Sashe 13
Hamshaƙiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kan hanya. Nace to, amma kai ai zamu iya tattauna maganar aurenmu ko? Ya ce "Sosai ma kuwa." Nace to yanzu faÉ—a min yadda aka tsaya. Yace Abba sunce za su yi shawara, domin shima Wan Abba cewa ya yi tunda na ce abinda ake dashi a kawo ki ba matsala to na shi ganin gara a yi bikin kawai. Shine aka ce a shawarci Ummanki. Nace to Umma tana kiran shekara. Yace Allah dai ya zaÉ“a mana mafi alkhairi. na ce ameen. Yace "Ni ma dai ya kamata in tafi, da har zan wuce, sai kuma nake tunanin ban muyi sallama ba." Nace yanzu sai yaushe? Yace, "Bazan sa lokaci ba gaskiya tunda an bani ke. amma kowane lokaci za ki iya gani na. Zan bada waya a kawo miki saboda za mu ke yin magana akai akai. Nace "To É—an Allah kar ka manta da Ni kaji. Ya yi yar dariya sannan ya yi Æ™asa da murya, ashe zan mantà kai na. Ina mugun sonki Baby. Cikin farin ciki nace ina sonka Aliyuna. Sai kuma naji kunya na saka hannu na rufe fuskata. Muryar Abba naji yana cewa "Malam Aliyu bari in baka saÆ™o ka faÉ—awa magabatan na ka.". Aliyu ya ce to shiga gida sai kin ga saÆ™on na ce to ka gaida su Hajiya da su Anisa. Na laÉ“e a soro ko zanji me za su faÉ—a amma banaji. Dole na shige ciki Umma harta kwanta na leÆ™a É—akinta ina yi mata sannu, ko dai ta yi banza da ni, ko kuma ta yi bacci. Na fita na je na saka tuwo na É—ebi ruwa a kofi na shiga É—akinmu na zauna ina ci. Jamila ta shigo da shirin baccin ta, tace Yaya Baby ki sa su Jafar su yi fitsari in kin gama, yau duk ni na yi aikin ki a gidan nan." Na ce me kika yi nawa da zaki faÉ—i haka?" Ta ce "Ni na tace gasara kuma na kammala komai." Na yi 'yar dariya. Ni da zan tafi ma gidan mijina daga can zan ke zuwa ina miki akin? Jamila ta yi gialala ta na kallona,sannan ta ce, gaskiya Yaya Baby abinki ya soma wuce tunani, kuma ko a jikin ki. Na kalleta Ni Kuma ke kike bani mamaki, ko da yake na miki Uzri bari ki faÉ—a soyayyar za ki gane abinda ya same ni. Tace haka É—azu ki ka yi ta rera wakokin soyayya a gidan nan ke da ko wani ya yi waÆ™a sai kin masa wa'azi." Na suÉ—e robar ina lashe hannu, na ce duk ba wannan ba, faÉ—a min abinda su Umma suka yanke da na fita. Abba ya tsorata da yadda ki ka yi,Ya ce Umma ta yi haÆ™uri ayi bikinnan a haka yadda ki ke yi ya nuna kin matsu da aure,abinda aka samu a kai miki. DaÆ™yar Umma ta yarda domin har abin sai da ya kai su kamar za suyi sa'insa, daga bisani Abba ya lallasheta. Amma tana ciki da ke,zaku gauraya da safe. Na É—anyi jim har ga Allah ni banga abin laifi ba amma dole in ke yin shiru dan in samu zama lafiya. Na dubi Jamila wadda ta kwanta tana Æ™okarin rufa. Na ce amma ya suka yi matsaya a Æ™arshe. Ta É—ago kai zakiji a bakin Umma da safe, shawarar da zan baki kuma ita ce, ki bawa Umma haÆ™uri, sannan ki daina magana sam in ana zance.Na miÆ™e tare da faÉ—in zan kula sosai. Da safe Umma bata amsa gaisuwa ta ba,to nan ne fa hankalina ya tashi na soma kuka ina bata haÆ™uri, tace haÆ™urin me zaki ba ni, ni a su wa É—anwake a Otal ba dai É—a namiji bane Baby Allah ya bada sa'a." Na ce Umma wallahi ni fa bansan me zance miki ba ne, kiyi haÆ™uri na tuba don Allah.Abba ku yi haÆ™uri ni ban san cewa ba a magana ba. Ya ce tashi kije ki yi aikin ki ta haÆ™ura. Na fita ina sharÉ“en kuka. Ina jiyo Abba yana baiwa Umma baki, tare da nuna mata cewa Æ™uruciya ce,kuma mu godewa Allah Salamatu da ya bamu yara masu kamun kai da nutsuwa, duk tsukunnan yaban su ake Allah ya sa musu albarka karki fusata Allah shine mai rufin asiri abar auren a lokacin da aka sa shi. A ranar wani matashi ya yi sallama muna Islamiya anci sa'a Abba yana gida . Suka gaisa yace Aliyu ne ya aikoshi da saÆ™o ya baiwa Amira. Abba ya amsa waya ce sabuwa a kwali sai layin da kuma kati wanda ya ce ace in ta saka ta kira shi. Abba ya ce to insha Allahu za a bata, taje islamiyya. Na yi murna sosai lokacin da muka dawo. Umma ta É—an saki jiki harma ta karÉ“i wayar ta sa albarka. Tace ki kula