana da tarin mabiya da suke karanta Littafin ta, wani abin farin cikin da ya sake samunta shi ne , yadda masu YouTube suka sai Littafin nata akai audio dinsa, nan ne sunanta ya sake bunkasa domin ba karamin hikima da tunani aka zuwa a wannan Littafin mai suna Fatima da zarah ba , duk da cewa ta fara rubuta wani Littafin.
Aunty Hauwa tana tsaye cikin falo tana amsa waya, domin tana waya ne da yayan babanta, tana sanar dashi tafiyar da zatai zuwa Dubai .
Bayan ta gama ta dawo cikinsu hajjiya Aisha ta zauna, ta kalli Anas da fad'in.
"Tom tafiya ta zo ."
Salma da sam batasan da tafiyar ba ta kalleta tare da tambaya.
"Aunty wacce irin tafiya."?
Cikin damuwa ta tambaya
Da annuri a tare da ita ta ce.
"Daga wajen aiki ne Salma, zamu je Dubai wata biyu kawai zami ."
Ajiyar zuciya Salma tai kafin ta sake fad'in.
"Yaushe Aunty har wata biyu."?
"Eh Salma wata biyu zami , sauran sati daya mu tafi , amma ai ga mommy karki damu."
Ta nuna hajjiya Aisha
Hajjiya Aisha tai wa Salma murmushi tare da fad'in.
"Karki damu Salma, ai an zama daya , sai dai mi mata fatan Allah ya dawo da ita lafiya."
Ajiyar zuciya mai zafi Salma ta sake saukewa tana kallon Anas.
"Tab Aunty ni zaki bari a wannan gidan, wallahi akwai matsala."
Tai maganar cikin zuciyarta
Aunty Hauwa ce ta sake fad'in.
"Kuma ina dawowa zamu je Kano, wajen yayan baban naki.".
Salma tai murmushi mai cike da damuwa tare da cewa.
"Tom Aunty."
Tunani Salma ta sake lulukawa ciki tana hango irin damuwar da zata shiga a wannan gidan idan babu Aunty Hauwa.
Jikin Malam Aminu ya yi tsanani sosai, domin jiya ma a asubiti suka kwana, sai dai mu ce Allah ya bada lafiya
Su Aunty Hauwa suna cikin cigaba da hirarsu, aka fara kiran wayarta .
Ganin kanin babanta ne yasa ta tashi ta shige dakinta.
"Assalamualaikum Baba."
Abin da Aunty Hauwa ta ce ke nan bayan d'aga wayar
Daga can bangaren yayan baban nata ya ce .
"Wa'alaikumus salam Hauwa'u, muna waya na tafi wani uzurin ."
Da girmamawa ta ce .
"A'a babu komai Baba."
Jin hakan yasa ya cigaba da cewa.
"Tom wannan shi ne , da hajjiya Aisha zata bayar da kadarorin mahaifinki tuni ta bayar, to amma babu niyyar haka, dan haka kotu zamu kaita ."
Ajiyar zuciya Aunty Hauwa tai tare da cewa.
"Baba bawai bana so a tayar da maganar bane, ammma hajjiya Aisha duk ta canza wallahi kwana biyu, a yi hakuri idan na dawo daga Dubai sai a yi maganar, yi hakuri Baba."