← Book details Kabilata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 7

Sashe 3

Kabilata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shuru ya yi kan shi a kasa, sanin halin Areef din, ko zasu kwana a nan idan bai yi niyar magana ba to ba zai yi ba.

“allah ya shige muna gaba, Babanku ya tafi ASHENGI.”

mikewa ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fita.

sai da ta kwankwasa kofar a ka bata izinin shiga, sannan ta tura kofar da sallama, sanyin ACn da ya fara tarbar ta ne yasa ta tsaya wa tana fadin,

“Ya ilahi,Habibty wani irin sanyi ne haka.”

“Amin wa’alaikissalam, Ummuh Hidaya, good morning.”

kallon inda ta ke ta yi, 
tana zaune a bed ta rufe kafafunta zuwa kugunta da lallausar blanket milk color, kayan bacci ne a jikin ta riga da wando masu laushi suma milk color, kanta na cikin slipping cap shima milk, kayan sun amshi jikin ta kasanciwar ta fara, cup ne rike a hannun hagunta tana siping zallar madara dake ciki, hannun damarta na rige da sadaddiyar wayarta tana dannawa.

isa inda take Ummuh Hidaya ta yi, ta yaye blanket din, ta amshi cup da wayar, ta ajiye gefe, hannunta ta riko tana fadin.

“maza tashi ki shirya, tunda abun ya zamar miki jiki,kullum sai ance miki ki shirya, kamar bake kika sa kan ki aikin ba.”

ya mutsa fuska ta yi, bata ce komai ba, ta mike tsaye a gaban Ummuh Hidaya, kafe Ummuh Hidaya ta yi da ido ko kyaftawa bata yi.

ita ma idanu ta zuba mata, aranta tana fadin “abubuwan sun zo kenan,” 
ganin bata da niyar daina kallon ta yasa ta hura mata iska a fuska, tace.

“zaki makara fa.”

ajiyan zuciya ta sauke, cikin yar karamar muryar da ke nuna ta gaji da tsayin, tace.

“Ina sonki Ummuh Hidaya.”

murmushi ta yi, ta kama hannunta, ta nufi toilet, sai da ta bude toilet din, sannan tace.

“Ni ma ina sonki, Habibty, yi sauri kada Abbanki ya gaji da jira.”

ta mayar da kofa ta rufe.

barin dakin ta yi, 

★……..

“ ASSALAMU ALAIKUM Barkanmu da wannan lokaci masoya!, kuna tare da SAMRAH KHAMAL  ASHENGI a yau tafe nike muku da wani kayataccen albishir da nasan za ku so shi, albishir ne akan shahararre kuma matashin dan kasuwan nan naku wato AREEF IMRAN mai kamfanin A&I BAG’S da dai sauran kanfanunuwan shi da kuka sani, albishirin anan shine ya shirya daukan matasa aiki a kamfaninshi na BAGS da ke nan cikin garin Minna wato A&I BAGS wannan kyakkyawan dama ne a gare ku matasa,sai ku yi hanzarin zuwa companyn don haduwa da madubin ku kuma ja gaban matasa, da wannan nike ce muku mu wini lfy.”

Ɗan madaidaicin Agogon Rolex ɗin dake hannunta ta shiga  dubawa  ganin har daya tayi yasa ta sakin dan tsiririn tsaki tana shafa cikin ta data ji yana mata kugin yunwa 

★……….★

“tahkawar ka lafiya ginshi ƙin dutse, kowa ya yi karo da kai shizai faɗi,Namijin mazaje, a takawarka lfy Yareeman Shambo anbuga dakai ambarka, domin kai ɗin hadari ne malafar duniya, taka a sannu garkuwar Kambari kaɗangaren bakin tulu a barka ka ɓata ruwa a kasheka kuma  ka fasa tulu. kai kadai ja gayya Kabewar kan kabari baƙin cikin me taushe, murucin kan dutse kake baka fito ba saida ka shirya , Allah yakaro albarka uban gidana Yareeman Shambo."

