← Book details Kida A Ruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 19

Sashe 3

Kida A Ruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

........“Mtsowww!!”. Wani soja yaja tsaki yana kallon agogon hannunsa. Tun 12:30 suke a wajen nan, gashi har 3pm babu alamar abinda suke zaman jira ɗin zai samu. Gashi ko zaman cin abinci a nutse oga ya hana su. Salla kawai ake basu damar yi, wanda ma basayi su basu da ko minti na hutawa. A kaikaice ya ɗan wurgama Imran harara, yana ganin zai juyo ya tsume ya gyara tsaiwarsa. Oho shi Imran ɗin ma bai san yanayi ba, umarni ne dai ya bayar matsayinsa na oga kuma dole-dole abi.
      A daji suke iya daji, dan ko dabbobin jeji akace za'a samu masu haɗari a wajen baza'ai musu ba. Dajin mahaɗa ce ta ƙasashe guda uku, daga nan zaka iya shiga kowacce ƙasa cikin sauƙi. Hakan yasa akowane iyaka akwai jami'an soji da aka ajiye na kowacce ƙasa da sauran jami'ai. Sai dai kowa da yanda yake gudanar da aikin sa da kuma iyakarsa. A tasu iyakar babu soja ko ɗaya bayan su ɗin nan da aka kawo awanni uku da suka gabata, gaba ɗayansu su ashirin ne kuma har oganni su guda uku. Abin takaicin kuma wai an kawosu ne kawai dan amsar rai guda ɗaya, ran ma na mace, macen ma yarinya ƙarama ƴar 16years. Wannan wane kalar abin haushi ne, duk da su jami'ai ne masu bada kariya ga al'umma ai bai kamata ace dan rai ɗaya an lalatar da lokacinsu a wajen ba, lalatarwar kuma da suma zasu iya rasa nasu ran. Tunda basu san wane shiri mutanen nan ke da shi ba a kansu. Zata iya yiwuwa sun shirya musu wani tuggu ko kisan mummuƙe bayan sun samu cikar burinsu. “Mtsoww!!” ya sake jan tsakin dai yana kallon agogo. Gulma yake son suyi dana kusa da shi, amma ba dama oga na kallonsu. Dole ya haƙura kamar kowa shima ya dake. A haka 4pm ta cika. Masu salla har sun gabatar.
        4:23pm dai-dai kira ya shigo layin Imran. A tare Imran da Dada daya saje cikin yaran Imran ta yanda babu wanda ya gane shi ne suka kalla wayar. Sai kuma suka haɗa ido. Idanu Dadan ya lumshe masa alamar ya ɗaga, sai kuma ya gyara tsaiwa cikin basarwa ya koma kamar yanda yaran keta kai kawo. Sai dai duk abinda Imran ke saurare a cikin wayar shima yana ji, dan sun raba bluetooth ɗin ne kowa da ɗaya a kunnensa.
         “Nan da mintuna talatin da bakwai kayanmu zasu iso. Zasu wuce zamu baku ita. Idan kukace zakuyi wani yunƙuri zakuga sakamakon hakanne a kanta. Daga yanzu ka fara ƙirga lokaci, sannan ga saƙo ka faɗama oganka, YA KULA DA KANSA. Idan ya shagala a kula da wannan ƘASAR, shine zai zama ƘASAR dan a maimakon kejin prison wannan karon CIKIN KABARI zai shiga”. Ƙittt. Wayar ta yanke kafin Imran ya iya cewa komai.
      Kamar yanda Imran ya ji komai, shi ma Dada ya ji komai. Sai dai wannan ba shine lissafin sa ba a yanzu. Ta inda Nimrah kawai zata bayyana yake kallo.

