← Book details Kadangarun Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 10

Sashe 4

Kadangarun Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaishe sa suka shiga yi cikin nutsuwa saboda kowa mugun shakkar sa ya ke,gaishe da Daddy yayi ya amsa ciki-ciki ya na wani ɓata rai kai kace wanda ya ke tamnar magani.
Ibrahim bai damu ba ya fara shan jus de goyave kafin ya fara cin naman hanji da Mamy tayi masa farar dafuwa,can ya ɗago yace "Mamy ina Imane ne?"duk dariya suka gimtse Mamy tayi murmurshi tace "ta tafi tiraku😹" ya sosa ƙeyar sa yace "ayya Mamy wai ba dai santi nayi ba?"Mamy ta dungure mashi kai tace "maza ci abinci da surutu"Ibrahim ya turo baki ya na cewa "ai ya ma ishe ni mu je na ci abinci tukunna"
Mamy tace "to duk ku tashi mu tai kan dining mu ci abinci Munira je ki kira Imane,Daddyn yara mu je ko?"cewar Mamy ta na mai miƙawa Daddy hannu shi kuwa gudan ƙato da shi ko kunya babu ya ɗora hannunsa kan nata,da sauri Ibrahim ya kawar da ido dama shi ne baƙon ganin haka dan su Munir har sun saba ganin soyayyar su Daddy wacce ba su ɓoyewa.

Ibrahim ya yiwa Munira tsawa yace "ke ba aiken ki aka yi ba?"da sauri Munira ta ajiye wayar Munir ta tafi kiran Imane.
Kamar wacce tayi maye haka ta fito fuska babu walwala Imane ta ƙaraso ta zauna,iyayenta ta fara gaishewa kafin Ibrahim wanda ya kafeta da ido ya na mamakin rashin tausayi na Daddy.
Ya na shirin amsa gaisuwar yaji Mamy ta ƙwala kira "Halimatuuu"haka kawai ya ji gaban sa ya faɗi sai kuma ya ji ya rasa nutsuwarsa jin muryar wata ƴar yarinya ta amsa "da na'am Mamy"sai kuma ta rugo daga kitchen ta nufo inda suke tace "gani Mamy"
Mamy ta ɗan murmusa tace "ayya zo ki yi saving ɗin mu ki fara aikin daga yanzu"da "toh"ta amsa kafin ta je gaban Daddy ta fara saving na shi kamar yadda Mamu ta koya mata yadda za tayi,ta na gamawa sai ta zuba ma Mamy sannan Munir sai ta dawo kan su Imane har ta kai ta zuba ma Munira.
Cike da mamaki ya ke kallonta ganin yadda ta zubawa kowa banda shi hasali ma ko kallon inda ya ke ba ta yi ba,har za ta tafi Mamy tace "ba ki zuba ma Babban yayan na ku ba"da sauri Halimatu ta juyo sai ta kalli inda Mamy ta nuna mata aka ci sa'a shi ma ita ya ke kallo nan take ta diririce ganin irin kallon da ya ke yi mata wanda ta kasa tantance na miye.
Jiki na ɓari tace "yi haƙuri ban lura ba,Mamu ce min tayi wannan ne babba"ta faɗa tare da nuna Munir, Mamy tayi murmushi tace "au!shiyasa kika manta da Babana to zuba mashi"ta amsa da "toh"ta ƙarasa inda ya ke ta ɗauki plate ta zuba mashi abinci sannan ta ɗauki cup ta fara tsiyaya jus ciki hannunta sai karkarwa ya ke.
Yatsunta ya ƙura ma ido uwanda suka sha jan lalle haka kawai ya samu kansa da kai hannu jikin cup ɗin ya karɓa ya na cewa "Merci !"da sauri ta ɗago kai ta kalle shi ta na jin wani daɗi saboda yace ya gode ba kamar sauran ba da suke mata kallon tsiyatatu.
Cup ɗin ya kai baki ya fara shan jus ɗin sai kuma ya ajiye ya fara tsakurar abincin,ita kuwa Halimatu kitchen ta koma gun Mamu wacce ta ke hadadar yin girkin dare Ƴarta na tanyata.

