← Book details Marubuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 19

Sashe 10

Marubuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan Hadiza ta fara cewa.
"Tom Aunty kinga akwai wata marubuciya Autar marubuta tom tana son kawon matsala da rashin cigaba hatta novels dina tana cewa babu kyau wai haram ne , tom shi ne muka je gun wani malami ni da Umma, za a kuturtar da ita harda makancewa, dan Allah karki fadawa Yaya Adam."

Ai baki daya Karima mutuwar tsaye tai da jin wannan batu, haka Hadiza tasa mayafi ta fi ce
"Innalillahi wa innailaihir rajiun, wannan wacce irin zuciya ce da Umma da Hadiza, yanzu mene laifin wannan marubuciya, innalillahi wa innailaihir rajiun."
Cikin tashin hankali Karima ta zauna a bakin gado tana maganar

Jimm ta yi sosai domin wannan maganar ta girgiza ta matukar gaske , yanzu bata san mene abin yi ba .

Autar marubuta.

*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️

Kaggagen labari ne ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~

Autar marubuta ce
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇

https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 23&24

Bauchi

Karfe 11:20 Salma ta farka a bacci , sannan ta karewa dakin da take ciki kallo, kana ta mike ta fita tsakar gida, koda ta fita mai gidan da matarshi suna zaune suna ta hira
Salma ta durkusa gabansu tana cewa.
"Ina kwanan ku , kuyi hakuri ."
Murmushi mijin ya yi , kana ya ce.
"Aa karki damu, Fatima ki dauko mata abinci ta karya ."
Ta mike kamar yadda ya ce .
Ta kawowa Salma doya da kwai sai kunu a cikin kofi
"Na gode ."
Salma ta fad'a bayan ta aje mata a gabanta
"Ammma baiwar Allah kinga jikin ki babu wahala, taya zaki tsinci kanki a haka."
Cewar matar tashi Fatima
"My sweetheart ki bari ta huta mana kina mata wannan maganar ko abinci bata ci ba ."
Ya fad'a wa matarshi
Murmushi Salma tai tana cewa.
"A'a babu damuwa ai , daga Gombe nake , Aunty na ta tafi Dubai jiya , tom shi ne matar gidan ta koreni , suka ma siyar da gidan , sannan yaronta ya sacewa auntyna waya bayan ya rakata airport, ya zo ya sani a mota tun dare jiya , ya ce duk inda zani naje ."
"Gashi sai nan da wata biyu zata dawo ,babu inda na sani ."
"Allah sarki."
Ya fad'a yana kallon matarshi
"Tom ni suna na Aliyuu ga matata Fatima."
Salma ta ce .
"Ni suna na Salma."
Fatima ta ta'be baki tana kauda kai
"Zaki zauna damu tsawon wata biyun , idan Allah yasa ta dawo sai ki koma."
Aliyuu ya fad'a , da sauri matarshi Fatima ta kalleshi tana cewa.
"Baby kamar ya wata biyu, daga baka labari baka san gaske take ko karya ba , kawai sai ta zauna damu."
"Haba Fatima, duk da ba a gane macuci wannan yarinyar ai da gaskiyarta , ki dubeta fa mene wata biyu, taimako ne kawai ."

Salma kasa tai da kai kawai tai shiru , matar tashi ta mike ta shiga daki.
"Karki damu Salma ki zauna anan ki yi hakuri, kije ki ci abinci."
Ya shige yabi matar tashi, kana Salma tai ajiyar zuciya tare da daukar abincin tai daki ita ma .

Kano

Allah sarki baiwar Allah umman Salma tana zaune ta yi shiru. Tana rike da wata takarda a hannunta, jin Shigowar Umar yasa ta muskuta tana amsa sallamar da ya yi , tare da tura wannan takardar karkashinta ,gabanta ya zo ya tsuguna .
"Umma babu wata matsala ko, ko akwai abin da babu."?
Ta murmusa tare da fad'in.
"Allah ya maka albarka Umar, sai dai akwai komai , sai dai kuma Umar tunda Allah yasa kana aiki , ka yi aure mana, rufin asiri ya samu ai ."

Jin hakan yasa shi jin kunya .
"A'a Umma, ina nan ina jiran Salma inajin tabbas zata dawo."
Umma ta ce .
"A'a Umar, ni yanzu na cire rai da Salma, ka manta da ita kawai, haka ta zabarwa kanta ."
Umar ya ce .
"Tom Umma kinga wannan gidan, zan gyara miki shi asa tayill a gyara dakuna koina in Sha Allah."
Umma tai murmushi tare da fad'in.
"Tom Umar nagode."

Washe gari

Sokkoto ❤️
Tun jiya da Adam ya dawo daga aiki ya gaza gane kan Karima, sai dai Karima tunda taji zancen Hadiza duk ta rasa nutsuwa, duk da cewa batasan wannan marubuciya ba , amma abin da taji za ai mata ya matukar d'aga mata hankali, sai dai aduk tunanin ta babu hanyar da zata iya hana wannan aika_aika.

