Sashe 4
Hamshakiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Mamakin kansa ya ke yadda ya ƙosa dare ya yi yawan murmushin da ya ke in ya yi shiru ya sa yaran kantin suka soma tsegumin cewa maigida ya faɗa soyayya, musun da suka yi ya sa ɗaya daga cikin yaran mai suna Ɗahiru ya ce bari ya gwada shi. inhar haka ne zai gane. Ya kunna waƙar Hamisu Breaker ta soyayya. Yaje ya zauna a bakin Office ɗin yana ci gaba da shi'anin gaban sa. Daga ciki kuwa Shamaki ya yi tsam da ransa yana sauraron yadda mawaƙin ke yin falsafa akan so, sai kawai ya ƙwala wa Ɗahiru kira, ya amsa ya shigo cikin girmamawa yace "Gani Alhaji." Wai ku bakwa rabo da jin wakane duk da ita wannan naji ta yi daɗi da ma 'ana, amma waye ya yi ta ne, tura min ita a waccan wayar in yi wani nazari a kanta. Ya ɗauki wayar ya fita yaje yana basu labari suna dariya. Ranar haka ya yini jin waƙar. Da yamma ya kira Malam Bala direbansa ya ce a wanke mota zai fita bayan Isha'i. ya kuma fara lissafin zai bi ta Zeena Store ya kwashi alawoyi yaje Zeena Factory ya haɗa mata kayan ƙwalam na Snacks. Kamanta gurin wa zaka kuma wane matsayin kake a idon ta? Zuciyarsa ta jeho masa tambaya. ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce sai dai in nemi ɗata ko yalo? Ɗan tsaki ya saki sannan ya yi maganar da ƙarfi Ayaba da Lemo zan siya. Hassan dake cikin Office ɗin yana rubuta wani rasit ya ce "Karɓo wa za ayi Alhaji?" Ya dubi Hassan me nace? Yace,"Naji kana maganar Ayaba da Lemo." Ya yi ɗan tsaki eh da za a karɓo ne amma bari sai na fita sai in siya kawai.
Nikam kafin Isha'i na shirya tsaf, ba sallah zan yi ba don haka na kame ina jiran zuwansa, gabana kuwa sai faɗuwa yake ina ayyana yadda zanji idan mun kasance muna hira,ina ta baiwa kaina shawarar ya kamata ace ina zaɓo kalamai inzan furta masa,sannan kuma kar inyi masa magana da irin muryar da nake yi wa kowa hakan zai sa in ƙara birge shi. Take na gamsu da hakan,kuma na yarda shi na musamman ne.
Shamaki ya wahala kafin ya samu kayan da za su nuna shi a talaka,suma dai yadine fari mara nauyi, yanada mugun tsada amma ba kowa zai iya gane hakan ba sai wanda ya san kaya. Ya zube wayoyinsa guda huÉ—u a kan gadonsa, sannan ya saka mai boturan wadda ya sawa sabon layi domin ita kaÉ—ai a alajihu agogo da zobe na azurfa duk ya zube su. Ya nufi sashen Hajiya.
Ta ƙare masa kallo sanna ta amsa gaisuwarsa. Ya ce zanje gurin Rabi a ne kamar yadda na sanar da ke tun shekaran Jiya. Ta ce "Na fahimta,kaje Allah ya bada nasara,kuma ka ce ina gaisheta. Sannan ka tabbata ka sami zuciyarta a yau,domin na lura kana matuƙar sonta. Allah ya yi muku albarka gabaɗayan ku." Ya ce Ameen sannan ya miƙe ya fice da sauri. Ta bishi da kallo a fili ta furta akwai matsala ya kamu da yawa, ni da nafi son ya samo wadda ta fi son sa dole inyi wani abu.
Ya dubi Malam Bala yace, in ka isa gurin masu Lemo na ɓawo za ka karɓo. Da suka isa ya rasa na nawa ya kamata ya siya yace Malam Bala ga dubu biyar su yi kashi biyu. Da aka kawo ya ga da yawa yace Malam Bala ka dauki kashi ɗaya. Sai da suka gota lungun sannan ya sauka,yace ka je zan kira ka nan da awa biyu. Ya taka da ledoji biyu a hannunsa ya dawo ya shiga lungu.
