Sashe 2
Hariji Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na dauko adama muka samu gida a suleja Na kama mana haya ,tunda Na hada mata biyu Na fara qaura da kwanciyar hankali,akuma lokacin Na samu izinin zuwa qaro ilimi qasar Ghana,yazama Ina aikina Ina samun kudina Ina Tarawa ,har Na Tara Na guduwa qasarmu
Sannan wayan hannu bai yawaita ba,saidai ka bada saqo ta gidan wasiqa ,sanda Na gama masters dina ,Na yi qudurin zuwa gida ,sannan aka kawo mun wai matana sun aihu ,daya wata biyar da suka gabata daya shekara,sunan yarana Irfan ,da Arif
Nayi farinciki sosai,saidai naqi komawa Nigeria Kar kudin da Na Tara su gantale
***
A lokacin da Na isah madina da tambaya Na iya gane tushena,zuwa lokacin arziki ya tumbatsa ,gidanmu ya Zama gawurtaccen gida da babu kamarsa ,
Babana har kuka yayi saboda ganina da yayi "ban kyautawa Atika ba,ai Atika bata cancanci bayanta su Zama hakan a wajena ba,ina ka shige yarona ? Tsawon shekaru,kana ganin tunda na rasaka ban kuma samun yaraba sai a en shekarun nan sanda tsufa ya kamani? Ban kyauta maka ba Kabeer,ban iya sauke nauyin da Allah ya sargafamun ku a wuyana dashi ba" kawai sai ya fashe da kuka
Rungumesa nayi Ina hawaye ina basa haquri,saida zuri'ar mu duk suka hallara sannan ne,na bada labarin duk abunda ya faru da kuskurena da na aikata Na baya" kowa Allah Wadai ya qarayi da Sulaimi,anan nikejin bayan tafiyata ita ta hurawa Sophy wuta saida ya auri babban sarkin madina,don kawai abun duniya,sannan aka kamata da kwarto dumu dumu. Yanzu haka suna gidan yari an yanke masu daurin rai da rai,saboda sunyi zina alhalin sunada aure"
Sosai kabeer yaji babu dad'i Adnan ya tambayi Ina hajiya babba ? Wanda Sophy taci sunan ta ,akace shekaranta uku kenan da rasuwa
Allah sarki komai ya Zama tarikhi kiyayya ta kau,yanzu Ana lelena a cikin dangina, ga matar babana Na lokacin. Tana sonmu da Sophy
Bayan Na huta da kwana biyu Na tafi gidan er uwata In dubata tunda mijinta baya qasar yina England kuma ya hanasu fita in bada izininsa ba.
Auren sophy a Babbar masarauta,da alheri kuma da cutuwa,tunda gayinan ta auri sarkin Babbar masarautan ,babba tsoho,harma shine ya qarawa baban su muqami ,saidai sarkin bayi haihuwa amma daga zuwan Sophy ta haifa masa d'a Namiji,saboda godiya ga Allah ya sama yaro suna *Mohammadu Adnan* yanzu shekaran Mohammed uku a duniya ,saidai Sophy da Mohammadu Adnan suna cikin halin iftila'in kishiya ,wai sau biyu Ana attempting kashe Adnan ,Allah yina tseratar dashi .
Sannan ba Wanda ya isah yace kishiyar Sophy ke neman aikata wannan danyan aikin.
Kabeer Ahlan sun Sha kuka da qanwarsa ,daga qarshe suka shirya plan in zai tafi zata bashi adnan ya gudu mata dashi in ya girma ya kawoshi usulinsa ,a lokacin ba me iya masa barazanin kisa
Aikuwa haka akayi,ya daukesa suka taho Nigeria matsayin yaronsa ,ya damqawa uwargida Adama ta rainesa,to ananne hassada da qyashi ya shigeta ,wai akan Mene ,zata riqe yaro balarabe duk inda suka shiga Da yaronta Irfan ,Adnan sai ya fishi farinjini da soyuwa a cikin jama'a ? Shima anan adnan ya fara fuskantar nashi kalar qalubalen ,don Abike nata yafi worse ,haka zata bashi rainon danta ,cool you imagine dan shekara uku da rainon dan wata shida ,me koyon Zama,in Arif yayi kuka ko ya kifa haka zatasa kililin dabino da suke dashi a gidan ta zaneshi ,kuma Adama bazata cecesa ba.
