← Book details Marubuciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 19

Sashe 18

Marubuciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan kuwa hankalin mutane duk ya tashi, ko aure ba a daura ba an tafi da Amarya har Jahar Kano, hakan yasa ango da zugarshi suka bisu , jingum-jingum kowa ya yi a cikin gida , saboda labari ya zo musu cewa ana tuhumar Hadiza da kisan kai ne ..
Sai da wajen misalin karfe 4:30 su Aunty Hauwa suka samu suka taho, bayan Hadiza ta amsa laifinta tare da nadama, sai dai babban abin da ya Sanya Hadiza amsa laifinta babu bata lokaci, ganin Sultan da Alaji Babawo a wannan gurin, domin a tunanin ta tabbas za ai mata uzuri da alfarma, domin babban mutum ne Alaji Babawo.
Sai dai aka sin haka ne ya faru , domin kuwa yana jin hakan ya yi Allah Wadai yaja zugarshi suka koma sokkoto .domin ya ce yarinyar da zata iya wannan, to tabbas zata iya kashe masa sultan.
Anan kuwa umman Salma tana cikin matukar tashin hankali, domin tunda ta fara sauraran hirar da aka saki cikin gidan wannan redion ta kasa sukuni
Hakan yasa ta kira Umar yana cann kallon Ball
Da sauri ya iso gida, domin ya ga irin Kiran da take masa, yana shiga a tsaye ya sameta
"Umma lafiya, me yake faruwa ne."?
Umman Salma ta nuna masa redion tana cewa. "Wallahi Umar yanzu naji anan gidan redion, wannan Autar marubutar Salma ce , Salma ta ce ."
Jin wannan batu yasa Umar rike haba tana cewa. "Salma kuma Umma? Ko dai mai irin sunanta."?
Umma ta ce . "Ka tsaya ka sauraran Umar wallahi wannan yata ce Salma, muryar ta ma bata canza ba har irin dariyar ta."
Shi dai Umar lamarin ya daure masa kai , baisan ta Ina zai fara ba
Da kyar Salma ta iya gane gidansu, saboda gyaran da yaji da kuma tarin sabbin gine- gine .
"Assalamualaikum."
Salma ta fara shiga cikin falon tare da tashin hankali, Umar da Umma suna tsaye
Babu Wanda ya amsa sallamar duk a cikinsu, har ita ma Aunty Hauwa ta shigo .
"Salma."
Cewar Umar, murmushi mai ciwo Salma tai sannan ta ce .
"Na am Yaya Umar." Yayin da idanunta suka kawo ruwa , Umma take kallo cikin matukar tashin hankali da tsananin kewa da kauna har hawaye suka fara zubo mata, ita ma Umma hawaye ne suka zubo mata , amma ta share su cikin kwarin gwiwa.
Da sauri Salma tai yunkurin sunkuyawa gaban Umma
Amma Umma cikin izza ta dakatar da ita tana cewa.
"Dakata anan."
Jin hakan yasa su duk mamaki
"Dakata anan ." Ta sake fad'a, sannan ta cigaba da cewa.
"Ya kamata ki nemi izini yayin shigowa gidan mutane, domin kina daya daga cikin Wanda ba muharraman wannan gida ba ."
Cikin wani sabon tashin hankali Salma ta zaro idanu tana cewa.
"Umma me kike fad'a ne , baki gane ni ba ne? Salma ce fa yarki."
Jin wannan maganar ya sake fusata Umma.
"Bani da wata 'ya a wannan duniyar, Ina so ki fitar mini a gida yanzu."
Kuka Salma ta rushe dashi mai matukar gwanin ban tausayi, aunty Hauwa babu abin da ta iya fad'a a wannan yanayi
"Ba haka Ummana take ba wallahi, Ummana nasan tana kewar gani na kuma tana kaunata " Cewar Salma cikin kuka
Babu annuri ko kadan a fuskar Umma ta ce. "Salma burinki ya cika ,kin samu daukaka kin samu kudi, babu abin da ya rage fa ce ki canja iyaye da zasi daidai da kudi da daukakarki."
Umma taja numfashi na bacin rai sannan ta cigaba da cewa.
"Kin tafi kin bar gida babu tunanin wanne hali muke ciki , babu neman mu har Saida burinki ya cika , ki fitar mini a gida Kona miki abin da baki tunanin shi ba ."
Kuka ta sake kecewa dashi tana faduwa kasa tana cewa."Haba Umma, Haba Umma."
Zazzafar ajiyar zuciya Umar ya sauke sannan ya ce . "Haba Umma, idan rai ya baci hankali ba ya gushewa."
"Kayi mini shiru Umar tun kafin na bata maka rai ." Inji Umma
Umar ya sake ajiyar zuciya tare da fad'in."Ki gafarce ni Umma, amma bazan iya shiru ki cigaba da cutar da kanki ba, domin kullum kina addu'a Allah ya kare Salma ya kuma dawo da ita zuwa gareki "
"Ki yi hakuri Umma ga Salma ta dawo, tabbas kina da damar hukunta Salma, sai dai karki hukunta kanki , domin har yanzu kina kaunar Salma fiye da komai, har sauraran gidan redion novels kike saboda kewarta."
Umma ta sunkuyar da Kai kasa, yayin da Salma take mikewa tsaye tana ci gaba da kuka
"Yanzu da zarar Salma ta juya , kuncin da zaki kuma shiga Allah ne masani Umma, Dan Allah ki yi hakuri, yanzun nan fa kika kirani cewa kinji Salma gidan redio, kin kasa samun sukuni, to me yasa ta zo gabanki zaki mata haka ."?
Jin wannan zan tuka na Umar yasa jikin Umma sanyi ta fara kuka
Da sauri Salma ta fara fad'in. "Dan Allah Umma ki dena kuka, wallahi Umma ina kaunar ki, rayuwar masifar dana shiga ta hanani zuwa gareku shekara biyu da watanni kuna zuciya ta, dan Allah Umma ku yafe mini dan Allah Umma."
Da sauri Salma ta fad'a jikin Umma tana kuka, jin Salma a jikinta yasa Umma ta rumgumeta ita ma tana kuka
Aunty Hauwa tai murmushi tare da kallon Umar
Kuka mai gwanin ban tausayi Salma take yi tana cewa."Ki yafe mini Umma, ki yi hakuri, tabbas nayi ba daidai ba wallahi, amma badan kudi ko daukaka ba Umma, ki yi hakuri Umma ki yi hakuri."
Umma jin Salma tana wannan maganar cikin kuka ya sake karya mata zuciya tana sake rumgumeta
"Na ga rayuwa mara adadi Umma, banyi zaton sake ganinki ba da Baba, amma cikin ikon Allah Aunty Hauwa ta zame mini gata , wallahi Umma na yi kewarku ki furta kin yafe mini dan Allah."
Cewar Salma ke nan cikin kukanta
"Na yafe miki Salma, wallahi na yafe miki." Jin hakan yasa Aunty Hauwa da Umar wani murmushi suna ta ya Salma farin ciki
Sakin Umman nata tayi , tana kallonta cikin idanunta da har sun kunbura tsabar kuka ."Umma ina Baba nasan zai yi fishi dani sosai fi ye da ke , ku hukunta ni Umma amma karku mance ni 'yar ku ce , da ta yi kuskure ."

