Sashe 7
Kabilata Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
AND
NOW KABILATA
BISSIMILLAHIRRAHMANIRRAHIM
Page 11&12
tun shigowar shi garin yana yin da yaga mutanen garin da yana yin kayan dake jikin su yasa shi fahimtar a Kwai wani buki da suke gudanarwa, bayan isowar shi masarauta ya ga abun da ya baro cikin gari, cike masarautar take da mutane ta ko ina sai kai kawo ake yi kuma duk yawan mutanen dake kai kawo a masarautar duk shigar su ta gargajiya ce ajikin su, mazan na daure da (walki) fata wanda ya saya musu iya guiwa basu da riga sannan yawan cin samarin sun bar sumar kansu tayi sayi an kitsa musu shi inda aka sako musu tsoro gefe da gefen kunnen su yadda matan bororo ke yi sannan wuya da hannayen su sanye suke da duwasu da suka sha ado da kaloli da ban da ban,
inda matan kuma ko wacce zaka kai duban ka gareta bata da riga sai nafkin da ganyen da suka daura a gaban su da baya yawan cin matan aski ne a kansu amma ba gama garin aski ba irin askin nan da za’a kwashe gefe da gefe abar gaba zuwa baya kuma bada suma yar kadan ba suma mai tsayi suke bari, suma wuyansu da kunnen su zuwa tsintsiyar hannunsu da damtsen hannun duwasu ne aka kawata su da su har zuwa sarkar kafa kuma yawancin su bakin su a rufe yake da pin blue color.
duban shi ya kai inda yaga dandazon maza tsofaffi, nan kuma ba komai suke yi ba sai dahuwar giya manyan tukane fin goma, gefe daya kuma ga abinci kala kala da aka fitar daga ko wani ban gare na masarautar da duk wani ahalin masarautar dake rayuwa a wajen masarautar sai da yayo abinci, sannan ga makida sai kida sukeyi suna rera waka da yaren su, sai lokacin Areef ya fahimci me ke faruwa, fuskar shi babu walwala kamar kullum kuma tana sakaye cikin yar gadon wato face mask ya fito daga cikin motar da guard dinshi daya ya bude mai, sam bai ji dadin yadda masarauta ta katya alkawarin da ta dauka na barin wannan aladar ta shude ba, idan da yan gargajiya ne to yanzu musulunci ya zo da sauyi,
“In kaji ana duhun dare mai ɓatar da Rigar sarki, Sarari mai ƙure gudun doki, tafi dai sannu Garkuwar Kambari, Jan zaki Maganin Abokan gaba, Sadauki Adalin Jagora_ kana Gaba kullum suna bayan ka, Yareeman Shambo, . Wasu mutanen tamkar hasken fitila ne acikin duhun dare, kamar haka kake acikin rayuwar Kambari kai Garkuwar mune, kaja sunja basu ga da kyau ba, kai din jeji ka ke kafi gaban Ayi maka ƙyaure, tahh kawar ka lafiyahh Yareema.”
hannu ya daga ma fadawan dake zube suna jero mai kirari, ya shige cikin gidan,
“Areef meyasa baka fada min ruhin Babana kake gani ba, kuma baka fada min abun da yake bukata ayi mai ba, sai bayan wucewar ka ne Yayanka Sadeeq ya ganshi, shine ya bayyana mai bukin mutuwar shi yake so ayi mai.”
“Amma Baba, ba ka riga ka yanke wan nan al’adar a yankin nan ba, me yasa yanzu za’a tayar?.”
“Aa Areef a ina ka taba jin an yadda al’ada baki daya, sai dai a rage wasu abubuwa amma ba duka ba.”
“Shi kenan Allah ya taimake ka, idan ka min izini zan shiga daga ciki.”
“ta ya zan maka izini Garkuwar Kambari, bayan kasan da akwai abun da nike son ji daga gare ka.”
shuru ya yi kafin yace,
“tana cikin koshin lafiya a tare da ni, amma?.”