kirarin da fadawa ke jerowa ne ya ankarar da Sarki Imran dake hakimce akan fatar zaki wadda aka ma ado ta ko ina, da sauran diyan shi da kannen shi, isowar Areef wirin,
tsayawa ya yi ba tare da ya kara ko one step ba yana kallon gefen da dawakai suke bayan wasu second ya ja tsaki da yasa Sarki Imran ya kalle shi, ganin ya kafe waje daya da ido ya sa Baba kallon wajen, ganin ba komai a wajen ba yasa shi mai da kallon shi ga Areef da har yanzu idanunshi na wajen,

“tun ba yau ba dama ya yi tunanin akwai abun da Areef din ke gani wanda su basu ganin shi, to amma menene? .”

wani tsakin Areef ya sake yi, ya na barin wajen, inda Baba ya ke ya isa gefen shi ya zauna ya na sauke bakin tsakin da ke yafe a kafadan shi ya yi shuru, shima Baba shuru ya yi, a ran shi ya na mamakin miskilanci irin na Imran, sun fi minti biyar a haka, kafin Baba ya kalle shi yana fadin,
“menene abun da kake gani wanda mu bamu ganin shi a gidan nan?.”
Cikin rashin son ya magantu saida yaja wasu sakonni kafin cikin deep sound nashi ya furta “ba komai.”
kyale shi kawai Baba ya yi ba wai dan ya yadda da ba koman da yace ba,mikewa ya yi, bai bi ta kan mutanen dake zaune a wajen ba ya nufi hanyar da zai sada shi da ban garen mahaifiyarshi,

“ai dole ya ga abunda mu bamu ganin shi tunda idanun shi ba irin namu bane.”
ya ji muryar Kawu Nuhu, bai juya ba yaci gaba da tafiya,

“Areef,”

Ya ji an kira sunan shi wanda yana da yaƙinin brother ɗInshi Sadeek ne, ba tareda ya bi takan Sadeek din ba ya cigaba da tafiya, kawu Babangida ne yace,

“ba ka ji kiran ka yayanka ya yi bane? Ko bai kai ya dakatar da kai ba?,”
Kawu Nuhu da ke tsaye gefe shima ransa a ɓace ya karɓe da faɗin 
“iyakar mu ya ke so ya nuna muna kamar yadda ya saba."
Har lokacin bai da alaman zai furta wata kalma, sai ma lumshe idanunsa da yayi"Yaya ka gani koh? wannan koyarwar uwarsa ce, ita ce ta koya masa duk wannan halin, yaro an koya masa raini da rashin girmama na gaba da shi,ba yayunsa ba har mu iyayensa bai bari ba," 
Kawu Babangida ya yi maganar yana huci,
har lokacin yana tsaye, sai dai wannan karan yayi folding hannayensa a ƙirji, jin ya ambaci Mamarshi yasa ya ɗago catly eye’s dinshi ya dube shi, 

“ƙarya yayi ne? Kake kallonsa da waɗannan  idanunnaka na aljanu? Ko ƙarya ya mata ne?” 

“ ya isa haka bana son kananun maganganu, kai Areef ta fi inda zaka.”

Mai Martaba ya katse cece-kucen da suke son daukowa,

dauke idonshi ya yi daga kan Kawu ya juya ya bar wajen.

★……..★

ke nike saurare Samrah.”

kasa ta sake yi da kanta, dan ta guje ma kaifin idanun su Abba da Mommy da Ummuh Hidaya da Yaya Sameer dake zaune acikin palon Abba,
“yanzu me Abba ke son ta ce mai bayan tsaka mai wuyan da ya jefa ta, ta ya zai tambaye ta auren Yaya Sameer din da ta ke ma kallon dan uwa, ita ko kadan bata ta ba mai kallon wanda zata iya yin rayuwar aure da shi ba,ta ya zata amsa ma auren shi.”

kallon ta Mommy ke yi da wani tashin hankali da tsoron da suka kasa boyuwa har sai da suka bayyana kan su akan fuskarta,
Ummuh Hidaya ma kallon ta take tana jiran jin me zata ce,  “a iya sanin da ta ma Sameer bai da wani aibu da zaisa a kishi, amma ko kadan ba ta son wannan hadin da Abba ya bijiro da shi yanzu, haka kawai taji hankalin ta bai kwanta da hadin ba.”

