← Book details Kida A Ruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 19

Sashe 10

Kida A Ruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ɓangaren shugaban ƙasa Yusuf Shu'aibu Tafida ƴan jam'iyya sun bala'in saka rayuwarsa gaba ta ƙarƙashin ƙasa akan naɗin muƙamai. Dan tun suna ƴar percentage har sun fito masa ƙuru-ƙuru da sunayen waɗan da suke buƙatar a bana manyan muƙamai. Hankalinsa ya tashi, duk da kuwa wanda suka kawo ɗin shi bazai ce suna da wani baƙin hali na zahiri bane. Amma a muƙaman da suka riƙe a baya a bayyane take su masu rauni ne ga sauke haƙƙokin talakawa. Babu abinda suke yi sai raya kansu da iyalansu da dukiyar ƙasar. Shiyyasa babu wani ayyukan cigaba na zahiri da suka fito daga yankunan su a sanda suke mulki na shugabanci ko na wani office da suka riƙe.
Received at 12:22 PMReactions: Rasa wazai tunkara yay shawara yayi. Gashi kwanaki uku kacal suka bashi. Yau hatta office yaƙi fita da wuri har kusan sha ɗaya. Wani gefe na zuciyarsa keta kawo masa Zak-Shadow da Imran. Kuma tabbas yana jin gamsuwa da yaran. Dan wannan rikitaccen mulkin baya yiwuwa sai da ɓoyayyun mashawarta. Wlhy badan fidda Haysam da yayi ba da yace shi wannan mulki baiga amfaninsa ba, dan rikicin cikinsa da kitumurmura sun wuce tunanin mai tunani. Wanda ke waje shike kallon shugaban ƙasa a mai zartarwa sama da kowa. Amma a zahiri hotone kawai a kujerar mulki shugabancin ƙasar nan. Ainihin masu mulkar ƙasar suna gefe ne kawai suna busa sigari kalar wadda suke buƙata. Sai abinda suke so, sai abinda sukace dole za'ayi, idan kace zaka bijire su ƙasƙantar da kai a idon talakawan ƙasar a bayyane, a ɓoye su raunana lafiyarka da kuzarinka. Duk mai baka goyen baya su siyesa da kuɗi, idan yaƙi bi shima su ɓatar da shi ko su tsigesa a kusa da kai ɗin. Wannan itace zahirin ƙasar da talaka bai sani ba, wata shari'ar dai sai anje can kawai.
Wayarsa ya ɗauka da mutane masu muhimmanci ne kawai a ciki yay gajeren text ya tura. Daga haka ya miƙe domin shirin fita office.....

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Saƙon shugaban ƙasa ya shigo wayar Dada ne a dai-dai lokacin da motar su ke hawa kan babban titi bayan fitowarsu a cikin asibiti. Dabo ne ke driving ɗin, gefensa Imran. A baya Nimrah sai Dada dake ta aiki da laptop a kusa da ita. Tana lafe ne jikin ƙofa idanunta a lumshe, ji take kamar tai tsuntsuwa ta ganta a gida saboda ɗoki. Duk da dai akwai ajiyayyar damuwa dake danƙare da zuciyarta da brain ɗinta. Amma kamar yanda tai alƙawari zata bi komai a sannu kamar yanda ta fara. Dan a yau ta sake fahimtar gane ainahin Dada ba abune mai sauƙi ba. Dole ta dake, dole ta shirya, dole ta jajirce, dole ta ƙara wayo da taka tsantsan. Sai dai duk da haka maganar auren nan na ɗaga mata hankali. Tana son taji tabbaci a bakin Mammah da sauran Uncles ɗinta da Daddy Imran. Harga ALLAH indai da auren nan batama san yanda zata fassara shiga ukun da take ciki ba. Waye wannan miji? Tana son ta sanshi, ta ƙagara ta sanshi.
Duk halin da take ciki Dada na lure da ita. Dan yanda take yamutsa fuska, ta cije lips, ta matse idanu yasa shi fahimtar akwai abinda take tattaunawa da zuciyarta. Kuma ko minene yana da girma da rikitarwa a gareta. A lokacin da yake ajiye wayarsa dake tsakkiyarsu bayan kammala karanta saƙon Mr President sai yaga tasa hijjab ta share hawaye. Hakan ya sake tabbatar masa da zarginsa. Baiyi magana ba ya cigaba da aikinsa yana sauraren tattaunawar Imran da Dabo akan Ojo da suke ƙoƙarin gano inda yake yanzun...
Gidan Daddy Imran suka fara zuwa domin sauke shi. Nimrah nason shiga taga Ammie tana kuma zumuɗin zuwa taga Mammah. Sai kawai ta saka a ranta tunda weekend za'a shiga zasu zo ita da Ruky. Isowar su gate ɗin nasu gidan sai taji ƙaguwar a buɗe, dan badan Dada bane a motar da tuni ta ɓalle murfin ta shiga da gudu. Amma jikinta sai tsuma yake ta yanda har shi ma ya gane. Aiko Dabo na tsayar da motar ta buɗe ta fice dan haƙurinta yakai maƙura. Dada ya bita da kallo kawai, dan kamar ƙyatawar ido har taje ƙofar falo.
Kansa ya ɗan girgiza yana miƙama Dabo daya buɗe inda yake laptop ɗin daya rufe. Daga haka ya sakko ƙafafunsa ya fito gaba ɗaya. Sauran kayan Dabo ya tattauro, dai-dai kuma isowar maigadi da malam Buba dake noƙewa a baya wajen. Cikin girmamawa suka fara gaida Dadan. Dada ya janye idanunsa daga kallon da yay ma malam Buba na seconds, kafin ya amsa gaisuwar tasu. Suka ɗora da nuna farin cikin dawowar Nimrah, sunata ambaton godiyar ALLAH. Shi dai wajen yay ƙoƙarin bari. Amma sai maigadi ya miƙo masa abinda ke hannunsa yana faɗin, “Af naso na manta. Ranka ya daɗe dama ga saƙo yanzun nan babu jimawa wani ya kawo shi a baka. Dan zanje nakai ciki ne ma kuka iso na dakata buɗe muku ƙofa.”
Received at 12:22 PM
reacted with ❤ Idanu Dada ya ɗan zubama hannun maigadi, sai kuma ya miƙa hannu ya amsa batare da yace komai ba. Yana barin wajen Malam Buba ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi da har sai da maigadi ya kallesa. Kamar zai yi magana sai kuma yay shiru suka koma bakin gate. Sanda da ya shige ɗaki wufff tun buɗe gate da akai ya fito shima sum-sum yana leƙa hanyar sashen Mammah da har Dada ya shige....