“amma me? ya ka yi shuru wata masalace, ko a kwai wanda take so ne,? kara suka shigar?.”
“har yanzu basu san ni na dauke ta ba,”
ya dan ja fasali kafin ya ci gaba,
“yariyar bata magana ban sani ba ko dama haka take?.”
“kada ka damu da rashin maganar ta, idan ka dawo da ita za’a san abun yi.”
“ke nan ka san me ya same ta,? dama ba kurmanya bace?.”
Areef ya yi maganar yana dagowa ya kalli Mai Martaba,
murmushi mai Martaba ya yi,
“aikin matar Khamal ce, kaci gaba da zama tare da ita har lokacin da KHAMAL zai tako kafar shi cikin garin nan.”
bai ce komai ba ya mike, sallama ya yi ma Baba ya fito, fitowar shi harabar Masarautar yasa shi jin kanshi na sarawa, sakamakon haya niya da kide-kiden da ya cika wajen, wan nan dalilin ya sa shi canza shawara daga niyar kwanan da ya yi, ta ina zai iya kwana cikin masarautar da wannan hayaniya, kawai kara ya koma, koma wa wajen Mai Martaba ya yi ya sallame shi, bayan ya fito sashin Mama ya nufa ya dan jima acan kafin ya fito inda guard din shi suke suka baro garin.
lokacin da suka isa Minna yamma ya yi dan har shidda ta gota, hakan yasa kai tsaye gida suka nufa, wanka ya yi ya kwanta dan huta gajiya, nan zuciyar shi ta tuna mai da Samrah da ko sunanta bai sani ba, tuna nin shi daya ta ci abinci,
(“wait, wa ya kai mata abincin da zata ci”)
a zuciya ya yi maganar yana mikewa zaune , tunowa da ya yi bai bar mata abinci ba duk da dai ba ci take yi ba, mikewa ya yi ya, ya canza kaya ya foto, koda ya isa bai ganta cikin room din ba amma yaji motsin ruwa a toilet alamar tana ciki, ajiye ledar take away din da ya yo, ya yi ya zauna a bed din yana dan kishin gida,
Ahankali ya shiga ware lumsassun catly eye's dinshi saka makon yadda yaji a jikinshi ana kallon shi, 4 eye's suka yi da Samrah da ke zaune ta hade guiwowinta guri daya ta rike da hannuwan ta, samm bata yi sammanin zai buɗe ido har ya kamata tana kallonsa ba.
Luuuuu yayi da idanunshi kamar zai lumshe su amma bai rufe ba, hakan yasa tayi saurin kawar da kanta daga kallon kurillar da take mai, ta cusa kanta cikin kafafunta, ahankali ya mike zaune daga saman bed din yana zuuro kafafun shi kasa,
bai san ya aka yi bacci ya dauke shi a dai-dai wannan lokacin ba, kallon shi ya kai ga agogo 9:50pm ahankali ya janye idanunshi daga kan agogon ya mayar ga take away din da ya ajiye mata, a rufe su ke ba alamar ta bude balle har ta ci abunda ke ciki,
mikewa ya yi bathroom ya fada akalla ya shafe 15mn a ciki kafin ya fito daure da towel fara kal a kugun shi,
har yanzu ta na nan zaune a inda ta ke kuma bata dago kanta daga cusa shi da ta yi cikin kafafun ta ba,
Kafeta yayi da catly eye's dinshi, kwakwalwar shi na hasko mai, yau kwananta ukku a tare da shi kumma acikin kwana ki ukkun nan zai iya kirga sau nawa wani abu ya shiga bakin ta da sunan abinci,
ji ya yi zuciyar shi ta yi wani iri, yasan ta na da tarin tambayoyi da take son a amsa mata su amma sai dai rashin maganarta yasa ta hadiye su,