Jafar ya shigo da ledoji suna rinjayarsa, yace Umma wai gashi inji wani mutum wai yace Yaya Baby taje. Cikina ya juya da sauri na É—auki buta zan shiga banÉ—aki, Umma ta ce "Ke dakata lafiyarki da tun É—azu kuna zaune sai da yazo zaki tarki shiga banÉ—aki?" Nace wallahi Jafar yana faÉ—a sai naji cikina ya juya, na shige da sauri. Ina jiyo Jamila tana tsaki tana mitar "Yanzu da wari zaki gunsa?" Na fito na sake shafa turare sannan na fita na samu har Jamila ta shinfiÉ—a masa tabarma ta aje masa ruwan fiyawata.
Cikin girmamawa na gaida shi, na kuma tambayi Hajiya da yara. Yace tana gaida ni kuma duk suna lafiya. Nace shine harda wata ɗawainiya haka? Ni fa karka matsawa kanka a irin wannan yanayin ba sai ka min wata ɗawainiya ba. Ya ce "Karki damu, ina da halin yin hakan ne, yanzu ki bani labarin soyayyata. Na ƙosa mu soma musayar ta ni da ke, domin har na soma zama wawa ina kasa jurewa tunaninki." Nace koda bansan so ba, na tantance kai na musamman ne, duk wani kai kawo nawa kana zuciyata kuma na kasa gano aibunka, zuciyata tana faɗa min cewa in maka uzri kuma in amince ka zama mijina. Na gamsu sosai da shawarar zuciyata kuma na amince ka zama mijina in ina gidanka sai ka koya min soyayyarka. Na kai ƙarshen maganar tare da rufe ido. Ya ce "Alhamdulillah wannan yanayin da ki ke ji shima alamun so ne Baby, yanzu sai mu yi maganar aure, zuwa wane lokacin ya kamata mu zama miji da mata?" Nace ai wanna da su Abba zaku yi magana. Ya numfasa "An saka ranar da zakuyi walimar sauka?" Nace har an fitar da katin manyan baƙi an raba tun wancan satin. Na mu sai wannan satin insha Allahu zan baka ina fatan zaka zo ka ga karatunmu? Ya ce "Ai ina tunanin a haɗa bikinmu da saukar ki... Kai! Na katse shi. Na yi ƙasa da murya. Saura sati biyar fa ayi walimarmu yaushe aka shirya? Ya numfasa "Wane irin shiri kike magana a kai?" Na sunkuyar da kai, yaushe ka kawo kuɗi har aka sa rana, kuma ga maganar lefe su Abbanmu ga maganar kayan ɗaki abin da za a ci abiki, kaga duk abin dubawa ne. Yace "Kinyi gaskiya, amma zan ɗauki wani kuɗin dashi na zan bada kuɗi cikin satin nan a kawo dubu hamsin, sannan nasan dai ko ba lefe zaki aure ni ko?" Har a zuciyata zan iya hakan Yaya, sai dai matsalar iyayena basu da halin yimin kayan ɗaki a cikin wata guda, yanzu ma suna ta abinda zasu fiddani kunyar walimar saukar nan da zamuyi. Yace to ke da me za kuyi a saukar? Nace walima ce kawai a gida, ya ce nawa zaki kashe... Na katse shi da A a bazan ɗora maka nauyi ba, kar ka rene ni da haka, kabari in saba da yanayinka na asali,ka koya min yadda zamu rayu a lokutan akwai ko na babu. Ya ɗaga hannunshi ɗaya tare da faɗin kinga dakata kiji. "Inada shine shiyasa, kuma ba roƙona ki ka yi ba, kawai ki faɗa min nawa zai ishe ki ko inje in ɗauki kuɗin da zan kawo miki na aure inyi gaban kai na da su.". Na ce Umma za su min faɗa, duka yau ne zuwan ka na biyu fa, kuma... "Kuma me?" Nace shike nan dubu uku ne. Ya ce "To zan baki sai kuma me?" Na ce shike nan. Yace "Ankon walima