← Book details Kida A Ruwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 19

Sashe 2

Kida A Ruwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

         “What!”.
    Ya faɗa cikin ƙaraji da mamaki yana miƙewa tsaye kamar wanda kunama ta halba a uwawu. Suma sauran duk kallonsa sukayi a razane, kowa na neman ƙarin bayani. Mr Specter ya kalla Oga Jush lips na rawa ya furta, “Wai kasan sun saki hanyar kuwa Oga!”.
      Gaba ɗaya meeting room ɗin babu wanda bai nuna razana ba maimakon murna da farin ciki. Black Spider ya ce, “Kai ina akwai matsala. Zak-Shadow ba mahaukaci bane ba fa?.”
       “Tabbas ba mahaukaci bane, dan gadararsa ma bazata bari yayi abinda muke so ba cikin awannin goma kacal.” Viper ya faɗa shima cikin tabbatarwa.
      Scythe ya ce, “To mi hakan ke nufi?”.
     Babu mai wannan amsar, dan haka duk suka zubama Oga Jush da baice komai ba idanu. Sai dai bashi da alamar zai ce ɗin tsahon mintuna uku. Sai da ya gama zuƙe sigarinsa tas kafin.
        “Ba mahaukaci bane, sannan ba TSORO yaji ba. Amma dole yay hakan bisa dalilai biyu. Na farko Imran, shine zai tirsasashi dan yarinyar ta dawo, sannan zartarwa da gidan soja a hannun Imran kawai take yanzu tunda shi bai koma aiki ba. Na biyu yana SONTA. Hakan ya nuna a randa ya je station kan case ɗinsu na makaranta...” yaja iska yana ƙoƙarin kunna sabuwar sigari. Dan gaka Iron Fang ya samu damar faɗin, “Amma Oga baka ganin zai yi hakan da wani abu a ƙasa?”.
        Baki Oga Jush ya taɓe. “Wannan tunanin naka nakan hanya, dan yana aiki da WAYO fiye da Ƙwaƙwalwa. Amma kar wannan ya dame ka. Ayi mata allurar da zata karya halin da take ciki. A daren nan a kaita inda next plan ɗinmu yake. A ɗorata kan komai cikin awannin da suka rage. Dan hannun karɓa, hannun bayarwa za'ai, kuma a cikin mintunan ƙarshe biyar kacal”.
       “What! Oga yanzu nan sakar masa yarinyar nan zamuyi?”.
[10/02, 9:35 am] Abue Saleh:      “Muma yin hakan dole ne a garemu. Dan munfi buƙatarta a wajensa fiye da a wajenmu a yanzu. Sannan tana da muhimmanci fiye da komai a garemu a yanzu. Ku ɗauka mune GANGAR JIKI, ita kuma ITACE NUMFASHI. Mi kuke tunani idan da ɗaya babu ɗaya?”.
      Tabbas wannan maganar ta Oga ta masifar girgiza su. Dan yanzu sun fahimci girman yarinyar ya wuce ƙaramin tunaninsu a wannan tafiyar. Kuma sai da ita sannan zasu cimma nasarar da suke buƙata. Ashe ba ƙarya bane da akace da yawan yaƙe-yaƙen waɗan nan ƙarnukan suna fara ne ta sanadiyyar MATA. Ga kuwa zahiri suna gani a yau ɗinsu. To bara suga yaya za'a kwashe wannan wasan. SU-NE ko SHI-NE..
      Cikin sauke numfashi mai nauyi Viper ya furta, “Tabbas oga mun fahimce ka. Sannan mun gamsu da wannan shirin. Musamman idan mukai dubi da She is a very clever girl. Dan ni ban taɓa ganin mace data bani mamaki ba irinta, idan har a wannan ƙarancin shekarun nata tana a haka ya kake gani nan da wasu 5-years masu zuwa kuma?....”
         “A gaskiyar ka Viper, yarinyar KADARA ce mai daraja. Kuma ya kamata ubanta ya ci wannan baiwar tata yanda ya kamata Oga. Lokaci yayi da ƙungiya zata ƙara duba ma Mole ko kuwa ƴan uwa?”.
      Yanda ya ƙare maganar da kallonsu su duka. Kai tsaye suka nuna amincewa. Dan girman kai irin na Mr Specter kaga ya yaba wani lallai ko waye ya ciri tuta............✍️
[11/02, 4:36 pm] Abue Saleh:        “Kiyi addu'a, in sha ALLAHU nan da wasu awanni zaki ganta. A yanzu haka muna kan aiki tuƙuru, hasali ma mun san inda take amsota kawai ya rage....”
         “Dada da gaske?”.
     Ta faɗa cikin washe baki.
Murmurshin gefen baki ya mata yana mai lumshe idanunsa da buɗewa alamar tabbatarwa. Ba Ruƙayya kaɗai ba har Mammah da Ammar zancen sa ya musu daɗi. Dan sai da Mmamah ta kauda kai gefe tana ɗauke ƙwallar da suka taru mata a ido, Ammar kuwa ya ɗauki waya ya turama sauran ƴan uwan bayani ta cikin group ɗin su na WhatsApp. Sarai Dada na lure da su su duka har Ammar ɗin. Sai dai baice komai ba. Tea mammah ta haɗa ta bashi. Zai yi magana ta hararesa, murmurshi yayi dole ya amsa. Da zata zuba dankali ne ya lallaɓata yace tea ɗin ya ishesa. Da ƙyar ta yarda. Bai ma wuce sha biyar ba kiran Imran ya shigo masa. Dole ya ajiye yana miƙewa.
       “Mammah inaga zan barku, su Imran sun kammala shirinsu. Dole kuma zan rigasu wucewa. Ai mana addu'a”.
      Ko bai fito fili ya faɗi inda zasu je ɗin ba Mammah ta fahimta. Dan haka ta fara jera addu'oi masu nauyi sosai a garesu dama al'umma baki ɗaya. Daga haka ya shafa kan Ruƙayya batare da yace komai ba ya fice Ammar biye da shi. Har mota ya rako shi. Sai da ya shiga har ya mata key sannan Ammar ya matsa ya bashi hanya. Dada akwai nutsuwa, sannan komai nashi zaka sameshi a nutse yake. Sai dai akan aiki baya ƙaunar ƙalula ko wasa, in za'ayi kawai ayi, in baza'ai ba a bari, amma maganar wasa anan ɓangaren ba'ayinsa da shi. Yana da zafin nama irin na jaruman maza...

