← Book details Kida A Ruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 19

Sashe 1

Kida A Ruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

[10/02, 9:34 am] Abue Saleh: BOOK 3

2

........Yanda duk suka zuba masa idanu zai tabbatar maka da ƙagararsu na son jin yace wani abu. Shima ya fahimci zalamar tasu, dan haka kai tsaye ya furta, “Imran bama Dabo yay tracking number ɗin nan?”.
      Cikin bin umarni ya amsa da. “Okay”.
     Babu ɓata lokaci Dabo ya fidda laptop ɗinsa a jakarta, dan da abinsa yazo. Faro ya miƙa masa wayar. Karo na farko Dada ya miƙe yana kai-kawo a falon hannayensa duk goye a bayansa. Jikin window ya ƙarasa ya tsaya. Yanda ya zubama compound ɗin gidan idanu ya saka Yusuf miƙewa shima ya nufi inda yake hango coffee maker. Sai da ya duba duk coffee powder ɗin dake wajen sannan ya haɗa wanda yasan boss na sha a da, duk da bai sani ba ko ya canja a yanzu. Amma dai ya haɗa ya jira har coffee maker ɗin ta gama matso masa shi sannan ya ɗauka. Koda ya miƙa masa cike da girmamawa sai Dada ya murmusa. A hankali ya furta, “You’re the best”.
      Yusuf yay murmushi shima har haƙoransa na bayyana. Cikin ƙara sirinar da kai ya ce, “Yace thanks you Boss”. Daga haka yabar wajen, shi kuma ya fara shan coffee ɗin yana maida hankalinsa ga wajen dai hannunsa ɗaya a aljihu.

        “An sauke layin akan waya gaba ɗaya fa. Sannan an goge duk wani information a kansa, tare da hanashi aiki na har abada.”
       Gaba ɗaya fuskokinsu ya canja daga sauraren Dabo mai maganar. Amma shi Dada a mamakinsu murmurshi ma yake yi. Dan a hankali ya tako ya dawo inda suke, ya zauna a inda ya tashi yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. Kamar bazai ce komai ba tsahon minti guda yana ta shan coffee ɗinsa. Ganin yanda a yanzu ma suka zuba masa idanun ya sashi sake murmusawa, sannan ya furta, “Wannan ba aikin jahilai bane. Idan lissafi na yayi dai-dai sun ɗauke ta ne dan karkata hankalinmu a kanta kawai su sami yin abinda suke so, Imran, Faro ku janye sojojin ku na ƙofar da sukace su sakar min matata”.
       Imran ya zaro idanu saboda kalmar (Matata) ɗin yana gimtse dariya, hakama Faro. Su Dabo kam sun girgiza ne kawai ta ɓangaren aiki duk da sun san Nimrah tun tana ficiciyarta, sai dai batun aure basu san da shi ba, ba kuma su fahimci furucin boss ɗin nasu ba a yanzu. Cikin kasa haƙuri Imran ya ce, “Lissafin ka dai-dai ne. Amma yanke wannan hukuncin duka akwai ruɗani.”
      Caraf Faro ya karɓe da, “Tabbas akwai ruɗani Imran, dan kuwa hakan na nufin zasu aikata abinda suka shirya a wannan yankin, sannan ba lallai idan sun sami biyan buƙata su saketa ba, ko kuma su cutar da ita kafin su saketa. Mutanen nan fa sun wuce duk yanda muke zato da tsammani Boss, ni nafi gane kawai mu farmake su, mu amso ta wlhy”.
        Dada da kamar baima jin abinda suke faɗa ya wani lumshe idanunsa ya sake buɗewa. Sai kuma ya taɓe baki kaɗan. Hankalinsa kwance ya furta, “Daga lokacin da lissafi ya zama RUƊANI ko mabiyan addini kan kasance a rikice ne. Dan zasu gagara gane waya kamata su bautamawa? Sai dai abu ɗaya tak da zasu nutsu da shi, mafitar mai sauƙi ce. Bayan ANNABIN ƙarshe UBANGIJI bai sake turo wani MANZO ba, kenan duk wanda zai faɗa maka wanene UBANGIJINKA zai koyar dakai bin ALLAH ne da koyarwar MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMAD (S.A.W). UBANGIJI ya halicci abubuwa guda biyu dake bama duniya hasken da har idanun mu ke banbance wanne muke ciki. Hasken RANA, dA hasken FARIN WATA. RANA duhun hadari, ko shigowar dare, ko shigowar hazo na sanyi ne kawai ke iya risinar da ita a garemu, amma hakan baya hana muga hasken DUNIYA. FARIN WATA, canjawar farkon wata zuwa tsakiya da ƙarshe ke canja mana ganin cikakken kaifin haskensa, sai kaga a ƴan awannin nan daya rissina dole muke amfani da fitilu. Shin hakan na nufin mun makanta ne? ko wannan hasken shine dama sandar jagorar idanun mu bisa hukuncin mai hukuntawa?”.
         Imran ya ɗan furzar da iska yana mai sakin murmushi. Dan shi ya fahimci komai, saboda yasan Zak-Shadow sanin da ko alfahari yayi da duk duniya babu wanda yay masa irin wannan sanin dole a yarda. Faro dai ba komai ya samu warwara a kansa ba. Amma da yake shima ALLAH ya bashi kaifin basira na tunani, sannan ya yarda da Dada yarda ta haƙiƙa sai ya jinjina kai kawai.
[10/02, 9:35 am] Abue Saleh: Dabo, Yusuf dama masu koyi ne daga ƙyawawan hali irin na boss ɗin su. Sannan masu biyayya ne akan ayyukansa musu ƙyau dan sunyi imanin in sha ALLAHU bazai taɓa karkatar da su zuwa mummunar hanyar bijirema UBANGIJI ba.
     Shima dai gogan bai sake cewa komai ba. Dan daga haka ma ya miƙe abinsa ya nufi ɗakin nan na sirri ya barsu a falon suna cigaba da tattaunawa. Saboda yanzu dai aiki ya rage garesu.....