        4:40pm dai-dai baƙar mota mai duhun glass ta iso wajen, sai dai nesa da su kaɗan. Sannan ta ɗayan ɓangaren ba ɓangaren da suke ba. Gaba ɗaya hankalinsu akan motar yake, sai dai tunda ta tsaya babu wanda ya fita a ciki sai da ƙurar da suka tayar ta gama kwanciya kusan mintuna uku. 4:45 aka buɗe murfin motar, jibga-jibgan garada guda biyu majiya ƙarfi suka fito cikin shigar rufe jiki gaba ɗaya dan babu abinda ake gani nasu. Ɗaya ya buɗe baya Nimrah ta fito. Kayan dake jikinta ne dai na jiya, sai dai yanzu an rufe mata baki, hakama idanunta da baƙin ƙyalle. Ƙafarata babu takalmi. Sannan an ɗaure mata hannayenta da aka maida baya. Sun lulluɓa mata towel alamar akwai abinda suka rufe a jikinta. Dan Imran har ya motsa saukar idanunsa akan towel ɗin da suka rufa mata ɗin ne ya saka shi tsayawa cak. Shi fa jam'in soja ne, daya kwashe shekaru yana aiki tun ƙuruciya. Ta ya zai gagara gane kowanne makirci koda daga nesa ne.
     Inda Dada yake ya kalla, sai ya ga shima Dada ya kallo shi. Da ido Imran ya masa magana, Dada ya mayar masa murtani alamar ya gane komai. Sake maida dubansu sukai kan Nimrah, a kuma dai-dai lokacin mutanen dake tare da ita suka yaye towel ɗin jikin nata. Bayyanar rigar bomb ta saka yaran sojojin zabura baya a firgice, shi kansa Imran da Dada sai da zukatansu suka buga duk da dama abinda sukai hasashen gani kenan.
Received at 7:46 PM
[11/02, 4:38 pm] Abue Saleh:         “Da....d...dah!”.
    Ta faɗa lips ɗin nata na rawa sosai fiye da da. Murmurshi mai nauyi ya sakar mata. Murmurshin da zata iya rantsuwar bata taɓa ganin irinsa akan fuskarsa ba. Sai kawai hawaye suka shiga silalo mata. Ta sake buɗe baki zata yi magana ya girgiza mata kansa. Tare da ciro dabino a aljihunsa ya sashi a bakinsa ya raba biyu ya cire rabin ya nufi bakinta da shi...
        “Haah”.
    Ya faɗa a hankali. Ai bama tasan ta buɗe lips ɗin nata ba a hankali ya saka mata. Sai kuma ya shafa lips ɗin nata da yatsa yana sakar mata wani murmushin. Ita dai kallonsa take kamar sakara, tama kasa tauna dabinon. Yanda ma ta shagala a kallonsa kamar wadda ta suma sai da ya fara share mata hawayen da suka gagara tsayawa sannan ta kawo nannauyan numfashi alamar dawowa hayyacinta..
       Baiyi magana ba, bai kuma daina murmurshin ba, ya dai maida hankalinsa akan wayoyin bomb ɗin cike da nazari, bayan ya kalla lokacin daya rage musu 18-minutes.........✍️
[14/02, 9:15 am] Abue Saleh: Sai ta samawa kanta lafiya akan ai yau ma rana ce. Dan haka yau ɗin ma ta matsu su taho da wurin nan.
      Har akai la'asar ƙawayen nata na nan. Sai da suka gama shaƙiyancinsu da ɗirka mata abubuwa sannan wajen 5 suka tafi. Da Ismat kawai aka barta, dan su Amimah basu biyosu ba. Itama Ismat ɗin Momy bata san ta biyosu ba, so take kuma daga nan ta gudu gidan Abbansu kawai.
          Ismat ɗin ta tura yau ma gano mata ko yana nan, idan ma baya nan taje wai dan su Mammah su san ta dawo, ai tasan Mammah ɗin zata saka shi zuwa inda take ko bai niyya ba. Sai dai me, Ismat na zuwa ta dawo mata da labari mara daɗi. Cewar shi baima kwana a gidan ba. Su Mammah kuma duk suna asibiti Ruƙayya babu lafiya. Ga kuma Lailah ma ta faɗi an shiga da ita cs har yanzu ba'a fito da ita ba.
        Maimakon hankalin Nabeeha ya tashi tace suje asibitin sai tayi shiru. Sai ita Ismat ɗin ce ta ce, “Aunty kodai asibitin zamuje muma. Dan na fahimci abin fa babbane, hankalin masu aikin nasu duk a tashe yake wlhy”.
         “K rabani da wani asibiti Ismat babu inda zanje gaskiya. A gama zuba min wannan uban ƙamshin a jiki da gyara ni na kuma ƙare a asibiti. Ƙamshi nake son D. ya ji ba warin magunguna ba”.
      “Amma Aunty.....”
   “Kefa matsalata dake kenan. To ALLAH zan kora ki gida yanzu. Haba ki fahimceni mana. Ke bama ƙya ganin idan nace zan fita daga kawoni akwai ganganci a ciki. Karfa ki manta yanda D. Ya tsani yawo”.
        “Hummmm”.
    Ismat ta faɗa kawai. A ranta ko faɗi take (Baki san ya tsani yawon ba sai yanzu. Bayan tunda yabar gidan kema baki zauna ba Aunty. Kina tunanin kuma baza'a sanar masa ba. Ke matsalar ki baƙya son gaskiya da ɗaukar shawara. Kin bar Momy ta tasirantar da ƙiyayyar dangin mijinki kuma ƴan uwanmu ma ta wani fannin a zuciyarki. ALLAH yasa ki gane, dan inba haka ba wannan karon ma zaman nan naki bamai ɗorewa bane. Dan yanzu mutanen gidan nan bana da bane da suke miki kawaici, sun ɗanɗana zama da wasu surukan sun ji daɗi)...