      ===============

           Kamar yanda suka buƙata an janye sojojin ƙofar yamma tun a daren jiya ƙarfe goma sha ɗaya. Sai dai a maimakon bada Nimrah ko wucewa da abinda suke sonyi wani waje suka kai Nimrah ɗin. Sun kuma nuna mata duk abinda suke son ta sani ta kuma gamsu da su akan zuri'arta. Da farko rashin kunya ta fara zubama su Jagwa dake tare da ita bayan farkowarta, haka ma koda aka kaita gaban wanda sukafi su Jagwa ɗin bata risina ba sai da suka buɗe mata abinda yay matuƙar gigizata. Tabbas tayi shaidar gani da ido, ta kuma shaidar ji da kunne na zahiri. Tayi kuka har hawaye sun daina fita mata. Daga ƙarshe tayi alwashin ɗaukar fansa akan Dada ta hanyar tabbatar masa da DAN HAKKIN DAKA RAINA SHI KE TSOLE MAKA IDO. Dan haka ta ɗauki alwashin zamewa Haysam Abdul-rasheed Shehu Shehu Kobi KIƊA A RUWA. MAI TADA HANKALIN DODO. Idan shi yace ya ƙware a iya FUSKA BIYU zata tabbatar masa da ita kuma RAINON SA ce. Zatai kwanciyar RUWA a gabansa, domin samawa kanta HANYAR wucewa harta ƙofofin gashin jikinsa.....