Yanda Dada ya samu falon ya kacame da murnar ganin Nimrah sai yama tsaya kawai yana kallonsu. Dan Ruƙayya na rungume da ita tana kuka ana lallashinsu. Su duka biyun suna jikin Mammah. Mu'azz ma sai sharar hawaye akeyi na farin ciki. Shigowarsa tasa su Bilal dake zagaye da su maido hankalinsu kansa. Sai kuma duk suka zaburo cike da farin cikin ganinsa suma. Mammah kanta yau ta kasa dannewa kallonsa take farin cikinta a bayyane. Gwaggo Alawiyya tazo ta kama hannunsa tana faɗin, “Sannu kaji Haysam, ALLAH yay maka albarka. Maza zo ka zauna ansha fama kwana biyu”.
Murmushi kawai yayi yana kaiwa zaune. Ya gaida Mammah sannan su Gwaggo Khadijah. Suma su Ja'afar suka gaisheshi. Kafin wani lokaci Aunty Mimi ta kawo masa ruwa. Dan suma duk suna gidan daga asibiti suke duba Lailah. Mammah tasan duk yanda suke son jin yanda aka samo Nimrah bazai faɗa ba, dan haka ta tambayesa a shirya masa abinci ne. Miƙewa yay yana amsa mata da zai yi wanka tukunna. Ya ɗan kalli Nimrah da Ruƙayya ke bama abinci a baki itama yana bata ya wuce abinsa. Dai-dai Ammar na sakkowa daga kai kayansa ɗaki da Dabo ya kawo. Umarnin kawo masa coffee ya bashi yana wucewa...........✍️
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889

Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

[16/02, 10:58 pm] null: KIƊA A RUWA 3

12

.........“Aunty wlhy Dada ya dawo”.
Zimbur Nabeeha ta tashi daga barcin da take yi tana kallon Rayhana mai maganar. Dan yanzu babu jimawa suka zo gidan ita da Amima. Iske Nabeeha na barci yasa sukai zamansu a falo suna kallo bayan sun saka mai aiki da suka zo da ita yanzun nan shiga kitchen ta musu abinci batare da ko matar gidan sun bari ta san da zuwanta ba. Momy ce tace su kawota kasancewar Nabeehar tayi mata complain a jiya game da aikin gidan. Tasan ragwantar Nabeeha sarai, ita kuma a wannan lokacin bata son a samu matsala kodan First Lady shiyyasa tai gaggawar samar mata da mai aikin, ko muce First Lady ta samar.
“Aunty badai can ɓangaren zakije ba?”.
“To mi kike so nayi Rayhana. Kin san dai mugayen can bazasu faɗa masa na dawo ba. Gara naje da kaina ya ganni.”
“Hu'umm da dai kin bari ya kawo kansa wlhy. Amma kije ai babu aji, bayan kin san shegiyar yarinyar nan tare suka dawo. Ƙilama babu wani saceta da akayi shiyya ɗauketa yaje yasha shagalins.....”
Kallon da Nabeeha ke mata ya hanata ƙarasa faɗa, sai kuma tace, “ALLAH ya baki haƙuri. Amma magana ta gaskiya yanzu fa ba da bace Aunty. Dole ne ki gyara wasu abubuwan musamman zumuɗin nan akansa.” tana gama faɗa ta fice a ɗakin. A ranta kuwa tana saƙa abinda ya daɗe a zuciyarta ne. Dan wannan karon tayi alwashin zatayi yaƙi domin kanta. Bazata iya haƙuri da ciwon dake ranta ba. Sai dai ayi ɗayan biyu. Kota samu, ko kuma kowa ya rasa...
Nabeeha kuwa ƙwafa tayi kawai. Ta nufi bathroom. Babu jimawa ta fito fuskarta jiƙe da ruwa alamar wankota tayi. Gaban mirror taje ta fara gyara fuskar da kayan kwalliya, sannan ta cire kayanta ta canja da wani arnen lass da yay masifar ƙyau ta saka turare sosai a jikinta. Koda ta fito daga Amima har Rayhana da kallo suka bita. Amima data saki baki na mamaki ta ce, “Aunty ina zuwa haka da rana tsaka?”.
“Sashen Mammah”.
Ta bata amsa a taƙaice tana ficewa abinta. Kallon juna sukai ita da Rayhana, Rayhana ta taɓe baki da faɗin, “Kin san bata da wayo sam.”
“To ALLAH ya ƙyauta wannan ai zubar da mutunci ne”. Cewar Amima...

()<>()<>()<>()<>()
Chapter 10 · 0% Book details