← Book details Maraicin Nawaf 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 7

Sashe 4

Maraicin Nawaf 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

STORY AND WRITING
BY
*MAMAN BABY💝AUTAR MARUBUTA*

*MARUBUCIYAR*

*MIJIN TACE*
*KATANGAR NERA*
*SAI KAMIN KISHIYA*
*DA*
👇🏻
*MARAICIN NAWAF*
______________________________________
*SHAFI NA HAMSIN DANA MASIN DABIYAR*
______________________________________

*🌎MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚🖊�*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

_Wanan shafin nakune Khadija Muhammad da Rufaida ina yinku🥰_

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

........📖 Inna lami tace Nawaf dakarfi sai kuma tafashe da kuka tanacewa"Nawaf dama Kana Raye"?

Nawaf yace"ina Raye Inna bakiso hakabako"?

Allah daya halicce ni shiyara yani yahadani da iyaye nagari Wanda banida kamarsu suka rikeni tsakani da Allah.!!!!

Inna lami tafashe da kuka tace Allah sarki Nawaf rayauwa k'enan Dan Allah Dan Annabi rahama kayafemin Wlh Allah nayi nadamar abunda na Aikata Bayan tafiyar ka abubuwa da yawa sunfaru Dani Dan Allah Kaya femun Inna lami Tafada Tana kuka me tsuma rai tafada gaban Nawaf.....

Aisai taba su Nawaf da Abbu tausai matuka ganin yadda tak'e kuka Tana rokon Nawaf...

Nawaf yatashi yakamota yace"Kidena kuka Inna nide kam naya femaki Allah mamuna maahi lefi yayafemana to ni wanene da bazan yafeba harga Allah nayafe yan zu Kigaya Mana suwaye ku kuma kibani labarin mahaifina..."

Inna lami "tace to bakagayamin suwaye wadan nan tananuna su Abbu da Ummi."?

Nawaf yayi murmushi yace "Allah sarki iyayan kwarai Wanan shine Abbu yana nuna Abbu yanuna Ummi yace wannan kuma itace Ummina Sune iyayena Dasuka raineni bayan Asabe tayaddani tatafiyarta"!!!! yafadamata dauk yadda abun yakasance.....

Inna lami tace "Allah sarki Allah yasaka maku da Alheri kunyi Abunda bakowane zeyiba harma Dani dayake da agurina Allah yayimaku keyakeyawan sakamako."

Su Abbu sukace"Ameen bakomi Aidanakowane."

Nawaf Yace" Inna kibamu labarin rayauwarku da Mamana dana Babana".

Inna lami tashare hawaye tace yanzu kuwa.....Anan takwashe Kaf tarihin rayauwarsu tabasu.....bayan tagama basu Tana kuka Nawaf nayi Sai su Abbu ne K'erararashinsu....

Nawaf yashare hawaye yace"Bayan Kunbaro Katsina Kinsake komawa "?

Inna lami cikin kuka "tace Wallahi nayi nadama Amman tsoro yahanani komawa"...

Nawaf yace to kishirya gobe In Allah yakaimu zamuje...

Inna lami tace "to Nawaf Allah yakaimu".

Wai ina malam da mujahid bangansuba cewar Nawaf.!!!?

Inna lami tasake fashewa da Kuka tace"

Ai bayan tafiyarka Anyi wasu mamakon, ruwa kusan duk unguwar nan bagidan, da be zubeba gini ya rufto masu, malam da mujahid Anan take suka Amsa kira bayan rasuwansu nashiga matsin rayauwa bacin yau bare nagobe basutura gashi banida kowa agarin nan sai Asabe Kawata Itakima wata Rana, Akakamata Agurin safaran yara kotu tayankemata hukunci Daga nan bankara jin labarinta, ba....to kunji yadda rayauwa tajuya man baya shiyasa Nike nadamar Abubuwan da na Aikata nasan ko Hakkin ku da na iyayena yasata awanan halin tana fada Tana kuka metsuma rai daganinta tayi nadama.....

Nawaf yace"Kiyi hakuri Allah yajikan su malam".

tace Ameen

Ummi tatashi taje gaban Inna lami tana rarrashinta....

*Washe gari*

Guk sunshirya Dan tafiya Katsina sai de Inna lami batada wasu kaya nakirki dazatasa sai da Nawaf yaje ya siyomata dinkaku tasa yasiyo masu Kalaci me kyau sukaci suka dau hanyar Katsina tadukko Dakin Kara......

KATSINA
"""""""""""««««««««""""""""""

Bayan sun sauka Katsina sai Nawaf yak'e tanbayar Inna lami wace Unguwa suka dosa...

Inna lami taKwatanta mishi Allah yaso yana Dan shigowa Katsinar yasan wasu Unguwanni aciki garin....