★★★ *BAYAN WATA ƊAYA*

Ameera tayi tagumi ta ƙurawa allon ajin da malamin su ke ta faman yi masu expliquer,a yadda ta ke kallonsa kai kace dukan hankalinta na gun shi ne.Ya na tsaka da cours ta fito waje ta shiga kelaya amai babu ƙaƙautawa kamar ranta zai fita,dakyar ta miƙe tsaye ta nufi can inda ta ke hangen pampo.Bakinta ta kuskure ta samu dakali ta zauna ta rabka tagumi "shin wa zan shaida ma wannan baƙin labari?babu shakka ciki ne da ni tunda ga alamomi nan sun bayyana kamar yadda malamar mu ta faɗa mana alamomin masu ciki..."kafin ta gama tunanin wani aman ya sake tawo mata.
Jikinta ta wanke ta fita daga harabar makarantar, adaidaita ta tara tace ya kaita ADS,suka yi ciniki ta biyasa kuɗin ya kaita.

A bakin ƙofar gidan tayi sallama, Baba Garbati mai gadi ya leƙo ya amsa, murya na ɗan rawa Ameera tace "cikin gidan ni ke son shiga" Baba Garbati yace "wajen wa kika zo?" "Mamy" ta basa amsa sai kawai ya bata hanya,har tuntuɓe ta ke wajen shiga.
"Assalamu alaikum"Ameera ta faɗa Halimatu wacce ke tsefe ma Ihsane kai ta amsa,shigowa tayi ta gaishe da su duk suka amsa kafin Ihsane tace "Ameera ke ce yau a gidan na mu ?"murmurshin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo tayi kafin tace "eh wlh Alhaji yace na zo na amshi saƙo"ba tare da wani tunani ba Ihsane tace "kin kau ci sa'a ya na gida am ki shiga ya na ɗakin sa"ta faɗa tare da nuna mata part ɗin,jiki na rawa Ameera ta nufi ɗakin Alhaji .
Da salama ta shiga amman ba ta ida ba sauran ta maƙale a maƙoshi sakamakon tarar da shi da tayi zirrr haihuwar uwar sa ya na biyawa kansa buƙata.

Sanin babu mai shigo masa ɗaki in ba Mamy ba yasa Alhaji ko waigowa bai yi ba sai jin shashekar kukan ta,da sauri ya juyo maimakon ya razana sai kuma ya ji wani bala'in daɗi.
"Ah!ah"Meeran Alhaji daga ina kike?"ya faɗa ya na washe baki tare da nufota zai rungume ta ja da baya ta na rufe idonta,da ƙarfi ya jawota ya manna bananar sa cikin tafin hannunta ya shiga mulmulawa har ya samu nutsuwa Ameera ba tace masa komi ba dan damuwar da ta ke ciki ta fi wannan.

Babu alwala balle wankan janaba haka Alhaji ya saka kayan shi ya na mai kallon Ameera wacce ta rasa ta ina za ta fara gaya mashi.
"Tashi mu je"ya faɗa ya na ɗaukar key ɗin mota,babu muso ta miƙe ta bi bayansa su na fitowa Mamy tace "sai kuma ina Alhajina?"murmurshi yayi yace "Malam Abba ne ke son kayan abinci to dama na ce ya je mangaza su amsa to wai shi Nairo ya hana su shine nace bari naje da kaina"
"Ina kwana"sai a lokacin Ameera ta gaishe da Mamy ta amsa kafin ta yiwa Daddy addu'a.
Ya na gaba ta na biye da shi a baya suka nufi motar shi,gidan gaba ya buɗe mata ta shiga ya yiwa mota key sai gidansa wanda ya ke GAO.
"Fito mu shiga ciki"Alhaji Mudi ya faɗa lokacin da yayi parking Ameera ta maƙe kafaɗa tace "ciki gare ni"ta faɗa ta na fashewa da kuka, murmurshi Alhaji yayi yace "ai na san da haka shiyasa na kawo ki a cire maki shi"jin maganar za'a cire ya saka Ameera fita daga cikin motar.

