← Book details Hamshaƙiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 18

Sashe 9

Hamshaƙiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

🖊️🖊️🖊️
[6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕🏻*

*NA*

*HALIMA ABDULLAHI K/ MASHI*

_PAID BOOK_
_Kuɗin karatu ₦600_
_Account number 0700549935 Halima Abdullahi Access Bank a turo shaidar biya ta wannan number 08140004302 ko katin Mtn_
_Phone 08140004302_

*DOKA*
_Ban amince wani ya É—ora littafin nan a wani Social media ba,ko a maida mini shi Audio ba tare da iznina ba yin haka daidai yake da fuskantar fushin hukuma. A kiyaye_

*Masu son a Tallata masu hajarsu suyi magana ta wannan number 09068032427*

*Free Page 6*

Muna shiga ƙofar da ya buɗe wani ƙamshi ya bugu hanci mu wanda baza mu iya tantance ƙamshi abinci ne kona turare ba, na raɗawa Jamila cewa ki kama kanki sosai. Ta ɗaga kai alamun taji. Mun isa wani falon da na zata nan ne sai muka ga ya ƙara buɗe wata ƙofar,muna shiga wani falon ne na alfarma da ya ɗara wancan. Ya nuna mana kujera,ku zauna a nan ku jira in faɗa mata.
Ya shiga wata ƙofaar, da sallama Hajiya ta ɗago ta dube shi,tana riƙe da wani ɗan littafi na addini,a hannunta ya je ya tsugunna,ga su sun iso na ce bari in sanar da ku. Ta aje littafin "Su shigo mana, ya ce amma Hajiya sai dai fa bance nan ɗin gidanmu bane,zan sanar da su Juma yanzu don Allah kar su yi wata alama da zata nuna cewa ni ɗin na gidan ne. Hajiya ta ce "Kasan ban iya ƙarya ba,amma zan iya hikima. Yace hakan ma ni ne da godiya Allah ya ƙara nisan kwana. Ya nufi gurin su Juma a kicin ya faɗa musu cewa kar su nuna cewa shi a gidan ya ke, gaban baƙin nan da za su shigo. Juma ta ce "To Allaji uban ɗamina. Ya zo yaje falon da su ke zaune,ya ce ku zo muje. Ya dubi Baby,"Dan Allah zan nemi wata alfarma a gurinki," Ta me? Ta tambaya cikin sauri da faɗuwar gaba. Yace duk abinda Hajiya ta tambaye ki dan Allah ki bata amsa ta gaskiya, kuma karki fusata. Nace To,,Yaya insha Allahu. Gabana ya tsananta faɗuwa bansan dalili ba, muka cusa kai cikin falon ƙamshi sanyi da laushin kafet ɗin da na taka shine ya ƙara sani a fargaba. Ko ban ɗaga kai na kalli ko ina ba,nasan falon na alfarma ne, na kalli inda aka amsa mana sallama kyakkyawar dattijuwa mai matuƙar kama da Yaya sai dai ita fara ce tas,kuma kamala da isa da bunƙasa sun bayyana kansu a gareta. Ta bimu da kallo tare da furta sannunku da zuwa cikin maganar hakiman mata. Yaya ya tsugunna a gaban ta ta gefen dama yana faɗin Hajiya ga su nan. daidai lokacin da ta nuna kujera tana faɗin ku zauna mana. Sai na zube ƙasa kusa da ita kamar yadda na ga Yaya ya yi Jamila ma tazo muka fara gaisheta cikin mutuntawa. Ta zuba mana ido,cike da mamaki ta ce, "Shamaki naga wasu 'yan tsintsayen yara,raino za kayi ke nan? To wacece a cikin su. Ya nuna ni. Na sake sunkuyar da kai. Tace to madalla. Ya miƙe tare da faɗin "Ina dawowa Hajiya. Tace to ba laifi." Wata Dattijuwa ta shigo da sallama muka amsa tare da gaisheta,ta amsa cikin fara'a tace Hajiya komai an kammala. Ta ce "To ku kawo musu abinci da na taɓawa." Wannan Dattijuwa tare da wasu mata biyu suka shiga jera kayan marmari da kayan fulawa dangin cincin harda alkaki,sai kuma can ga kaji da wata shinkafa ƙamshi kuma tuni yawuna ya tsinke amma ko kallon gurin banyi ba, ta ce "Ga abinci sai kunci ko?" Jamila ta kalle ni wadda nasan ta ƙosa ayi mana ta yi,da ido na nuna mata 'a 'a sannan nace, Alhamdulillah Hajiya mun ƙoshi. Tace aikuwa dai ba a zuwa gidana afita haka dole sai anci wani