← Book details Hamshakiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 18

Sashe 12

Hamshakiyar Uwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya ta kalli Shamaki, "Ƙarfe nawa zasu je su kawun naka?" Ya saki fara'a sai da dare in kowa ya gama sabgar sa bayan sallar Isha'i. Tace "To nawa za a kai?" Yace dubu Hamsin kinsan bana son ta san komai da wur ne. Tace "Akwai gejin da dole su sani, tunda za su yi bincike." Yace haka ne,amma kafin lokacin na samu abinda na ke so. Bayan sallar Isha'i Shamaki ya kwashi su Ƙanin Hajiya da kuma ƙanin mahaifinsa sai limamin masallacin gidansu suka nufi kai kuɗi, saidai tun a hanya ya ce musu ba zai ce suyi ƙarya ba, amma yana son kar su nuna shi mai arziki ne ya faɗa masu komai a taƙaice da kuma dalilin sa. Suka ce insha Allahu za su yi yadda ya ke so. Ya ɗauki waya zai kira layin Ummarsu. Sai lokacin yaga miss call da yawa, ya yi mamakin ina ya jefar da wayar har da Baby ta yi masa wannan kiran haka. Ta ɗaga wayar ya ji muryarta can ƙasa, ta gaishe shi, ya amsa tare da tambayar lafiya ya ji muryarta haka. Tace banajin daɗi ne, yace ashsha sannu, kin sanar da Abba mun kusa zuwa kuma nan gidan zamu zo? Ga mamakin sa sai ya ji tace dan Allah kun taho?" Ya ce kinsan abinda za ayi wasa daban ya ke ko?" Tace dama kiran da nake maka kenan ɗazu dan in faɗa maka Abba ya ce gidan wansa za a je,amma babu nisa daga nan gidanmu bari in kira Abban a waya ya fita yanzu." Yace "To faɗa mishi gamu tafe a hanya. Naje da gudu gurin Umma,nace Umma Yaya sun taho da iyayensa. Tace I kon Allah! Wai kuwa Baby lafiyarki ƙalau yau wane irin hali kika canza ne?" Na ce yi haƙuri Umma. Na koma gefe na tsaya. Umma ta ce sai ki kira Abban naku ki sanar da shi. Jiki na ɓari na kira Abba na faɗa masa. Yace gashi nan dawowa gidan. Shamaki ya sanar da su wakilan nasa cewa su faɗawa iyayen yarinyar nan yana son auren ne a lokacin walimar saukar karatunsu. Direba ya sauke su bakin lungun ya tambayi Shamaki ko ya jira su? Ya ce e ka jira mana sai ka kai kowa gida sai ka dawo ka ɗauke ni. Yace "To" Abbansu Baby ya fito ƙofar gida ya tari su Shamaki yace ku zo muje can ayi mai gabaɗaya. Suka juya har shamaki. Ƙatuwar tabarma aka shinfiɗa a barandar ƙofar gidan inda dama anan suke salla kuma ana ɗaukar karatu daga gurin limamin da ke jan su sallar maƙocin shi ne. Annan ne Dai suka gaisa cikin mutunta juna sai Shamaki ya miƙe ya ce to bari ya dawo. Tun da aka ce ga su nan na hau ɓare ɓaren gyaran jiki, ina ta kwalliya sam ban damu da yadda Ummanmu ta haɗe fuska ba. Jamila kanta sai da ta tambaye ni wai kuwa lafiya na ke irin wannan abin? Nace me nayi dan kawai na yi kwalliya laifin ne,kar ki manta da daga yau ya zama mijina,kuma kinsan dai matsayin yiwa miji kwalliya ko? Cikin "Matsananci mamaki Jamila ta ce "Yaya Baby wai ina kunyarki da kawaicinki suka tafi ne?" Wallahi karki fara kice za ki ke irin wannan rawar kan, wai baki lura ma da yadda Umma ta ke jin haushin canzawar ki tun jiya ba?" Na ce ni banga wani canzawa da na yi ba. Kafin Jamila ta ce wani abu Muryar wani yaro ta ratso cikin kunnuwanmu yace ana sallama da Baby, cikin rawar jiki na ɗauki mayafi na zira takalmi ina faɗin Jamila ki kawo mana tabarma. Umma tace "Baby ki zo nan." Na nufi gurin ta a ƙofar ɗaki kan tabarma na ce ga ni. Ta ce, "Kinsan daga Allah ba wani in har baki haɗa min hankalin ki guri ɗaya ba zamu samu matsala da ke, tun jiya sai wani shashanci kike yi girma hauka ne? Wato kin riƙa kin so aure shine ki ke wannan rawar kan, dama rashin samun saurayin ne ya sa ki ka nutsu kamar ta Allah ko?" Na sunkuyar da kai ina faɗin Umma dan Allah ki yi haƙuri ni ban fahimci me nake yi ba,yanzun ma Jamila ta gama min faɗa wai na canza. Na daina Umma. Bari inje yana jira. Ban jira me Umma zata sake faɗi ba na yi waje da sauri har ina tintiɓe. Umma da Jamila dai abin har tsoro ya ba su. Ina fita yana jingine inda ya saba tsayawa, na isa da sauri ina faɗin sannu Yaya da zuwa. Yaya ce "Sannu Baby " Na gaida shi ya amsa. Na ce Yanzu sun can ana maganar aurenmu? Ya ce e na rungume hannuwana tare da ɗan tausaya wa ina faɗin Alhamdulillah Naji daɗi Yaya zan iya bacci in aka ɗaura mana aure kuwa? Mamaki ya hana Shamaki magana,duk da cewa shima fa yana jin wata ƙaunarta a zuciyarsa wadda bazata misali ba. Ta katse mishi tunani da faɗin lokacin walimar