Bayan sunje Unguwar Dutsin safe lokas Sukayi Parking Awani Katan gida mefadin gaske Gashi ya hadu bakarya Yasha ginin zamani me Burgewa da kayatar da Wanda yaganshi..

Inna lami taga gida yacinza yazama hadade kuma da alama part part ne saboda gidan gaskiya Katon gaskene tace"Nawaf Anya gidanne."?

Nawaf yayi Murmushi yace"to Inna shekaru da yawa mude muje mugani"

Ummi tace"Dan Allah kikwantar da hankalinki insha Allah nanne."

Inna lami takada Kai kamar wata kadangaruwa...

Suka nufi cikin gidan sukasa megadi yayo masu sallama meganiyacw waza'acer...?

Nawaf yace"Kace bakine daga Kaduna"

Megadi yafito yace" ance Kushiga".

Sukayi mashi godiya sukaje suka taho da motocinsu megadi yabudemasu Gyat suka shiga bayan sunshiga sukayi sallama Aka Amsamasu tare da basu izinin shigowa...

Suna shiga Matar da take zaune A palon tayi zubur tamike tace"lami Dakarfin gaske kece nikegani koko de"?

Lami Tafashe da kuka tanamecewa nice Mami tafada Tana medukawa gaban Mamin...

Wanna daga muryar da Mami tayi shiyajawo Hankalin sauran mutanen gidan gaba daya sukayo waje....

"Suna Mami lafiya"?

Mami tayimasu nuni da su lami daketa kuka.....aisai suka zaro ido lami suduka suka hada baki gurin fada dukda shekaru da'aka Dauk bazasu kiganetaba....

Aikuwa sai iyayan mata sukasa kuka sunci kuka Kamar bagobe sai dasuka gaji Dan kansu sukayi shiru.....

*Bayan minti Shabiyar*

Kowa dake cikin gidan harma da wadanda basunan Ankirasu Kowa ya hallara...

Baba Daddy Mami Ammi Aunty Kalisat Mujahid Sadeeq ya Naseer Da kuma Aunty Habiba Duk sunhadu kowa da tashi zuri'ar

Inna lami tamatsa kusada su Baba tana kuka Tana neman gafaran abubuwan da suka aikata nabarin gida...

Baba yadagota yace bakomi lami ninayafe maki Allah yakiyaye nagaba....tamatsa Kusa da Daddy shima tananeman gafara Daddy yace"lami wallahi Kunbani Kunya Yanzu gayaman wace irin riba kukasamo da kukagudu da gagida."?

Babu Daddy babu wata riba damuka samu sai faduwa lami tafada cikin kuka....

Baba yace "Kayi hakuri Kayafemata Dan Allah ba'anfanin tuna baya...

Daddy yace bakomi Allah yayafe mana bakidaya....lami tamatsa ga iyayanta mata da yan uwanta tarokesi gafara suma suka yafemata.....

Baba yace "towai ina sumaiyya naganki kekade ko ita haryanzu Duniyar bata koyamata darasiba."?

Inna lami tasake fashewa dakuka tace"Baba tarasu tafada tana rintsa ido....Innalillahi wainna ilaihir raju'un....gabadaya dakin yadauka....

Baba yace"yanzu sumaiyya tarasu."?

Tace" eh Baba"

Daddy yace bamu labarin Abunda yafaru

Anan Inna lami takwashe Kaf tunbarunsu gida da Abubuwan da sukafaru dasu Dama tarihin Nawaf dayabata Komi tafadamasu Bata boye komiba......

Ainan mutuwar sumaiyya tadawo masu sabuwa kuka kawai suke Harda su Nawaf Da Abbu Akarasa waze rarrashi wani Daddy da Baba ne Sukayi Karfin halin Lallashinsu....

Inna lami tanuna Nawaf wanan shine *NAWAF* Dan sumaiyya da tabari wadannan kuma sune iyayanshi da Suka temakeshi tafada Tana nuna su Abbu da Ummi...........🖊�

Comment
Comment Share
8/14/20, 6:02 PM - Maman Baby: 🌹MARAICIN NAWAF🌹

STORY AND WRITING
BY
*MAMAN BABY💝AUTAR MARUBUTA*

*MARUBUCIYAR*

*MIJIN TACE*
*KATANGAR NERA*
*SAI KAMIN KISHIYA*
*DA*
👇🏻
*MARAICIN NAWAF*
______________________________________
*SHAFI NA HAMSIN DABIYAR DANA SITTIN*
______________________________________