   <<••>><•••••><<••>>

      “Dada zan MUTU ko? Zan mutu bazan sake ganin Mammah da Ruky ba, bazan sake ganin su Uncle's Ja'afar ba da su Mu'azz”.
         Dada da hankalinsa gaba ɗaya ke kan aikinsa ya saki murmurshi kaɗan. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da faɗin, “Bayan kin shiga labor room sau goma sha biyu, kin haifo magadan SOJA, jikokin Abdul-rasheed Shehu Kobi ko Kiddo?”.
      Ita sam bata wani fahimcesa ba. Shima kuma yanda yay maganar a basarwarsa yana kuma aikinsa bama zakace shi ya faɗa ɗin ba. Ya sake kallon mintinan da suka rage. 9 kawai. Dai-dai nan Imran dake nufosu ya taka wani abu. Cak ya tsaya yana kallon ƙafarsa. Dan haka Faro dake kallonsa shima ya ce, “Yaya dai?”.
     Ƙafarsa ya nuna masa sannan yay masa alamar bomb. Sai kuma yay masa nunin yay shiru kada Dada yaji. Ya ilahi wata muguwar bugawa zuciyar Faro tayi, a take jikinsa ya kama rawa. Ya kalla Imran ya kalla su Dada. Ya rasa ma ina zai kama. Suma sauran sojojin hankalinsu ya tashi matuƙa. A take suka fara zagaye wajen da na'urorin bincike bomb. Dan tunda ogansu ya taka hakan na nufin akwai wasu a wajen. Ai ko sai gasu cikin ikon ALLAH kusan bakwai a cikin ƙasa irin wanda Imran ɗin ya taka. Tuni masu ilimin akansa suka fara aikinsu. Sauran jami'an suka ja baya sosai. Sai dai Faro ya kasa yin hakan. Ya kafa ma su Dabo idanunsa kawai da sukayi jazur na tashin hankali...

         “Dada ƙara min Dabino”.
    Nimrah ta faɗa idanunta a rufe dan ta sadaƙar kawai lokaci yayi. Shi kansa uban gayyar hankalinsa ya gama kaiwa ƙarshen tashi. Dan saura minti huɗu ya rage musu. Gashi ya katse waya har biyu basu bane, saima ƙara na ƙidaya lokaci da suka saka bomb ɗin ya fara. Dabinon ya ciro ya saka mata a baki, batare daya bar abinda yake ba.
       A dai-dai wannan lokacin kuma Faro ne ɗauke da wani ƙaton dutsi yana tafiya a hankali a hankali ta bayan Imran dake tsaye cak a wajen nan har yanzu idanunsa a rufe. Babu abinda yake maimaitawa sai kalmar shahada a zuciyarsa. Dan ya riga ya sadaukar ya kuma sadaƙar yau babu makawa ranar amsa kiran UBANGIJI ce. Babban fatansa Nimrah da Haysam su tsira a idanunsa kafin lokaci ya cika.....
Received at 10:47 AM
[14/02, 9:15 am] Abue Saleh: 6
Chapter 3 · 0% Book details