tamu za a saka ko? Yace ban sani ba gaskiya haka dai nace su tambayar min." Nace Kaga Yaya, asa hakan wallahi na yafe lefen, kuma kayan ɗà kin ma zan faɗawa Umma ba takura ko? Yace "Sai ki iya faɗa mata haka baza ta ga cewa kinyi rashin kunya ba?" Nace to wai me na ke yi ba daidai ba? Tun jiya ake cewa wai na canza ina ta zumuɗi, kuma ni ina jin wani sonka ne bansan ya zan fassara maka abin ba. Ina samun nishaɗi da jin daɗi ne kawai in naji muryarka, da na kira baka ɗaga ba har kuka fa na shiga ban ɗaki na yi, sai ina ji a jikina kamar zaka fasa. Yace "Gaskiyar magana kin canza gaba ɗaya kamar ba ke ba. Nima dai ina mamaki." Nace to Allah ya sa dai su amince shine damuwata. Yace "Ya maganar walimar ku?" Na yi ɗan jim sannan nace tana nan, amma gaskiya dai zaka zo min ko,duk da masana cewa kana cikin shirin biki lokacin ai na san zaka so ka ga karatu na. Yace in sha Allah zan zo sannan karki saka a ranki cewa dole sai lokacin da muka ce, in basu yarda ba dole mu jira lokacin da suke ganin ya fi." Na ce Ni fa damuwata kada ka zo ka ce ka fasa, wallahi zan iya mutuwa har lahira. Yace Baby in kinga na fasa aurenki wallahi na mutu ne,matsawar ina numfashi bazan fasa ba. Daɗi ya rufe ni, nace Allah na gode maka. Munata tattauna batun soyayyarmu na ga Abba ya zo ya shiga gida. Ya ce bari inje in sallame su, ki koma gida zan dawo nace to. Na shiga gida don inji yadda suka yi. Anan na samu Abba yana ba Amma labari ya zauna genen tabarmar da yake kai har Jamila ta kawo masa abinci. Yana faɗin "Wato Salamatu Allah ya amshi addu'armu ya kawo wa Jamila mijin ƙwarai ba sai mun bincika komai ba sun wanke shi tas. Limamin Unguwarsu inkinji yadda ya ke yabon sa abin zai baki shi'awa ga neman na kansa ga alheri duk sun yabe shi,ƙanin mahaifiyarsa da ƙanin mahaifinsa banda albarka babu abinda suke sa masa. Kuma sun nemi alfarma ko za a sa aure tare da walimar saukar su nace a a saboda yanayi shima kar ya takura kansa muma haka, amma sai suka dage kan cewa gaskiya yana buƙatar aure sosai kafin nan da azumi. Sanna duk abinda ake dashi bashi da wata matsala akai wa yarinyar. Na ƙara kaso kunne inji me Umma zata ce. Sai naji tace, Gaskiya a sa shekara ya yi haƙuri dan shekara kwana ce Abban Baby, bikin 'yar fari ba mu yi mata komai ba ai sai mun shiga bakin duniya. Ban san lokacin da nace Umma zai fasa inhar aka sa shekara,ni dai gara lokacin da yace ɗin dan in ya fasa mutuwa zany.... Saukar ta kalmi da naji a fuska ta shine ya tuna min cewa bai kamata in tsoma baki a zancan aurena da mahaifana su ke yi ba. Na lalle su dan in gane waya jefe ni,sai naga ashe Umma ce, sai huci take ta rasa abin faɗi dan takaici. Shi kuma Abba ya sunkuyar da.kai, sai suka bani mamaki, domin a magabata banga wani abu na tashin hankali ba, na faɗa musu abinda ni nake so ne, kuma dai su iyayena ne wazan fadawa halin da zan samu kaina in an fasa. Sallamar wani yaro ce ta ratsa shirun da gidan ya yi kamar mutuwa ta gifta, Abba ya amsa sai yaron yace "Ance Baby ta zo." Na tashi da sauri na shuri takalma sai da na kai bakin soro sai na waiwayo dan naji a jikina ni suka bi da kallo dama na zargi haka. Na fita ina tunanin ko dai na kuma wani laifin ne? A fili nace garama amin auren in tafi tunda har sun soma gajiya da ni. Na isa gunsa ina faɗin yau Jamila ta ƙi kawo mana tabarma. Yaya sun tafi ke nan? Ya ce "Sun tafi." Nace amma sun faɗa maka komai yadda aka yi? Yace "bakiji ba da Abba ya shigo?" Na ce Banji matsaya ba a maganar na saka musu baki Umma ta jefe ni sai kuma suka yi shiru. Yace "Subhanallah! Me zai sa ki saka bakinki cikin managarsu?". Na ne Yaya Shekara fa Umma ta ce, kuma kai nasan baza ka shekara bada matarka ba. Yace Banda haka Yaya nima ba zan iya ba. Yace "Baby bai kamata ba kina saka baki a maganar manya. Hajiyata tana da zafi in kinje kina mata irin wannan za ku samu matsala wanda hakan zai kawo matsaloli a cikin zaman aurenmu. Ni kuma bana son a ce ni da ke mun rabu, saboda akan Hajiya zan iya komai. To gaskiya in kina son mu daidai ta ni da ke, to sai kin sawa bakinki linzami in manya suna magana babu ruwan ki." Na sunkuyar da kai, insha Allahu na dai na. Nima jiya ne suka fara wannan kukan da ni,amma bana yi, ko yanzu a maganar ka kaɗai suke cewa na canza. Ni kuma banga canjin ba. Ya ce "Nima na gani dan haka ki dawo
Chapter 12 · 0% Book details