Sashe 7
Kadangarun Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Waleed ne sanye da Kayan likitoci fitowar sa daga teater kenan ya fito waje, direct inda motar shi ta ke ya nufa.Shiga yayi ya mata key ya nufi Pays-Bas dubo Mai gadi wanda dama duk bayan kwana biyu ya ke zuwa ya yi mashi allurai,shigar sa quartier ke da wuya Nabeela ta fito ƙofar gida sanye da kayan makaranta.
Tun daga nesa ya ƙarewa baƙar fuskarta kallo wacce talauci yasa ta ƙara rinewa,ta na ganin motar shi ta ɗan noƙe jikin ƙofa,fitowa yayi idonsa kanta da sauri ta baza da gudu.
Waleed ya ja ƙyaci a zuci yace "au kenan da gangan ta zuban ruwan tunda har ta shaida ni ?"yayi ƙyaci kafin ya shiga gidan mai gadi wanda ya ke na laka.
Da murna matar shi ta tarbi Waleed ta aza masa kujera tare da gaishe shi duk da yadda ya ke haɗe fuska ya na kuma nuna ƙyanƙyamin su.
Ciki-ciki yace "ya ƙarfin jikin?" Wani siririn tsoho ne ya amsa "da sauƙi likita ya mutan gidan?"Waleed bai amsa ba sai akwatin aikinsa da ya buɗe ya fara fiddo allurai,nan ya yi mashi kafin ya miƙa masa kuɗi yace "ga albashin ka nan na wannan watan,ranar nan mantawa nayi ban baka ba "
Godiya mai gadi ya shiga yi saboda wannan zamanin ba dukan jama'a ne ba ke iya biyan mutum albashi alhalin ya na gida ya na jinya ba tare da yayi aikin ba.
Waleed na fitowa ya tsaya cak sakamakon hangota da yayi ta na yi masa rubutu jikin mota,a zuciye ya yo kanta.....
Please share
[05/05 à 11:20] MRS SADAUKI 💫: Ƙ_B💅🏻💅🏻💅🏻
Book ɗin kuɗi ne ki biya ki karanta hankali kwance 200₦/300f ne kacal,ki yi payement ta wannan account ɗin 0039161883 Bala Maryam Mikailu Starling bank sai kiyi screenshot ki turo shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin MTN na ɗari biyu.
Masu son tsofin book ɗina: *TUZURU, HADEEYATULLAH, KARUWAR GIDA, ƁOYAYYEN SIRRI,SADAM SOJANA ,MAHAUKACIN SO, ƘAWAR MOMYNA,MATAR MAHAUKACI* zaku samu ragi in kun sayi Books biyu lokaci ɗaya
*PAGE* 13_14
Wani gigitacen mari ya ɗauke Nabeela da shi wanda ya sa ta ganin taurari na gilma ma ta,ɗagowa tayi ta dube shi da idonta da suka kaɗa suka yi ja musamman ijiyar da ke côté kumcin da ya mara ɗin.
Yawu ta zubar jin bakinta ya cika da jini wanda rashin tsaftace shi ya jawo mata hakan,ido ya ƙanƙance zai zuba mata masifa ganin ko gizau ba tayi ba balle yasa ran ta matsa ta bashi gu.
"Ke Nabeela keeee!"Umma ta faɗa wacce ta leƙo waje,waigawa tayi ta dubi Ummar sannan ta maido dubanta ga Waleed ta furta "ina son ka"kawai sai ta tafi ta bar sa shaye da mamaki.Cike da takaici ya buɗe motar sa ya wuce,direct gida ya nufa sai da yayi parking sannan ya lura da rubutun da tayi masa a vitre *Mai kyau ɗan fari kyakkyawa ina son ka* tsuki ya ja ya goge rubutun da hannu ya na jin wata irin tsanar yarinyar.
"Waleed mushen école ka koma na ga hannun ka da la craie?"Ammi ta tambaya ta nuna hannun sa wanda ya ɓace da farin alli,baki ya turo gaba yace "wata baƙauya ce ta yi min rubutu a mota wai ta na sona kiji fah shashanci"Ammi tayi dariya tace "ina laifin mai son ka?gaya min yarinyar wace?"
"Ammi ba fah wata budurwa ba ce kawai irin ƙwailayen yaran nan ne da ba su san komi ba,kawai duk abinda kwanyarsu ta raya masu sai su ga daidai ne in ba haka ba wannan ƙazamar yarinyar ko wankin takalmina ba zan bata ba amman wai kin cewa tayi ta na sona mtsw"Waleed ya ja tsuki ya na mai gyara zama kan salon.
"A'a fah Likitana banda sharri,kar a zo kaji duk duniya babu wacce kake so sai ita"Ammi ta faɗa ta na gumtse dariya,shi ma dariyar yayi yace "haba Ammi ai kuwa da kun ce na walwale,na je na ga likitan ƙwaƙwalwa"
"Hum!naji tunda duk ka kushe ta ai sai ka fiddo matar aure irin ƴan gayun nan"
Fuskar Waleed ce ta sauya jin an ambaci aure,kawai sai ma ya miƙe ya nufi part ɗin sa.
Bayansa Ammi ta bi da kallo ta na mamakin birkitacen hali irin na Waleed shi sam bai da maƙiyi sai aure.Ta sauke ajiyar zuciya ta na mai tunanin mafita, kitchen ta shiga ta sauke abincin da ke bisa gaz.