“na san kina jina Samrah.”

Abba ya sake fadi har lokacin idonshi na kanta,
wani yawu ta hadiye na tsoron kalmar da zata furta ma Abba, kafin tace,

“I am sorry Abba amma ni ban son Yaya Sameer asalima ni kallon dan uwa nike mai.”

da gudun da ya zarce misali wani abu da Sameer bai san ko mene ba ya taso daga cikin kirjinshi zuwa makoshinshi yana neman fito wa waje, “Innalillahi wainnailaihin raju’un ya allah.”

ya furta a ranshi 

dagowa ta yi ta kalli Abba da tun bayan yin maganar ta taji shurun shi bai tanka ta ba, ganin yadda ya kafe ta da ido yasa ta yi saurin sauke kanta kirjinta na dukan uku-uku,

“shikenan tashi ki tafi.”
taji muryar Abba, ba musu ta mike kamar wadda kwai ya fashe ma a ciki ta bar palon.

Typing📲
      KABILATA 
            (LOVE MEET POWER )

Story and writing ✍
👸🏻Queen mk👸🏻

KABILATA
daga Marubuciyar 

📙TSUGUNNO BATA K’ARE BA:free

             AND 
NOW        KABILATA 

BISSIMILLAHIRRAHMANIRRAHIM

PAGE 5&6

“wai ni kam Mariya ina aikin Malamin nan da kika ce ya na ci kamar yankan wuka, abu har yanzu shuru kamar an aiki karuwa dakin kwarto, idan ba zai iya ba ya sanar in nemi wani, ban rabu da wan nan ba ga wani sabon masifa na sawo kai.”

Mommy ke maganar ya yin da take zaune a gefen bed dinta da waya a kunnenta, daga daya bangaren wadda ta kira da Mariya tace,

“wani irin masifa kuma Samira,
“mutwww ki bari kawai wallahi ina cikin tashin hankali, wai aure Alhaji ke son hada Sameer da Samrah.”

“what aure fa kika ce, lallai.”
“yadda kika jin nan ke kuma aikin Malamin nan naki shuru, kamar an shuka dusa.”

“kwantar da hankalin ki wannan shine first time din da kika fara aiki da shi shiyasa kike ganin aikin bai ci ba.”

“kai wallahi aiki kam bai ci ba, Malam ya canye kudi ya yi shuru, yariya sai wani ji da ita Alhaji ke sake yi kamar zai mai da ta ciki, yanzu kawai a canza aiki a kurmantar da ita ya zama tana ji amma ba ta iya magana, ina dan mafari yariya ta zamemin kadangaren bakin tulu, wallahi na tsani yariyar nan da uwarta.”

“ wan nan duk mai sauki ne, amma fa zaki sake kashe wasu kudin.”

tsaki Mommy taja tana fadin, “ke kin san wannan ba masala ta ba ne mai wuyar dai aikin ya yi.”
“ok zan kira shi mu yi magana zaki ji ni.”
da haka suka yi sallama, farin ciki fal zuciyar Mommy

★…………★

 “mai Martaba yanzu a Kwai adalci cikin takurama Babana da suke yi akan maganar aure, shi aure fa lokaci ne dashi, idan har lokacin yin shi ya yi to ba makawa sai anyi ko ka shirya ko kada ka shirya.”

“ki sani suna wan nan maganar ne akan zabar shi da nayi a masayin Yareema, ba wani abun damuwa anan tun da dai baza su yi mai auren ba, dan na riga na zaba mai matar da zai aura.”
Chapter 3 · 0% Book details