Misalin karfe 8 na safiya, Salma harta samu ta karya ta yi wanka , kana shi Aliyuu ma har ya tafi wajen sana'arshi ta shayi da burodi .
Jimmm ta yi sakamakon yadda taji kanta yana mata ciwo sosai .
"Allah sarki Aunty Hauwa, kona kira bana samu ."
Tai maganar tare da tuna cewa ta ce ."Ta tura mata dubu 30."
Murmushi Salma tai tare da ciro wayarta a caji da nufin shiga opay .
Diffffff
Salma duhu kawai ta gani , tasan da cewa waya ce a hannunta, amma bata iya ganin komai sai duhu .
"Innalillahi wa innailaihir rajiun meke faruwa."?
Ta fad'a cikin tashin hankali tare da wurgar da wayar hannunta.
"Aunty."
"Aunty Fatima."
"Auntyyyy."
Salma tana kira cikin tashin hankali, yadda matar aliyuu taji tana kiranta , dah kamar baza ta fito ba , amma ta fito ta shiga dakin
Ganin idanun Salma a bude yasa tai tsaki tana fad'in.
"Kina ta kirana kamar makauniya lafiya."?
Salma ta daddafa ta mike tsaye tare da fad'in.
"Wallahi Aunty bana ganin komai sai duhu, bana ganin komai wallahi."
Ta fashe da kuka.
"Okay wata yaudarar kika zo msna da ita ke nan, to wallahi kiji tsoron Allah mijina ba kudi gareshi ba , shayi da burodi ne yake siyarwa."
Fatima ke nan
Cikin sabon tashin hankali Salma ta ce .
"Innalillahi wa innailaihir rajiun."😭
Ta ke ce da wani kuka sai ga wasu hawaye zirrrr
Sai a lokacin fatima ta matsa kusa da ita , kana tasa hannu a fuskar ta , don tabbatar da bata gani .
"Innalillahi tom garin ya kika dena gani Salma, dama kina irin wannan ne , ko kina da àljanu."?
Da mamaki Fatima tai maganar tana jahh da baya ,
Fi ce wa tai tare da daukar wayarta, kai tsaye ta kira mijinta, dake shima dan albarka ne ko minti 10 bai bata ba , sai gashi ya zo
Tsakar gida ya samesu dake Fatima ta riko hannunta sun fito
"Me ke faruwa haka ne ? Da gaske bata gani."?
Da rudewa ya ke maganar
"Wallahi kuwa, ina daki take kirana."
Fatima ta ba shi amsa

Aliyuu ya juya ya juyo da matukar mamaki .
"To ai gara mu tafi asubiti, tun kafin lamarin ya yi tsamari ."
Haka suka wu ce suka tafi asubiti, aiko suna isa likitan ido ya zo ya duba Salma.
"Dactor ya ake ciki to ."?
Likitan ya kalli Aliyuu yana ba shi amsa da fad'in. "A'a karka damu ba babbar matsala ba ce , muna warware irin wannan da dama , dan haka in sha Allah zata sami lafiya, sai dai akwai kudade sosai da zaku cire , domin magunguna idan ta kama harda aiki ma ."
Ajiyar zuciya Aliyuu ya yi yana kallon Salma "Tom shi ke nan likita."
"Yaya Aliyuu akwai dubu 30 cikin account dina , sannan a gida ina da laptop, a siyar tare da wayata ."
Matukar tausayin Salma ne ya sake rufe Aliyuu, sai da wasu hawaye su ga gangaro masa , yasa hannu ya share .
"Tabb sannu wai kuka kake yi nan , idan bani da lafiya ko irin wannan baka mini."
Cewar Fatima
Da fuskar tausayi ya kalleta " Haba Fatima ki dubi halin da take ciki ."

Ya koma ya kalli Salma dake cikin damuwa da hawaye ya ce .
"Ki yi hakuri Salma, ni ba mutum ba ne mai kudi, banda haka bazan siyar da laptop da wayarki ba , sai na siyar na hada da nawa zan samu damar ....."
Bai kai aya ba Salma ta katse shi .
"Na sani , ko baka ce ba , babu yadda zan da wannan kaddarar ."😭
Ta cigaba da kuka ,da sauri Aliyuu ya fice cikin wani yanayi .

Fatima ce ta zauna wajen Salma har wajen magariba , tunda Aliyuu ya fita bai dawo ba sai a wannan lokacin
"Wai sai yanzu zaka dawo haba , ka barmu da yunwa babu kudi ."
Abin da Fatima ta fara tarar shi dashi ke nan
Wani bacin rai yaji ya turnike masa zuciya, kawai shiru ya yi , ya kalli Salma da fad'in.
"Ya jikin naki Salma."?
"Da sauki ."
Ta bashi amsa
"Tom kin ga yanzu haka na hado dubu dari biyu Salma, sannan SMS dinki suna kasa ."
"Dan haka bari naje gun likita ."
"Wai dan Allah mene ne na wannan barin jikin, na ce maka yunwa nake ji , ammma sai ta wannan yarinyar kake yi ."
Yaji wani abu ya tokare masa makogaronsa, ya fita babu cewa komai
"Wallahi bari Baba ta dawo daga katsina ,zaku had'u."
Abin da Fatima ta fad'a ke nan tana kallon Salma da harara

Autar marubuta
07040805269

*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*🥰✍️

Kaggagen labari ne ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~

Autar marubuta ce
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...🥂👇
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 25&26

Bayan Aliyuu ya kai wannan kudin , likita ya rubuta musu wani magani suka siyo , ya ce a diga cikin idon nata , haka dai har kwana uku babu wani canji duk da irin magunguna da Salma take sha , hakan yasa likitan ya musu transfer zuwa babban asubitin da ake duba marasa lafiyar ido , domin yi wa Salma aiki .
Chapter 10 · 0% Book details