irin wannan ta shafawar ba wuya ta fashe. Na ce to. Na saka layi na sa katin na shiga É—aki na kira wata Number É—aya daga cikin lambobin da ke jikin wani kati da ya sako a ciki kwalin. Wani ya É—auka, nace Aliyu nake nema. Yace mai gida baya nan ya yi tafiya. Nace Shamaki fa na ke tambaya? Yace nima shi nake magana ya tafi China É—azu. Na ja tsaki sannan na kashe waya, ina faÉ—in Ni Aliyu na ko filin jirgi baya zuwa bare wata China. Na sake É—akko katin don in duba wata Number. Sai naga ya yi wa wata lamba alama da biro a Æ™asa ya rubuta ki kira wannan layin. Cikin sauri na saka na kira. Ya É—aga "Baby zan kira ki kinji?" Na ce to Yaya na gode, ina jira fa ka kira ni fa. Yace karki damu. Haka dai abubuwa suka ci gaba da tafiya, iyayena suka tada hankali gurin neman kuÉ—in da za a yi min kayan É—aki aure saura sati uku da 'yan kwanaki. Umma ta sanar da Baba har Kurna taje,Baba tace Allah ya sa hakan ya zama alkhairi, abinda za ayi yanzu zata sa akama Awakinta guda biyar a saida su, a zo a karÉ“a a sai min kayan kicin kuma zata sanar da sauran dangi. Shi kuma Abba an sanar da dangi sun nuna murna amma da suka keÉ“e sai Æ™anwar Babanmu Saratu wadda dama basa shiri da Umma tace "Shi Abbana su Babyn da ya kama ya sa rana sati huÉ—u kila ya tanaji kuÉ—in da zai yi mata kaya da na abinci da za a dafa. Dija tace Nima dai na yi mamaki muna neman gudunmawar sauka mu bashi, shi kuma ya na tataro aure abinda Allah ya ba ni shi zan bada. Saratu tace ita matarsa dan hauka gata da tsohon ciki shine ta yadda da wannan gangancin koda yake Æ™ila ma ita ce tace a saka dan a ce yar ta ta riga 'yay'anmu aure. Dija tace ko wane kwashe ne kuma zai É—ebi wannan yarinyar kamar taÉ“arya oho. Matar waliyin ta taÉ“a baki tare da faÉ—in jiya da na shiga murna ai na ga 'yar da wata Æ™atuwar waya wai saurayin ya aiko, shiko Abban su Zuhra sai rawar kai shi ga waliyyi nace dubu goma dai ya baka abikin Ummi dan haka sai ka nemi shabiyu kar kaji ance waliyyi ka fara neman siyan gado. Suka sa dariya gara dai ki faÉ—a masa dan ga sunan riÉ—a riÉ—a duk wadda ta samu shima hidimar ce a gaban sa. Haka suka yi ta maida zantuka ta re da alwashin zura ido su ga abin da zai biyo baya. Har kwanaki biyu ina jiran kiran Yaya, Ni kuma inna kira bata shiga. Hankalina duk ya tashi amma babu dama inyi maganar sai Jamila kawai inna faÉ—a mata sai ta ce bani da aji wai in jira ya kira ni. Ranar kwana na uku ina zaune a kan tabarma a tsakar gida ina rubuta sunayen waÉ—anda zan kaiwa katin sauka 'yan uwa da yan makarantar bokonmu. Jamila na ke kira ta raka ni. Umma tace to kuma yaushe za ki kai na 'yan Kurna? Nace sai mu kai ranar Lahadi ko asabar tunda bata da Boko sai muje. Umma tace hakan ya yi saura ku kuma zuwa wani gidan nace imsha Allah babu inda zamu Æ™ara zuwa. Wayata ta soma kiÉ—an na É—auka da sauri. Sanyin zuciyata, haka na rubuta a lambarsa. Na tashi na shiga É—akinmu. Na É—auka da sauri. Cikin shagwaÉ“a na ce sanyin zuciyata shine ka Æ™i kazo ko? Yace "My Baby ki yi hakuri tafiyar gaggawa ta taso min." Nace na kira wata lamba aka ce ka tafi China . Yace a a Kaduna na je ina can har yanzu aka wasu kayanmu. Nace to Allah ya tsare shiyasa nace ni Aliyuna ko filin jirgi bana zaton ya taÉ“a zuwa. Ya yi dariya "Na taÉ“a raka maigada ba so É—aya ba ma. " Nace Allah ya sa kai ma wata rana in raka ka. Yace "Ameen Allah ya sa mu hau jirgin tare. Na ce ameen. Ya ce "To ya ake ciki menene labari?" Nace wanne zan baka?" Yace "Sabo wanda ya ke tashe." Na ce kati zan kai in raba na sauka in Jamila ta dawo. "To kuma na bikin yaushe za araba?" Ya katse ni. Kaga karka wani damu da katin Biki duk kashe kuÉ—i ne, karatun saukaramu asabar ne É—aurin aure Lahadi sai a faÉ—awa kowa a haka. Yace "TaÉ“ aurenmu ace ba kati Baby ko bashi ne ni zanci don in buga mana katin biki." Don Allah karka ci bashi a zo ana sallama da kai. Na faÉ—a cikin shagwaÉ“a. Yace "Ai misali na yi. [6/16, 19:58] Ummi Tandama😇: *HAMSHAƘIYAR UWA🧕ðŸ»*