Sashe 4
Marubuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sannan Zainab ta kalli Umar tana miki masa wannan Littafi na hadisi tana cewa.
"Yaya Umar naga wani rubutu a ciki Salma ce tayi ."
Jin haka yasa duk suka 'kagu dajin abin dake faruwa
"Mene a ciki karanto shi." Inji Alaji Yusuf
Yayin da Umar ke kokarin budewa , page din karshe da yake da rarar gun rubutu ya nufa kamar yadda Zainab tai masa nuni.
Yana bude gurin ya kallesu sannan ya fara karanta rubutun a zuciyarshi
Alaji Yusuf ne ya sake fad'in."Karanto mana Umar."
Umar cikin rashin jin dadi ya sake sa ido kan rubutun da akai da pencil.
"Zainab idan kin ga wannan rubutun ki kaiwa Yaya Umar, domin ni daga nan bansan inda zan nufa ba , saboda babansu Karima zai mai dani gidanshi, saboda baya so na cigaba da rubutu."
"Ina mai basu hakuri, na yanke wannan hukuncin ne domin cikar burina na zama marubuciya, Ina son rubutu kamar raina, kuma Ina San iyayena fiye da komai, amma zama gidansu Karima zai zama tarnaki ga burina, a yi hakuri a yafeni, kar kuma a neme ni domin nayi nisa daku ."
Daga karshe aka zana wata fuska tana kuka
Umar ya d'ago yana kallonsu
"Habawa habaawa, wannan shi ne abin da Salma zatai mana, mene ne mutane zasu ce innalillahi wa innailaihir rajiun." Inji Alaji Yusuf cikin matukar mamaki
Umma kawai kai ta durkusar ta fara kuka
Malam Aminu Kam yayi shiru yana mamakin ikon Allah.
Alaji Yusuf ne ya kuma fad'in."Wannan yarinyar ta lalata tarihin gidanmu , yanzu dai ta rantse sai ta yi wannan rubutun."
Malam Aminu ya ce .
"Tom yanzu me ne abin yi ."?
Umar ya yi shiru yana sake kallon wannan rubutun.
Cikin kuka Umma ta ce ."Ga shi nan yanzu Salma tabar gida mene aibun abin da take yi , Allah ne yasan sanda zanga Salma."
"Allah ya bayyana ki Salma, Allah ya kareki a duk inda kike." Ta sake fashewa da kuka
Alaji Yusuf ya ce ."Allah ya kyauta amma wannan yarinyar tayi rashin hankali ke taya kika samu wannan rubutun nata ." Ya nuna Zainab
Zainab ta ce .
"Jiya da muka taso daga islamiyya na bata, saboda zatai Assignment, kuma a jiyan ta dawon dashi, saida Yaya Umar ya kirani dana duba na gani ."
Alaji ya girgiza kai , haka duk jikinsu yayi sanyi babu wanda yaji dadin wannan abin, Alaji Yusuf ya koma gida.
Aiko yana isa gida duk suna zaune a falo suna jiranshi domin ya dawo suji inda aka kwana.
Jiki a sanyaye Alaji ya shiga gidan, domin yana tunanin silarsa ne Salma tai wannan aika aika .
"Alaji an ganta kuwa."?
Tambayar da mamansu Karima ta fara masa ke nan, zama yayi kan kujera yana cewa."Allah ya kyauta."
"Ta ya za a ganta ta gudu harda wasika ta ajiye."
Husna da Karima suka kalli juna
"Wai Alaji meke faruwa, sai kace za ai mata auren dole." Cewar ummansu Karima
Alaji Yusuf ya jingina jikin kujera yana cewa."Saboda mun hanata rubutu, mun hanata rubutun banza dana wofi shi yasa."
Sannan Alaji ya kalli Karima yana cewa.
"Ke Karima karki kuskure wannan zancen ya fita dangin mijin da zaki aura . Saboda Salma ta gama zubar mana da mutunci, idan kuwa kika sake kika saki baki zancen ya fita, to ina tabbatar miki kin samu abin Gori wajen dangin miji."
Karima ta sauke kai kasa
Umma ta ce ."To ubangiji Allah ya bayyana ta."
Alaji ya tashi ya shige ciki
Husna da lamarin ke dukanta ta ce ."Amma Aunty Salma ta yi rashin hankali wallahi."
Karima tai ajiyar zuciya tana girgiza kai .
Umman Salma ta matukar shiga wani yanayi, sai dai kawai Allah ya bayyana mana Salma
Salma tafiya tayi tafiya, tamkar Mahaukaciya ta koma , lokacin data fara hango bakin titi da giftawar abin hawa yasa ta dau damarar kaiwa wajen , tafiya ta fara yi sosai, abin da ya bata mamaki tana tafiya amma kamar bata yi , domin akwai gonaki sosai kafin ta kai ga bakin titi.
Haka har yamma ta kawo kai rana ta kusa faduwa, sannan ta isa wata gona ,daga wannan gonar sai titi.
Saidai babu kowa gurin banda wani tsoho da ya tula Kara kan kekensa.
Ganin yana shirin hawa ya tafi Salma ta nufi gunshi da sauri tana d'ingishi tana cewa."Baba. Baba."
Jin haka yasa tsohon dakatawa bayan yana shirin hawa.
Kallon Salma ya yi yana cewa."Ke yarinya yanzu ai babu aikin gona sai kuma gobe ."
"Gobe ki zo ."
Salma ta sake matsawa kusa da shi tana cewa."Baba ba aiki na zo ba , wai dan Allah nan wanne gari ne ."?
Dattijon ya sake kallon Salma da fad'in.