*🌎MANAZARTA
WRITERS ASSOCIATION 📚🖊�*

*M. W. A*

```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________________

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

.......📖 Su Duka suka Dube, su Baba yace" koshakka babu gakamanan taso kazo cikin yan uwanka."

Nawaf yatashi yana me share hawaye ya isa gurin da su Baba suke.

Baba yasha fa Kanshi yace"Allah yayimaka Albarka yajikan mahaifiyarka."

Suduka suka amsa da Ameen.

Daddy yadubi su Abbu yace"Alhaji Allah yasaka maku da alheri wanan kokari da kukayi bakowane ze iyaba Allah yatemakeku, yabaku ladan wanan kokari."

Abbu yace" Ameen Aibakomi munzama daya."

Inna lami tace"Wai yanaganku anan garin Daddy bayan nasan kuna sokoto."?

Daddy yace"Ai kusan shekara biyar kenan da dawowarmi Nima natataro kasuwancina nadawo kusa da dan uwana yanzu muduka munan Katsina."

Tace"Allah sarki yau gani cikin yan uwana danayi kewarsu abaya ga zuri'a muntara Amman Wai banga ya Umarba."?

Baba yace"Allah sarki Umar shima shekara shidda kenan da rasuwanshi sakamakon wani hadarin mota da yasamu Allah yayi mashi rasuwa Amman yabar Mana yarinya daya da Allah yabashi damakuma tunbayan Auransu da matarshi ya daya Allah yabasu yanzu Haka tana gurin mahaifiyar ta Amman lokaci zuwa lokaci tanazuwarmana Hutu maman tata tayi Aure sai taroki da mubata ita kuma mijin da ta Aura yayadda, zeri k'eta Danshima betafa Haihuwaba."

Inna lami tace Allah sarki Allah yajikan ya Umar da sumaiyya gaskiya munyi rashin mutane nagari sai de muyitamasu Adduar Allah yamasu rahama dama Kullihin musulmai."

Sukace Ameen.

Yau de wanan Family suna cikin jin dadi da Annashuwa musanman ma Nawaf wai yau shine cikin Family dinshi.....

KANO
««««««««""""""""""««««««««
Humaira Humaira K'e Humaira".

"Na'am Mommy." Tafada afirgice.

"Aisha me kikeso ki zama ne? wanan tinanin naki yayi yawa, Dan Allah kisama ranki salama haba Aisha."cewar Mommy."

Aisha tace"Mommy kiyi hakuri nadena Wallahi Mommy narasa, yazanyi sai hawaye shar."

Mommy tace"subahanallahi menak'e gani haka haba Humaira Shin bazaki hakuriba kimikama Allah lamarinki nasan de berasa nasaba da wanan son da kikadorawa kanki Dan Allah kimikama Allah lamarinki kiyi ta Addua komi sai yazomaki da sauki."

Aisha tace"Mommy narasa wane irinso nikema Nawaf gashi tun ranar da akayi taron nan bansake ganinshiba gashi in ba wani mihimmin aikiba bezowa gidannan, kuma Mommy kodama yazo bazan iya fadamashiba, saboda Daraja da kima da Allah ya yi mani bazan iya tinkaranshiba da sunan inasonshi" takarasa maganar tana me zubar da hawaye.

Mommy tatausaya ma yar tata domin so bawasaba.

Cikin tausayawa tace"Kiyi hakuri kede kicigaba da Addua kamar yadda na cemaki wata rana sai labari Kinji ko."?

Humaira tace"in sha Allah zancegaba Mommy kema kitayani Adduar."

Mommy tace Ai kullin cikin yimaki nike.

Yauwa Mommy Dan Allah zuwa jibi zanje Katsina.

To zumincin yatashi kenan to Allah ya kaimu cewar Mommy.

In Abban ki ya dawo zanga ya mashi.

To Mommy nagode.

Bayan Abba ya dawo Mommy Tak'e gaya mashi yace" to Allah ya Kaimu yama Kamata muje bakidaya Dan mundade bamu ziyarce suba kinga yanzu muna lokacin Hutu kinga sai muje baki daya Koya kika Gani."?

Gaskiya Kam Hakanma yayi Allah ya kaimu.

""""""""
Yau ne su Abba da iyalan shi suka shirya Dan zuwa Katsina

KATSINA
"""""""""««««««""""""

Nawaf ne tsaye shida murja Diyar Auntya Khalisat Sai wani yauki take tana shi,shige mashi wai ita me Dan uwa Tace"wai yaya natan bayeka."?

Nawaf da hankalin shi yana ga waya yace"Ina junkie."

Wai Dan Allah Kana da budurwa kuwa.?

Nawaf yace"Miyasa kika tanbaya."?

Ah ah Bakomi yaya.

Ta bude baki zata sake magana sai ga wasu motoci kusan su biyar suka shigo.

Lokacin da motocin suka shigo shi kuma Nawaf yatashi yanacema Murja bara nadan zagaya namike 'kafa.

Bayan motocin sunyi parking mutanan ciki sukafito Murja tatashi tatafi da gudu Tana oyoyo my sister Aisha ma tataho suka rungume juna suna masu farin cikin ganin juna.

Mommy tace "Oh nibaza aminba sai sister ko."?

Murja tace"la Mommy bahaka Bane." tafada tana rungume Mommy.
Chapter 4 · 0% Book details