A ɓangaren Ibrahim kuwa gaban idonsa Alhaji ya fita shi da Ameera ,da sauri ya shigo falon cikin rashin sa'a Halimatu ta kai masa karo kwanan kunun da ke riƙe da hannun ta ya faɗi ya zube mata a ƙafa.
Ihu ta saki ta na yarfe hannuwa,jiki na rawa Ibrahim ya nufeta da sauri ya cire rigar sa ya kamo ƙafarta ya shiga goge mata.
Ta na kuka ta dafa kansa shi kuma sai busa mata iskan bakinsa ya ke, Mamy wacce ihun Halimatu yasa ta fito tace "lafiya mi ke faruwa?"Ibrahim ya ɗago yace "Mimi ce kunu ya zube ma a ƙafa"
Mamy tace "ayya!to ayi mutum kullum cikin gudu,takwara ki rinƙa kulawa mana mu ga ƙafar"ta duƙa ta na dubawa ƙafar duk tayi ruwa "ina ga sai an kaita asibiti"cewar Mamy Ibrahim yace "a'a bari na bata magani"ya miƙe tsaye ya na jin sa wani iri Mamy ta ja hannunta suka nufi salon sai ɗage ƙafar ta ke ta ƙi takata😒

Babu jimawa Ibrahim ya dawo,cup ya cika da ruwa ya miƙa mata ta ƙi karɓa sai jujuya kai ta ke.
"Please Mimi ki sha wannan zai taimaka maki wajen ɗauke zafin ciwon sannan yayi saurin warkewa"cewar Ibrahim ya na mai sake miƙa mata Mamy ta karɓa dan haka kawai ta ke jin yarinyar har cikin zuciyarta amman ta alaƙanta haka ƙila dan sunan su iri ɗaya.

Juyin duniya Mimi ta ƙi shan magani,karɓar maganin Ibrahim yayi rai ɓace ya nasa sa cikin wani kofi ya zuba ruwa sai da ya narkesa sannan ya riƙe dukan hannuwanta Mamy ta yi mata ɗure.
Yawu ta shiga zubarwa ta na kwaɓe fuska alamun rashin jin daɗin goût ɗin, Mamy tayi dariya tace "oh!takwara yanzu maganin ne sai an yi maki irin na ƴan yara?"
Ihsane wacce ta saka apple ga kanta tace "Mamy ke ma fah haka Daddy ke fama da ke in za ayi maki allura ƙila dan sunan ku iri ɗaya da Mimi ɗin shiyasa..."kallon da Ibrahim ya watsa mata ne yasa ta yin shiru ta na sunne kai.

Part ɗin sa ya nufa ya na jin wata irin kasala na rufe sa,wani ɓangaren kuma sam zuciyarsa ba ta kwanta da fitar da ya ga Daddy sun yi da Ameera ba duk da bai ga fuskar ta ba yadda ya ga mahaifin na shi na rawar jiki har da buɗe mata mota yasa ya so bin su sai kuma Mimi ta dagula masa lissafi.
Ajiyar zuciya ya sauke a fili yace "akwai aiki gabana ashe shan magani ma ba ta iyawa mtws na tsani mace mai shegen son jiki ita ba ta iya kula da lafiyar ta to ina ga ƴaƴan mu"sai kuma yayi dariya yace "oh! Ibrahim wai mi ke damun ka ne?"jin an buɗe ƙofa ya sa shi juyowa da sauri Munir ne.
Chapter 4 · 0% Book details