Ga horon yunwa da Ake masa ,sannan in ya gani yaci to Abike ta iya horon borkono,haka zata cikamai baki da barkono mara magi da gishiri tsuran garin yajin,nan zeyi ta ihu,bakinsa ya d'ashe yayi jajur,sai yayi kwana da kwana ki baya iya cin abinci,ranar da quliya ya fara Lura ,yayi fushin da bai ta6a yiba,ga d'a ba baki,aikuwa ya sa dorina yayiwa dukkansu mugun duka,don ya gane hakan ne saboda zawon barkono da yaro yayi tayi saida aka kwantar dashi a Asibiti ,Kuma matan suka qi Kula dashi ,sai zainabu ne tazo daga minnah ta zauna da adnan ,tana kuka tana kallon gata irin Na adnan amma Ake masa irin wannan izayar,kawai saboda kishi ya had'u masa ta kowani angle
Sosai Zainabu itama tayi fushi da adama,saidai quliya ya kwa6eta da ta bari su San usulinsa ko shi wanene...
73&74
*Alheri writers asso.*
Haka rayuwa ta cigaba da murginawa da dad'i ba dad'i,saidai zuwa yanzu kudi sun fara Zama ma quliya ,ga courses da yike zuwa akai akai ,yaransa har sun Isa shiga makaranta ya sakasu duka,amma sanda Adnan yakai shekaru biyar ganewa yayi in ya bar yaron a hannun matansa to zai iya salwanta,yaro dan amana. Yakuwa daukesa ya fitar dashi waje karatu ,shima yaje yin PhD dinsa ,a rutsutsin ya dawo ya tarar da duk matansa suna laulayi ,bayan ya koma da watanni Abike ta koma gida haihuwa ,itakuma Adama ta haihu a gidanta ,Aka sakawa yarinya suna rufaida,itakuma Na Abike mufida.
Abunda ya fara sakawa quliya shakku akan matansa yanda Sam suka qi turo masa hotunan yaran da suka haifa,sannan ya Kira en uwansa (me -lafiya family) sunce ba'a fada masu haihuwar ba,ya tura abokinsa yaje ya dubo masa yaransa ,an hanashi ya shiga wajensu,Sosai abun ya daure masa Kai ,To a lokacin ya Zama cikin Alqalan da suke Zama a gaban Alqalin ,Alqalai Na wancan lokacin don haka, ransa yaji ta darsa masa wata abu Na dabam,amma ya barshi sai yayi bincike...
*Bayan shekaru sha biyar*
Adnan a lokacin ya gama Isa duk wani munzalin girma,amma har kawo lokacin quliya bai ta6a kaisa gurin danginsa ba,kuma yaron ko ya tambayi quliya mahaifiyarsa saidai ya kama masa en dabaru,amma bazai bashi takamaiman amsa ba,ga matan quliya da suke wareshi a cikin yarorinsu ,a cewarsu adnan shegene ,quliya garin yawon duniyarsa ne ya dirkawa balarabiya ciki ta haife shi,don haka adnan ya taso Sam bashi da sakin jiki da jama'a ,yafi gane rayuwar makaranta fiyeda Na gidansu
A lokacin da Adnan ya samu hutun semester exams ne Na sati biyu,Quliya ya shirya Adnan suka tafi madina,anan ya bayyanar masu da adnan wato 6ataccen magajin masarautan su ,lokacin Sam baya jin larabci sai turanci ,zuwan adnan ya kawo rikita rikita a dangin kafin daga qarshe bayan tsauraran hujjoji da quliya ya kawo suka kar6i adnan cikin gata da so , Sophy tayi murna da dawowar adnan ,don zuwa wannan lokacin dakin kwana ya gagari safiyya saboda makircin kishiya ,saidai ta kwana a katafaren zauren gidan ,ta kulle kanta in asuba yayi maza zasu wuce masallaci ta cigaba da galantoyi a tsakar gida,ta Zama tamkar almajira ,abinci saidai a bata sauran da mutane sukaci suka rage,amma sai gashi dawowar adnan ya karya duk wani qulli ta koma tayi retaining position dinta kamar da,saidai sarki yace adnan bazai komaba,shima ya kamata ya fara koya masa sha'anin Mulki,don haka akayi masa transfer ya dawo school anan madina.
