← Book details Marubuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 19

Sashe 15

Marubuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karima da Adam ne suke karyawa, farin ciki ya ishi Karima, domin kuwa jiya da dare bayan ya dawo ya taho mata da wayarta, sannan yake tabbatar mata yanzu idan ya fita zai sa a sako mata data

"Wai kuwa kin karbo dinkin ki Karima, bukin nan fa sauran kwana biyu."
Cikin shagwababbabbiyar murya Karima ta ce da mijin nata "Ni ban karbo ba , kai ne zaka anso mini."

Ya kalleta da cewa.
"Ni kuma , ina ni ina shiga gidan mata ."
"Ni dai ba ruwana." Cewar Karima
Mikewa Adam ya yi ya dauki jakar shi ."Tom ni dai zan tafi my love ki kula da kanki ." Nan ta mike sukai sallama sannan ya wuce gun aikinshi na asubiti

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 35&36

"Jama'a anan muka kawo karshen wannan Littafin namu mai suna Fatima da zarah."
"Na wannan shahararriyar marubuciya Autar marubuta."
Umman Salma ke nan dake sauraran redio.
Nan ita ma Karima tana zaune tana bude WhatsApp take sauraran wannan gidan redio, daidai lokacin da yake cewa.
"In sha Allahu gobe misalin karfe 4 na yamma zamu kasance tare da wannan marubuciya a wannan gidan mai albarka." "Ga duk masu son turo sako zasu iya fara turowa tun yanzu a wannan number kamar haka."...
Sai ga Hadiza ta shigo
Firgita Karima ta yi ganin Shigowar Hadiza, domin kullum Karima bata barin Hadiza taji tana sauraran Littafin Autar ,
"Gaskiya ne Aunty ki ce kema kina yin wannan marubuciya." Cewar Hadiza
Hade rai Karima tai sannan ta ce ."Ina fa , kawai ina kamo tashar naji ana fad'a, to amma naji ya ce za a gayyato ta , taji sauki ke nan."?
Ajiyar zuciya mai zafi Hadiza tai , sannan ta fara cewa.
"Shegiya ba , ai Aunty Karima ki bari kawai, gobe ranar aure na , kuma gobe sai na yi ajalin wannan yarinyar, farin ciki biyu, ki duba fa wannan fim din da ake mai suna Zumunci ita ce writer fa ."

Murmushin yake Karima tai sannan ta kashe redion.
Hannun Hadiza ta ja wo tana zaunar da ita ."Haba Hadiza, me ne wai wannan marubuciya tai miki, kisa fa ba abin wasa bane ."
Hadiza ta janye hannunta tana cewa.
"Wannan yarinyar sunanta Salma Aminu kuma 'yar tarauni ce a Kano, shekara wajen biyu ke nan da guduwa daga gidansu , dan kawai tana so tai gasa dani a duniyar marubuta, na tsaneta wallahi Aunty."

Wani faduwar gaba Karima taji da tashin hankali.
"Salma kuma ."
Ta maimaita sunan cikin tashin hankali
"Eh sunanta Salma a tarauni take . Ko kin santa yar Kano ce ."

Sai da Karima ta fara mutuwar zaune, kana ta jingina da kujera."A'a bansan ta ba Hadiza, amma yanzu ta ya zaki kasheta kanon zaki je ke nan."?

Jin hakan yasa Hadiza dariya ta ce .
"Haba Aunty, nima fa yar kano ce , kuma ita yanzu tana Gombe, amma gobe zata zo gidan redio, kuma nasan wanne gidan redion ne , shi yasa tun jiya na kira wani domin a gama da ita ."

Karima jin kanta tayi ya kuma mata nauyi sosai .
"Kamar ya to."?
Ta tambayi Hadiza
"Zai tsaya da babbar mota, nasan da cewa a mota zata zo Kano , kafin ta karasa gidan redion ta mutu , shi kuma ya fito ya gudu , zan kasheta tun kafin iyayenta su san tana raye , domin har yau bata koma Kano ba ."Tana gama fade ta mike tsaye
"Aunty zanje salun ne fa , zuwa anjuma zan dawo ."
Karima ta ce . "Tom Allah ya kaimu."
Kana ta fice Karima na binta da kallo
Kanta taji ya sara mata kamar zai fashe
"Daman Salma ce wannan, innalillahi wa innailaihir rajiun, meke shirin faruwa ne."?
Karima tai maganar cikin sabon tashin hankali
"Tabbas Hadiza bazan bari ki kashe yar uwata ba , ke azzaluma ce Hadiza jahila mara ilmi, to wallahi ko hakan zai sanadin rabuwata da Adam sai na tona asirinki."

Karima ta dafe kai tana tunanin yanzu me ya kamata ta yi , wayarta ta dauka tai sauri ta bude WhatsApp, kafin ta nemo number wayar Salma nertwork ya dauke baki daya .haka Karima ta ringa sintiri cikin tashin hankali, babu wanda ta iya fad'a wa wannan maganar
Nertwork bai dawo ba duk irin zaman da Karima ta zauna jira har karfe 12 bacci ya kwashe ta
Washe gari da safe kuwa, Karima harta zuge ta rame , anjuma za a daura auren Hadiza da a karfe biyu, domin kuwa har baki sun fara zuwa.
Tun asuba ta fara yiwa Salma magana a WhatsApp, amma Salma ta hau bata duba ba , hakan yasa ta ringa mata flashing na company, amma Salma bata biyoba , da sassafen nan Karima ta fita ta siyo Kati .