      <••••><•••><•••><••••>

     A gidan Mammah cikin tashin hankalin Ruƙayya suke bayan wanda suke ciki. Dan ta rikice musu ga jikinta ya ɗauki mugun zazzaɓi sai amai take. An kira doctor ya dubata ya tabbatar musu damuwa ce sannan gudun zuciyarta ya canja sosai. Dole ya buƙaci su wuce da ita asibiti. Hakan dole akayi, Ammar ya ɗauketa gaba ɗaya zuwa mota. Yaya Bilal yaja. Ma'aruff da Ja'afar da Mammah suna wata motar. Dan tace bazata iya zama a gidan ba. Suna isa aka fara bata taimakon gaggawa.. Abinda ya sake tada hankalinsu har bayan awanni biyu allurar da sukai mata ta barci taƙi ɗaukar jikinta. Kuma babu abinda sukafi buƙata tayi irin barcin a yanzu. Sunan Ninah kawai take kira. Da ƙyar, da addu'oin da Mammah keta faman tofa mata aka samu nasarar barcin ya ɗauketa. A lokacin kusan 2:30 na dare.
        Su Ja'afar sun gagara barin asibitin. Dan cikin ikon ALLAH ma a kusan lokacin sai ga kiran Dada ya shigo wayar Bilal. Ya kira ne dan son jin yaya Mammah ta kwanta dai ko? Sai kuma ya ji akasin lissafi. Yay ɗan jimm na sakanni, kafin ya furta.
        “Wane asibiti ne?”.
    Sunan asibitin Bilal ya sanar masa. Dada bai ce komai ba ya yanke wayar. Fitowa yay daga ɗakin sirrin daya shiga. Su Imran dake ta faman aiki duk suka ɗago suna kallonsa.
         “Faro cikin jami'an daka haɗa ɓangaren masu farin kaya mutum goma suje kk hospital ka tura musu number ɗin su Ma'aruff”.
     “Wani abu ne ya faru?”.
  Cewar Imran yana tsaresa da idanu. A taƙaice ya ce, “Ruƙayya ce ba lafiya”. Daga haka ya sake juyawa ya koma.
      Imran ma aikinsa ya cigaba da yi, sai Faro ne daya ɗauka waya ya fara ƙoƙarin neman ɗaya daga cikin jam'an sirri daya haɗa batare da kowa yasan ɗan uwansa ba.....

★)))((((★))))(((★
Chapter 1 · 0% Book details