abu, kuma ansha wani abu. Nace To na tashi na ɗakko robar ruwa na dawo na zauna,ta ɗakko wani ɗan faranti da dabino manya jajir tace, "Ci wannan tunda duk can bakiga abinda zaki iya ci ba." Duk da dabino bai fiya damu na ba, sai na saka hannu na ɗauki guda ɗaya na soma ci sannan na buɗe ruwan na kurɓa. Ta kalli Jamila ke jeki can kici duk abinda ki ke da shi'awa a can. Ta tashi taje ta zauna kusa da gurin sai ta ɗauki alkaki. Hajiya ta dube ni. "Ki cinye dabinon tas tunda kin ƙi cin komai." ban yi magana ba. Na dai kuma ɗaukar wani. Tace "Ina ne asalin garinku?" Nace Ummanmu 'yar asalin Sumila ce, shi kuma Babanmu ɗan Rano ne. "Kece ta nawa a gidanku?" Nace ta fari ce ni sai wannan ƙanwar tawa."Ai ƙanwarki ce! Ina ƙawayenki kike tafiya da ƙanwarki?" Na sunkuyar da kai, bani da ƙawa ita ce dai mu ke komai tare. Ta ce "Ya yi kyau haka,bayan ita kina da wasu ƙannai?" Nace akwai biyu maza ƙanana ne. Ta ɗanyi shiru, can tace, "Ina sauran dangin ku suke?" Na Babana unguwarmu ɗaya akwai kuma wansa da ƙaninsa da kuma ƙannensa mata duk suna unguwanni suna aure, dangin Ummanmu kuma suna Kurna. Ta ce "Madallah. Amma iyayen ki sun kyauta da suka bari kuka kawo min ziyara duk da cewa ba wata magana mai ƙarfi taje musu ba ." Yadda ta yi wannan maganar sai naji kamar habaici, sai nace, Ai basu san zamu zo ba, gaida Kakarmu zamuje shine muka biyo. Na kalli Jamila wadda ta zuba min ido kamar ta kai min duka dan haushi nasan tunanin ta me yasa zan yi wannan maganar, ni kuma nasan dalilina na faɗin hakan. Hajiya ta yi ɗan tsam tana kallona, sai ta yi ɗan murmushi ke nan ƙarya ki ka yi wa iyayenki ko? Kin yi wa iyayen ki ƙarya wazai sha?" Na sunkuyar da kai, kamar shirin Film sai naga hawaye sun soma ciko idanu na, cikin shashshekar kuka nake faɗin ban so yin hakan ba, kuma abin ya dame ni, dole inna koma in nemi gafararsu amma Yaya ne yace shi yana son in zo in gaishe ki, shine muka fake da zuwa gidan kakarmu. Jamila ta ce Innalillahi Yaya Baby meyasame ki haka?" Nasan haka zaki yi wallahi ba zan zo ba, ta aje ballin alkakin dake hannun ta ta koma gefe cikin fushi. Hajiya ta yi ɗan murmushi "To ai kamar ba a yi wani abin kuka ba ko?" Na numfasa ban kyauta musu bane shi kuma Yaya zai ga kamar ban ɗauke shi da muhimmanci bane. Na kalleta bayan na sauke ajiyar zuciya. Ta ce "To shi Yayan da kike faɗa wanene?" Cikin mamaki na tsura wa gefe ido, tsabar rainin hankali ne, ko kuwa dai da gaske bata fahimci wa nake nufi da Yaya ba.Na numfasa wanda ya kawo mu. Ta taɓa baki, "Au wai Shamaki ne Yayan? Kuna da wata dangantaka ne ta kusa ko ta nesa?" Na girgiza kai, babu, kawai bazan iya kiran sunanshi ba ne kai tsaye Hajiya. Na soma ƙosawa da tambayoyin ta ko ita ce uwar shi ai bazata min Wannan maganganu ba. Wata zuciyar ta ce shi yasa ya baƙi haƙuri tun kafin ku shigo. "Menene matsayin karatun ki?" Wata tambayar ta kuma katse tunanina Muna jarabawar kammala Sakandire zamu gama jibi. "Kina da burin ci gaba?" insha Allahu in har Yaya ya amince kuma yana da halin hakan ina son ci gaba da karatuna. Ta yi ɗan murmushi Ki daina kiranshi da Yaya ki faɗa mishi wani sunan ko dai ki kira shi da sunan sa. Na yi shiru cikin mamaki. Ta nuna min ɗan farantin Dabino. "Akwai buƙatar ki cinye wannan dabino." Na kalla na ci guda uku. Sai naji kamar zan zargi a wani abu a cikin dabino. Nace ya ishe ni ne Hajiya ban cika cin dabino ba. Ta maida kallon ta ga. TV kamar ba zata kuma magana ba, na kalli Jamila ta min alamar wai inzo mu wuce.
Chapter 9 · 0% Book details