tunawa da bata magana yasa ya sake jin wani iri, tattaro duk natsuwar shi ya yi, inda take ya nufa durkusawa ya yi a gabanta har guiwar shi na gogon kafarta,
da mugun sauri ta dago kanta jin kamshin showergel dinda ya hade da hadadden kamshin da jikin shi ke fitarwa ko yaushe sun mata yawa a hanci,
kai tsaye cikin catly eye's dinshi, idanunta suka sauka, kallon seconds ta mai ta dauke kanta tana mayar dashi kasa ga fararen zara-zaran yatsun kafar shi,
Gently shima ya lumshe nashi fararen idanuwan ya na sauke wani nannauyan ajiyan zuciya,
soft fararen zara-zaran yatsun hannunsa uku ya sanya yaɗago fuskarta, saurin lumshe idanunta ta yi wanda hakan ya ba zara-zaran eyelashes din ta damar kwanta wa luff akan farar fatar kumatun ta dake sheki,
har zuwa lokacin kuma shi be janye idanun nasa a kanta ba
motsi ta fara yi da idanun ta, tana ƙoƙarin kwatar numfashin ta dake barazanar dauke wa. lips inta na ɗan rawa a ƙoƙarin ta na ganin ta yi magana. sai dai laɓɓantan sun mata nauyi sun gaza bata haɗin kai wurin yin maganan.
lips dinta dake motsi ya zuba ma idanunshi har adams apple ɗinsa na ɗan motsawa a maƙoshinshi,
"me yasa baki cin abinci?.” A natse cikin hosky voice dinshi ya yi maganar, slowly yana janye idanunshi daga kallon lipsdinta.
Wani irin tsalle taji zuciyarta ta yi a karo na farko, dajin saukar kakkausan muryar shi mai zurfi a kunnen ta kuma kusa da ita da kuma iskar da yake fitarwa daga kirjin shi da kai tsaye yake sauka akan fuskarta,
rawa bakin ta ya fara yi sosai da hannuwanta, dan sam bazata iya jure ma wannan kusancin nasu ba gab take da fashe mai da kuka,
jaye yatsun shi da ya tallefe fuskar ta dasu ya yi, ya juya ga take away din ya jawo shi gaban shi, bude wa ya yi, har lokacin abincin da zafin shi jolop din Macaroni ne da dankali da busashshen kifi, spoon ya sa ya dibo, kai tsaye ya nufi bakin ta da haryanzu yake dan rawa kuma idanunta na nan rufe,
“open ur mouth.”
taji saukar muryar shi cikin kunnuwanta, slowly ta shiga buɗe idanunta akan spoon din da ya kawo saitin bakinta idon ta suka sauka, ɗan lumshesu ta sake yi tana ƙoƙarin saita kanta dan koda wasa ba zata iya yi mai mutsu ba,
kuma ko ba komai ta na bukatar abincin dan yunwa na gab da yi mata illa,
a hankali ta bude bakinta ya zuba mata abincin, ta fara taunawa sai da ta hade sannan ya sake debowa ya bata,
bai fi 10spoons ba ta kawar da kai,
bai ce mata komai ba ya mike da ga durkushen da ya ke tun dazu, karamin fridge dake dakin ya bude goran ruwa mai sanyi amma ba sosai ba ya dauko ya dawo inda take tana binshi da kallo, bude ruwan ya yi ya mika mata amsa ta yi ta sha sai da ta sha fin rabi sannan ta mika mai goran, amsa ya yi ya mayar ya aje,
cikin nasuwa da kwanciyar hankali ya ke shiryawa, ita ko Samrah fuskarshi take kare ma kallo ta cikin mirror yau ne ta ga complete face dinshi dan bai sa yar gadon ba face mask, har ya gama shirin shi cikin riga da wando na trouser, ya yi parking sumar kanshi da ya gyara ta saf ya dauki phone’s din shi, ba tare da ya ce mata komai ba ya fita hadi da rufo kofar.