Ita kuwa Salma tun da ta tashi da asuba hankalinta yake tashe , shi yasa ko damar duba waya bata dashi , sam ta kasa samun sukuni, hakan yasa ta nufi dakin Aunty Hauwa
Tana zaune tana jan carbi , tasan sam bata ganin Salma a dakinta a irin wannan safiyar.
"Salma lafiya meke faruwa, kar dai ki ce mini Kano ne baki son zuwa." Cewar Aunty Hauwa dake kan sallaya , yake Salma tai ta zauna cikin mutuwar jiki.
"A'a Aunty ba haka ba ne , ina son fad'a miki wani abu."

"A'a mene haka kuma Salma fad'a mini da sauri mene ne ."? In ji Aunty
Idanunta Salma kamar zatai kuma ta ce .
"Amma ki mini alkawari, baza ki juya mini baya ba , ko ki kasa fahimta ta ."
Jin hakan ya sa hankalin Aunty Hauwa ya tashi.
"Haba Salma mene haka, fad'a mini mene ne."?
Salma ta sunkuyar da kai kasa duk ta tada hankalin Aunty Hauwa
"Ina jin ki ." Cewar Aunty Hauwa da matukar 'kaguwa taji wannan maganar
D'ago kai ta yi tana cewa.
"Da farko ki yi hakuri, na shirya karbar duk kan hukuncin da zaki mini Aunty." Taja numfashi sannan ta cigaba da cewa. "Aunty Hauwa mahaifiyata da mahaifina suna raye a wannan duniyar."

"Kamar ya."?
In jita
Salma ta ce . "Kwarai kuwa na yi miki karyar cewa kanin babana ne ya koreni a gidansa, maganar gaskiya babu wanda ya mini hakan, nabar gida ne saboda kanin babana baya son na zama marubuciya, hakan yasa yake zuga banana."

Cikin sabon mamaki Aunty Hauwa ta ce .
"Ni fa ban fahimta ba Salma." Nan Salma ta zage ta warware mata komai da ya baro da ita daga gidansu har da yin kuka
Shiru Aunty Hauwa tai ranta babu dadi , cikin wata irin murya ta ce . "Kina nufin karya kika mini a komai, har zuwa Bauchi ke nan da cewa kin makance ."?

Da sauri Salma ta girgiza kai tana cewa. "A'a wallahi Aunty, wannan gaskiya ne , har zuwa Gombe da nayi a kafa , nasan nayi kuskure dan Allah ki yi hakuri." Cikin kuka tai magana
Yadda ta ga fuskar aunty Hauwa yasa Salma sake rudewa da kuka .
"Salma wannan ai yarinta ne da rashin hankali, tsawon lokaci da duk irin wahalar da kika sha, amma baki koma gida ba , wannan wacce irin zuciya ce dake , baki tunanin halin da iyayenki zasu shigaba Salma, shekara biyu harda watanni , ko dan kina da iyayen ne kike haka , ." Cikin zafi Salma ta ga Aunty Hauwa tana maganar

Da sauri Salma ta sake matsawa kusa da ita tana sake rushewa da kuka , ta rike hannunta.
"Wallahi ba haka bane Aunty, wallahi ba haka bane , ina kaunar iyayena, babana yana jin duk maganar da yayanshi ya fad'a masa, yana girmamashi sosai ."
Cikin sake turo sabon kuka Salma ta cigaba da fad'in. "Hakan yasa ya ce zan koma gidanshi, wallahi idan na koma gidanshi burina bazai taba cika ba , yana da zafi yana da tsauri."
Ta aje ajiyar zuciya ta cigaba da damke hannun Aunty Hauwa tana cewa.
"Sannan ina son tabbatar wa mutanen da suke tunanin marubuta ne ke lalata tarbiya, ba haka bane,mutane da yawa suna mana wannan kallon , cikin burina harda tarwatsa alkalamin marubutan batsa, shin ba babban abu bane Aunty, ko kuwa ya dace su hanani."? Cikin jajayen idanu Salma ta gigice da kuka tana kwanciya a kafarta.
Jinkin Aunty Hauwa taji ya mata sanyi , ta sa hannu ta d'ago Salma dake sharar kuka tana cewa.
"Haka ne Salma, amma tuntuni da kin fad'a mini , sai naje na same su , da duk haka basu faruwa."
Salma da shashshekar kuka ta ce .
"Wallahi baza su amince ba , domin ya canza musu tunani, amma Aunty gani , ki hukunta ni dan Allah kafin mu je Kano si mini nasu, ki hukunta ni Aunty." Jin wani kuka mai gwanin ban tausayi yasa Aunty Hauwa ta rumgumeta. Sunyi wajen minti guda a haka, tana sauraran kukan Salma
Daga bisani ta d'ago Salma tana murmushi da cewa.
"Shi ke nan, ya isa , ta faru kuma ta kare Salma, sai dai kin yi kuskure amma ni na yafe miki."
"Ta shi kije ki yi wanka , gashi har 7 ta yi ."
Salma ta share hawaye da cewa. "Bazan ta'ba mancewa dake ba Aunty, ke ce nasarata kuma rayuwa ta."

Aunty harara ta jefa mata kana ta ce ."Tom gwana sarkin barin gidansu ai mini shiru."
Dariya Salma tai hakan yasa itama tai dariya tana cewa.
"Ki tashi fa zuwa 12 nake son muje gidan redion nan mu gama komai ."
Salma da jajayen idanu ta ce . "Ke nan hirar ba kai tsaye ba ce ."?
Aunty ta bata amsa da fad'in.
"Eh sai karfe 4 zasu sake ta ."
Aunty Hauwa ta mike tsaye tare da cire hijabi tana cewa. "Okay yanzu na gane abin da yasa ba kya hira da kafafen sada tsumunta , Allah ya shirya ki ."
Salma tai dariya gami da hawaye.

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 37&38
Chapter 15 · 0% Book details