da hijabi Lemo da kalanda kinsan dai nima na taɓa saukar nan nasan ya ake yi. Na ce ai duk Abba da Umma sun sai min. Ya ce to shike nan zan kawo miki dubu uku jibi mu koma kan maganarmu in turo a kawo kuɗin ko?"Nace bari in faɗawa su Umma, yace don Allah da kin shiga ki sanar musu,kuma zan kira komai dare yau inji ko sun amince." Na ce to shike nan, amma nima zan nemi wata alfarma a gurinka. Ya tattaro hankalinsa gurina "Faɗi da sauri in har zan iya kin samu." Ina son in ci gaba da karatu ko da makarantar koyon aikin jinya ne. Ya yi shiru can yace "Bazan miki alƙawari ba,saboda wasu dalilai amma mu aje maganar zuwa gaba." Nace to shike nan. Ya kwai kwayi muryata "Na gode Babyna." Na sa hannu na rufe fuska ta. Yace to bari in tafi, nace yau naga baka zo da Kekenka ba? Ya ce tayar ce ta yi faci ɗazu ina hanyar dawo wa daga kasuwa, na ce to Allah ya tsare ya ce "Ameen muka yi sallama cikin shauƙi da ƙauna.
Na samu Abba yana ta faɗa wai ko dai nice nace wa Aliyu zan sha Lemo domin yaran zamani ba abin yarda bane. Na zauna na ce Abba wallahi ban roƙeshi ba yanzu ma dan baku san ya mu ka yi da shi ba ne, cewa ya yi in faɗa masa abinda zan kashe a walima lokacin sauka zai bani kuɗin nace a a ya bari shine ya ji haushi. Umma tace "Abban Baby na faɗa maka ko Jamila bazata yi roƙo ba, bare kuma Baby, duk da ba 'a shedar 'yan zamani akwai abinda zaka shedi ɗanka dashi, yace "To Allah ya muku albarka dukanku har da ke Ummar ta su,domin tarbiyyar ki ce, shi kuma Allah ya saka masa da alkhairi ya jiƙan magabata." Muka ce Ameen ya ce "To sai a yanka aba kowa, ku rage akai gidan Yaya ba ma ci mu kaɗai ba." Jamila ce me yankawa Ni kuma na yi zugum ina tunanin ta ina zan fara sanar da iyayena saƙon shi. Umma ta ce, lafiya ke kuma ai Abban na ku ya gane ba roƙarsa aka yi ba. Nace ba wannan ba ne, haka ya ce wai a satin nan za a kawo kuɗi, kuma wai in kun yarda za a yi biki tare da walimar saukarmu... Tarin Umma ya sa nayi shiru ta ƙware da ayabar da ta ke ci, na tashi da sauri na kawo mata ruwa ina yi mata sannu.Abba ya taso shima cikin sauri yana mata sannu. Bayan ta samu kanta tana maida numfashi tana magana, "Baza a yi gaggawa ba gaskiya sai anyi bincike, kuma bamu da halin biki a wata ɗaya." Abba ya ce ki daina magana kin ƙware ki yi shiru tukunna. Sai da ta samu natsuwa sannan Abba ya ce, "Inda haka zata samu zanfi kowa murna ace na aurar da Baby a ranar saukar ta. To amma hidimar da yawa ga haihuwarki ko yau ko gabe." Umma tace, ta haihuwa mai sauƙi ne, ba taron suna zanyi ba Allah dai ya sauke ni lafiya. Abba ya ce "Ameen, dama tun farko ya faɗa min aure ya zo, sannan ya taɓa aure kinga dole ya buƙaci aure da wuri, ina ga abinda za a yi mu amince su fara kawo kuɗin sai mu yi maganar da ta dace." Umma ta ce to shikenan ke sai ki faɗa masa in yazo. Na sunkuyar da kai na ce yace infaɗa masa a waya zai kira a ta Umma in yaje gida. Abba ya ce to. Sai ki sanar dashi. Da wayar Umma na shiga ɗakinmu ina ta jiran kiransa har bacci ya kwashe ni.