***
Bayan dawowar quliya gida da kwana uku
Yina zaune a living room dinsa yina kallon CCTV system dinsa ta laptop ,yina kallon jaguljagul din kishin matan gidan wani yayi dariya wani yayi tunanin hanyar gyara,dama kuma don haka ya maqala batareda saninsu ba
Abun tsoro!
Cacan bakine ya sarqe tsakanin adama da Abike akan driver mai Kai yara makaranta,wai saidai akoma Kai su Irfan a baya tunda su manya ne,ana shiga hakkin yaran Abike ,Ana kaisu makaranta late.aikuwa Haj. Adama ta buga qasa akan lallai baza a canja tsariba ,don drivern ba bawan gidan yarbawa bane ba
"Au bawan gidan nufawa ne ko? To wallahi sai an canja tsarin nan tunda dai dukiyar ubansu ne ba Na uban wani ba"
"Me kike nufi ? So kike kicewa yarana shegu ko yaya? "
"Zancen shegu ai kin fini sani tunda duk dubaran tare muke shirya wa"
"To aini Na gode Allah tunda ni gidan marayu Nike zuwa in samo yaran ,ba dakko kwarto nikeyi ba,yina cinmun tsuliya ,a haka nayi ciki Na kawo shegiya matsayin er quliya ba"
"Ahayye to se Mene? Da inje Ina rainon yaranda ba nawa ba ai gwara in San dan masoyina Na haifa yasha nonona,ba yaran wasu ba arnane ko musulmai oho "
"Nadaiji ba daukan zunubin zina inada aurena kawai saboda kwadayin abun duniya ,gado don shi baya haihuwa..."
Da sauri ya yi pausing videon ,wani irin zazzafan hawaye Na fita masa a Ido,a take yaji ya tsani duk matansa ,wani ziciya ce take raya mashi ya sakesu duka amma da yayi tunanin yaran ,ya zasu tsinci rayuwar su? Kurum sai ya qyale wannan amma yasa a ransa bashi ba matansa har abada , abun nufi su din ba matansa bane ,kuma duk hidimar da zai yi masu ya daukeshi a matsayin sadaka ,amma dole zai qara aure don bazai iya rayuwa ba mata ba
Da wannan tunanin yaje ya auro Nnenna Wanda take nacin sonsa kuma Account ne a wajen aikinsu,don har alaqawari tayi masa akan indai ya aureta zata musulunta.
Amma da yike batada cika alkawari da ta shigo sai ta ki musuluntan. Saima qaton plaza da ta bude tana Satan masa kudi tana dibga kaya ta saka saurayinta ,matsayin manager din wajen,ashe dama ta auresa ne saboda taji labarin yinada kudi kuma bayida banki ,don haka tabbas a gida yike ajiyan kudinsa.
Da quliya ya gane hakan ,sai ya sa aka tottone tsakiyar bed room din kowaccensu ,ya zuba mata maqudan arziki ,da yasan zai sustaining din rayuwar su Dana yaransu da suka roro koda bashi,da rai.don a gaskiya ya fara tunanin komawa saudiyya dingurgum da Zama don ya Lura matan Nigeria basuda kirki Sam,dukkansu yarigada yayi masu kudin goro,.
Kuma bai bari wata tasan wainnan tsubin kudin yina dakin er uwarta ba,yayi hakan dan su samu peace of mind a barshi ya zauna lahiya,suyi tunanin kowacce itace yardajjiyar mijinta,amma sai kuma kowacce akalanta ya koma yanda zataga bayansa don ta nade dukiyar ita daya...gane hakan yasa ya daina cin komai a gidan don yasan zasu iya zuba masa guba ,amma ya yanke lokacin rabuwarsa dasu da zaran ya aurar da yaransu ,don sune vayaso su hofinta .
...Saidai Ana cikin hakan ummi ta 6ullo rayuwarsa ,wannan ya canja masa lissafinsa Na komawa madina amma ya maida Nigeria tamkar zuwan week end