Waleed na shiga ɗaki ya rage kayan jikinsa, toilet ya shiga ya fara wanka.Sanyin ruwan ya saka shi lumshe ido,baƙar fuskar Nabeela ta faɗo masa a rai lokacin da ta furzar da jinin a baki.Tsuki ya ja ya buɗe ido a fili ya furta "da wasu shagun haƙoranta da suka ruɓe mtsw"wani irin takaici ya ke ji saboda gani ya ke yarinyar ta raina sa sosai.
A can ɓangaren Nabeela kuwa faɗa Umma tayi mata akan mi ta ke jira da har yanzu ba ta tafi makaranta ba.
"Yanzu fa zan tafi"cewar Nabeela ta na ƙyaf-ƙyaf da ido,Umma tace "to miye wannan mutumen ke faɗa maki?"da murmurshi tace "wa?wai Likita?"kai Umma ta gyaɗa mata.
Ɗan sosa ƙeya tayi tace "laaa! ba fah komi kawai mun gaisa ne"
Umma tace "to daga yau kar na sake gani kuma ki kula sosai banda biye samari duk namijin da yayi maki magana kar ki tsaya" da "toh"kawai Nabeela ta amsa kafin ta tafi makaranta.
★★★ *MARADI*
Sosai Daddy ya fara shirin tafiyar Imane France duk da kuwa babu wanda ya bashi goyon bayan hakan.
Baiwar Allah ta na zaune a ɗaki ta zuba ma valises ɗin da ta zuba duk kayanta ciki ido ,tun ɗazu ta ke ganin kiran Jabeer na shigowa wayarta amman ta kasa ɗauka saboda kwaramniya duniya da ta ke ciki.
"Anty Imane ya kamata ki fidda damuwa a ran ki kar kije ki kamu da wata cuta ta daban,kiyi haƙuri ki rungumi ƘADDARA (Mrs SADAUKI) saboda gidanmu na da wani tsari daban da ko wane gida sam abubuwa ga su nan maras fasali ke ta wanzuwa shi kuwa Daddy babu ruwan sa da mu"Ihsane ke faɗa bayan ta dafa kafaɗar Yayarta.
Ƙwalla Imane ta goge tace "Ni fah ba wai zuwa France ba ne damuwata,a'a yadda Daddy ke nuna ma mu sam aure bai cikin jadawalin abinda ya tsara mana yanzu sabida Allah duk girman mu ace shi bai taɓa damun sa ba?"
Ihsane ta ja huci "Hummm!ki bari ni wlh har kunya na ke ji ace gamu gandara-gandaran ƴan mata har uku a cikin gida,kuma abun haushi babu wacce ake niyyar aurarwa shi ma Munir ya ɗau layi sosai ya ke son aure amman ya na tsoron faɗi"
Jin an ambaci sunan Munir ya saka zuciyar Munira fara bugawa amman sai ta sake lumshe ido ita a doli barci ta ke."Shi Munir ɗin yace maki ya na son aure?"Imane ta tambaya,Ihsane ta zauna ta na mai cewa "a'a bai faɗan ba sai dai alamu na gani,dan ɗazu da idona na kamasa shi da wata a ɗakinsa na waje ina jin shashekar kukanta shi kuma sai wani abu ya ke kamar dai alamun ya na sex"
"Fat!fat!fat!"haka zuciyar Munira ke bugawa,rumtse ido tayi da ƙarfi ta na jin soyayyar da ta ke yi ma Munir na rikiɗewa zuwa tsana hoton yadda yayi ta yi mata ɗazu ke ta dawo mata a kai ko kunya ba ya ji ƙanwar sa ya ke shafa.
"To Allah kyauta"shi kawai Imane ta faɗa,kafin ta miƙe ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta gabatar da sallah isha.
Ihsane kuwa falo ta fita tun daga nesa ta ke kallon mahaifin nasu wanda ya harɗe hannuwa ya ƙura ma Mimi ido ya na kallo wacce ita kuma sai faman jera abinci kan dining.Sam bai san isowarta ba sai ji yayi tace "Daddy ina wuni?"da sauri ya juyo ya haɗe rai sannan ya amsa da "lafiya"gun Mimi ta ƙarasa tace "ke zuba min abinci ki kai min ɗaki ki haɗa da jus"
Ibrahim wanda ke shigowa yace "ke kuma halan masaka uwar ki ta haife ki da ba za ki zuba da kan ki ba?mtws sai shegen girman kai da ɗagawar tsiya ki zuba da kan ki"
Ihsane ta turo baki ta na hararar Mimi wacce tayi tsaye ta na kallonta,murya na ɗan rawa tace "kiyi haƙuri kije zan kai maki"ido Ibrahim ya fiddo ya na kallon Mimin a zuci yace "ko ba ta ji abinda nace ba dai?"sai kuma ya tamke fuska ganin Daddy na kallon shi.
"An fah yi sallah isha'i tuni"cewar Ibrahim ya na mai zama kan kujera,kawar da kai Daddy yayi sai ya nuna sam bai san abinda Ibrahim ke nufi ba duk da ya san da shi ya ke saboda ya ga bai je masjid ba.
"Ke zo nan"Ibrahim ya faɗa a dake ganin Mimi ta zuba abinci a plate za ta nufi part ɗin su Ihsane.
Tsayawa tayi tace "wa?Ni?"kallon da watsa mata ne yasa ta dawowa gabansa ba ta shirya ba.
"Zauna"ya faɗa cikin bada umarni zaman tayi, ya kuma cewa "ki canyen wannan abincin"ido ta waro tace "abincin Ihsane ɗin?"da ido ya mata magana dandanan ta fara ci.
Ihsane wacce ke tsaye tun ɗazu ta na jiran har Mimi ta kai mata abinci ɗaki sai ta mara mata baya,kujerar table à manger ta ja ta zauna a doli tayi servir ɗin kanta.