      ★★★★

          Ƙarfe 12:pm su Imran suka samu saƙon inda zasu amshi Nimrah. Ba kuma a ko'ina bane sai ta inda suka janye sojojinsu. Dan su Oga Jush sunyi alƙawarin a gaban idanun su Imran zasu wuce da kayansu dan su nuna musu MANYAN ƘWARI ne da sukafi ƙarfin kowa. Dan haka suka shirya sosai kuma akan Nimrah da shirin da ita kanta bata sani ba.
       Koda Imran ya turama Dada saƙon ya jima yana maimaita shi shiru cikin nazari, dan ya tabbatar zasu iya wasa da hankalinsu. Idan kuma sukai irin wannan tunanin zasu iya aikata yanda suka ce. Ya kamata ace duka kada suyi sakaci, musamman ma shi, dan wannan shine zaren da zai kama na fara shinfiɗa aikinsa akan su.
      Bayan ya gama ƙullawa da kwancewa ya turama Imran saƙo shima. Daga haka ya tashi ya fara shirin cikin uniform ɗin soji domin yin ɓadda kama. Dan shi a yanzu ba jami'in sojoji bane a zahiri. Shi Special Presidential Intelligence & Covert Operations Commander ne a yanzu, amma a wannan gaɓar dole yay ɓadda kama cikin sojojin dan samun abinda yake buƙata. Duk da ya san Imran da Faro zasu iya yin duk abinda zai iya yi in sha ALLAHU..
        Kodan ya jima bai saka kanyan ba, ko kuwa dan ya ƙara canjawa da cikar kamalar shekaru ne da nutsuwa. Kayan sun masa ƙyau fiye da shekarun baya ma da yake sakasu da ƙuruciya. Buɗaɗen jikinsa, zuwa shafaffen cikinsa sun zauna fyaram a cikin kayan. Kai da kaga wannan ZAKIN a cikin waɗan nan kayan manyan kasan kasan ba zakin ajiyewa a gidan zoo bane domin kallon yara.
Received at 7:46 PM
[11/02, 4:37 pm] Abue Saleh: Zaki ne na farauta da in ba'a ma saka masa linzami ko takunkumi ba ɓarnar da zai yi sai ya zama abar rubutawa a tarihin da za'a kafe a bangon gidan gwamnatin ƙasa dan ya zama barazana ga BABBA DA JAKA. Bayan ya saka Handkachiff kamar facemask ya saka baƙin eyeglass daya ɓoye idanunsa da ainahinsa gaba ɗaya. Sai da ya tabbatar kayan aikin da duk zai iya buƙata na cikin jikinsa sannan ya fito compound ɗin gidan. Dan yana a UNIT ZERO ne shi kaɗai. Parking space ya nufa kai tsaye cikin takun sa na masu ƙarfin jini da babu wasa a ciki ko wani rangwaɗar shashanci, dan wannan mazan a mazansu suke kai tsaye. Hannu ya kai kan blue tempol da aka rufe wani abu ya yaye shi, sai ga wani gingimemen ƙaton mashin baƙi wulik mai shegen ƙyau da tsari ya bayyana. Da allama madadin tsohon mashin ɗinsa ne ya dawo a sabon salo, sabon zamani. Hularsa dake ajiye samansa ya ɗauka ya saka, kafin ya haye yana karanta addu'a yay masa key. Koda yazo gate remote ya danna ya buɗe da kansa, yana gama ficewa ya maida ya rufe kansa. Shi kuma ya ɗauki hanya..........✍️

Mun tafi amso Ninah. Wanda ya shirya muje zuwa🤕🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️😎.
Received at 7:46 PM
[11/02, 4:37 pm] Abue Saleh: 4
Chapter 2 · 0% Book details