"Yarinyar baki san inda kike bane , ai nan Gombe ke nan ."
Wani dasss taji a ranta dajin irin amsar da ya bata .
"Gombe kuma ." Ta maimaita cikin mamaki tana duban garin.
Autar marubuta
*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️
Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin 👌🙏kar a yi kuskuren canza mini duk abin da aka gani a wannan labarin ✍️
A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<>
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 9&10
Haka wannan tsohon yaja kekensa ya tafi, tun Salma na hango shi , har ta dena ganinshi.
Ga magariba ta kawo kai, lokacin da ya tabbatar mata tana Jahar Gombe ta sake shi ga tashin hankali, kafadunta sun kunbura duk ciwuka a jikinsu .
Kuka ta fashe dashi ta kara matsawa bakin titi tana tare abin hawa , amma babu wanda yake tsayawa, domin wasu ma suna mata kallon Mahaukaciya ne .
A daidai wannan lokacin ne wata farar mota ta tsaya gaban Salma, sai dai bata iya ganin waye ciki , saboda bakin gilashi dake rufe .
A hankali akai kasa da gilas din motar
Salma cikin hawaye take kallon mai motar .
Wata farar matashiya ce mai kimanin shekaru 28
Sanye da abaya da rolling din mayafi, sai wani card dake sa'kale a wuyanta .
"Ke lafiya kike tsaye anan kina kuka ."?
Tambayar data fara jefawa Salma ke nan
"Wallahi ina bukatar taimako, tun daga Kano nake , yan fashi suka tare mu , sun kashe koya , muna ta gudu cikin Daji yanzu wani tsoho yake tabbatar mini a Gombe nake yanzu, babu wanda na sani ."
Ta karasa maganar da kuka
Matashiyar ta kalli Salma sama da kasa , ta kuma gamsu da jawabinta , hakan yasa tai jimm na wani lokaci kafin ta ce .
"Allah sarki.
Ki yi hakuri."
"Shigo ciki ."
Ba tare da Salma tai tunanin wanne irin hannu zata fad'a ba kawai ta shige cikin motar
Matar ta rufe glass din , suka tafi .
Ganin halin da Salma take ciki yasa matar murmushi tare da kara gudun na'urar sanyaya motar.
"Nagode Allah ya saka da alheri."
Salma ta kalli matashiyar ta fad'a cikin girmamawa
"Mene ne sunanki ."?
Matashiyar ta tambaya tare da karyawa da shiga zuwa wani titi da ya rabu biyu .
"Suna na Salma."
Matashiyar bata kuma cewa komai ba , kawai ta cigaba da tuki .
Wani titi ta sake shiga wanda kana iya gano wasu manya-manyan gidaje na masu kudi .
Nan tai tare da shiga wani lungu ta nufi wani babban gida launin toka .
Tana karasawa mai gadi ya bude mata babban bakin get din , kana ta shige .
Sannan tai burgi , ta fito ta budewa Salma kofa .
Salma ta fito tana kallon wannan katafaren gida tun kafin ta shiga ciki .
"Taho."
Matashiyar ta fad'a tare dasa kai ciki
Suna shiga falon , wata farar mata ce mai kimanin shekaru 47
Zaune tana cin abinci.
"Assalamualaikum."
Tai sallama
Matar bata amsa ba , hakan bai hana matashiyar zama a daya daga cikin kujerun alfarmar ba
Salma kamar mai jin tsoro ta karaso ta zauna a kasa
"Ina wuni hajjiya."?
Ta gaida wannan matar
A lokacin ta d'ago cikin isa tana cewa.
"Lfy lau, wannan kuma daga ina."?
Matashiyar kawai tai ajiyar zuciya tare da warware rolling din dake kanta .
Bayan Umman Salma ta idar da sallah, tai addu'a kamar yadda ta saba , sai dai kwana biyun nan tana yawan kuka , shima haka malam Aminu yana cikin damuwa Sosai, sai dai suna ta addu'a.
Hadiza ce ta ke sauraran voice din da Ruma ta aiko mata bayan ta gama saurara ta maida mata da cewa .
"Allah sarki kawata, wallahi nima bansan zamu tashi ba ,kawai abin ne ya zo ."
Sannan ta tura mata ,Ruma da kamar jira take a aiko tai saurin budewa tare da maido da amsa .
"To ai shikenan kawata, Allah ya sa haka ne yafi alheri, sai dai gaskiya ina kewarki sosai , sannan kuma in baki labari mutuniyarki Salma an nemeta an rasa wlh , ta gudu saboda kanin babanta ya hanata rubutu."
Bayan Hadiza ta gama saurara, ita ma ta maida mata da fad'in.
"Waii Ruma gaske ko karya , tab , dama ina ita ina had'a kanta dani to Allah ya kyauta."
Tana tura mata , ta bude group dinta domin yin reply
Wani sako ta gani wata mai irin sunata tana cewa.
"Muna godiya Aunty Hadiza, gaskiya wannan labarin akwai citta."
Ba tare data bata amsa ba ta sake karanta wani sako dake kasanshi .
"Mun gode, muna jiran update na yau dan Allah ,gaskiya Najif ba shi da hankali gaban kowa ya fad'a wa matarshi daga aure."
Ita ma bata bata amsa ba , ta fito daga group din kana ta bude wani sako wanda number babu suna .
"Wallahi kiji tsoron Allah, kina koyawa yara iskancin banza da sunan novels, Allah yana ganinki , ko mutuwa kikai wannan abin bazai goge ba , kin rubuta wallahi ki tuba ."
Bayan Hadiza ta gama karantawa kawai tai blocking din ta .