Taja numfashi tana kallon Umar, "Yaya Umar ina baba yake ."?
Umar ya kalli Umma yayin da suke had'a idanu, ganinsu kamar marasa gaskiya yasa Salma rudewa
"Umma ina Baba ya ke ." ? Cikin tashin hankali ta sake tambaya
Babu wanda ya bata amsa cikinsu, hakan yasa take jin tabbas wani abin ya same shi
"Ko ya mutu ne ."?
Cikin tashin hankali ta fad'a tana rike baki, da sauri Umma ta matsa ta bude wata dirowa tana dauko wata takarda, ta mikawa Salma
Da sauri ta karbe jikinta da hannayenta na rawa ta bude takardar

Autar marubuta

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 43&44. End.

Allah - Allah Salma take ta fara karantawa cikin zuciyarta ba tare da nutsuwa ba ta fara karanta rubutun mai blue biro .
"Assalamualaikum 'yata Salma, nasan komai dadewa zaki dawo wannan gidan, ni kuma wata kila kafin wannan lokacin bana raye, hakan yasa nake son sanar dake cewa, ban ta'ba kyamar rubutun da kike yi ba , na biyewa yayana ne matsayinsa na babba da yake da wahalar fahimta, amma sai gashi matsalar ta kai ga har kin bar gida ."
Salma ganin wata fuska da aka zana tana kuka ne yasa hankalin ta sake tashi tana rudewa da kuka, a wannan yanayi ta cigaba da karanta wannan takardar
"Duk inda kike Allah ya kare ki , ki girmama yayana domin shima mahaifinki ne , na yafe miki Salma duk abin da kikai mini , Bissalam."
Karshen rubutun ke nan , kudundune takardar tai cikin hannunta tare da shiga wani sabon yanayi, hakan yasa Umma jin tausayin Salma
"Baba ya rasu ke nan Umma, ya rasu ke nan Umma, innalillahi wa innailaihir rajiun, innalillahi wa innailaihir rajiun."😭
Maganar Salma ke nan cikin sabon yanayi mara dadi
Aunty Hauwa hawaye taji sun zubo mata, saboda irin yadda Salma tai matukar bata tausayi
"Allah ya yi masa rasuwa Salma, yanzu shekara 1 ke nan, yana sauran kwana biyu zai rasu ya bani wannan takardar." Inji Umma cikin damuwa
Sunkuya Salma tai bisa jirin da take ji , ta zauna a kasa tana dafa kanta tana cewa.
"Allah ya jikanka Baba, babu rabon mu sake ganin juna , Allah sarki babana."
Ta mike tsaye kamar an tsireta tana kallon Umar da cewa.
"Yaya Umar ina son zan je kabarinsa, ka rakani dan Allah."
Umar ya ce . "Tom shi ke nan."
Umma ce ta kalli Aunty Hauwa tana cewa.
"Baiwar Allah ki karaso ki zauna mana".
Hakan yasa Aunty Hauwa zama tare da gashshe da Umma tana mata ta'aziyya tare da rarrashi .
"Umma wannan ita ce Aunty Hauwa." Cewar Salma
Nan shima Umar ya zauna Salma tana basu labarin irin rayuwar data shiga tunda ta fice a wannan daren , Umma ta tausaya mata sosai, sannan ta jinjinawa aunty Hauwa tare da mata godiya sosai,
Wajen karfe 6 Yaya Umar yake kiran Alaji Yusuf yake sanar dashi dawowar Salma, a cikin dare kuwa sai ga zainab ta zo , bayan an sanar da ita
Aunty Hauwa ita ma a wannan gida ta kwana da sassafe Umma ta tashi ta dora musu doya da kwai , Umar ya siyo breadi
Chapter 18 · 0% Book details