← Book details Gidan Yan Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 12

Sashe 6

Gidan Yan Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta kashe kiran, ta maida hankalinta kan Tv, ana wani Film a tashar b4you na mai suna After everything, sosai Film ɗin ya tafi da ita ƙamshin turarensa ne ya sanar da ita Sultan ya fito cikin wasu kananan kaya masu masifar tsada faɗar irin kyaun da ya yi ɓata lokaci ne, kallonsa tayi kana

tace "Fita zakayi ne.?" Yace "Gashi ke faɗa." "Hamm." Kawai tace tare da tashi ta raka shi, suna fitowa ta maƙale shi jikinta, ya riƙe hannunta, saboda sun hango Hajiya Uwani da Farida, wurin hutawa da alama akwai abinda suke shiryawa, Suhana kuwa wayarsa ta karɓa ta shiga Camera tace,

"Hi Baby." Sultan ya juyo ta ɗaukesu hoto, hadda video, suna kissing ɗin juna haka ta rakashi har gaban motar da zai fita, security suka taso ya ɗaga musu hannu alamar shi kaɗai zai fita, saida suka koma rungumar juna, Suhana ta zura harshenta cikin bakinsa suka tsotse juna, kana ya shiga mota,

ya tada suna ɗagawa juna hannu har ya wuce, ita kuma ta juyawa zuwa ciki sai ga motar Kamal tsayawa tayi yana gama parking su Lili suka fito kowace tayi arniyar shiga wacce duk wani lafiyayyen Namiji ya gani sai ya ƙyasa, wani ihu suka saka kana suka rungume juna,

kana tayi musu jagora zuwa part ɗinsu, Afiya tace "Kai Hana gaskiya kina hutawa, ke samu duniya wallahi, dama ace ni ce a gidan nan." Suhana tace "Karki damu wata ƙila kema zaki shigo gidan nan ko ince zaku shigo gidan nan gaba ɗaya!." Lili tace "Kai Hana taya zamu samun gurbin zama a wannan gida.?"

Suhana tace "Ba abin damuwa bane, idan Sultan ya dawo zanyi ma sa magana a baku part ɗaya ku zauna saboda gudun Jamal ya gano inda kuke zuwa kega zai iya bibiyarku har ya gano a gidan nan nike." Afiya tace"Haka ne fa Hana, to ya amarci.?" Suhana tace "Lafiya."

nan suka baje suna hira, Lili tace"Wallahi hana gaba ɗaya Jamal ya rame ya yi wani haske, dogon hanci ne kawai a fuskarsa sai idanu gwanin tausayi yana matuƙar sonki!." Afiya tace "Babu wani so da yake mata jikinta kawai ya keso idan har ba haka bane me ya saka yaƙi aurenta tsawon shekaru, sai moriyar jikinta kawai yake,

kefa Jamal ya yi aure amma be gaya mata ba, ai ni wallahi wannan auren da Hana tayi shine dai-dai." Ajiyar zuciya Suhana ta sauke! Kana tace "Ai ni ko kaɗan baya bani tausayi na jima da sanin jikina kawai yake so, tun lokacin da Kamal ya gaya min Jamal ya yi aure, kawai ina zama da shi ne don babu yadda zanyi."

tare suka shiga kitchen ta dafa musu lafiyayyen abinci mai rai da lafiya, Suhana akwai iya girki, bayan sun kammala cin abinci suka fara shirin tafiya, sai jin sukayi an banko ƙofar paroln da ƙarfi,ko sallama babu Hajiya Uwani ce ta tattaro ƴaƴanta, azo ayiwa Suhana dukan tsiya, kowace su riƙe da muciya wasu da ice,

su kusan biyar, Hajiya Uwani tace "kun ganta nan kuyi mata mugun duka sai ta mutu, har waɗannan shegun ku haɗa!." Afiya da Lili ne suka kalle juna kana suka fashe da wata dariya, Afiya tace "Jar uba kaciyar Ubanki muka fito da zaki kira mu da shegu, wallahi yau zaku daku a gidan nan." Suhana kuwa kitchen ta shiga itama ta ɗauko musu

kayan aiki, tace "Duk wacce takejin ta isa to ta ƙaraso tsakiyar paroln nan wallahi zanci uwar yarinya, Hajiya Uwani ta ce "Kai me kuke jira su uku ne ai Sarkin yawa ya fi Sarkin ƙarfi." Tana rufe baki su Jidda sukayo kan su Afiya.......

Writer ✍️ *Bey PINKY DARLING MRS JAY*

Hajiya na kusa kammala free pages ayi niya a fara payment, karku Bari ayi wannan tafiya babu ku saboda labarin ko rabinsa ba'ayi ba yanzu ma aka fara

Following this link to join my WhatsApp Channel https://whatsapp.com/channel/0029VawsLxR65yDI5tHjxh2e Masu neman gidan ƴan bariki daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu tare da sauran littatafai na

*GIDAN ƳAN BARIKI*

(*Hot love and Romantic Story*)

Story and Writer ✍🏻 bey

*Zainab Abdullah Usman*
(*PINKY Darling Mrs Jay*

*PAID BOOK*
₦500 only account number 7060577995
*Zainab Abdullah Opey*
Evidence of payment 👇
09033580667

__________________________________
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)

*DIAMOND 💎 STAR 🌟 LADIES🧝‍♀️*
(*we stand together*)
🤝🤝🤝

*Bissmillahi Rahamanin Raheem*

*PAGE* 1️⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣

Suhana ta ɗaga muciya Jidda na isowa ta kai mata duka a gadon baya, su Lili ma haka sai cin uban su Farida suke Afiya saboda jangwalo masifa har Hajiya Uwani ta kaiwa duka a hannu, Suhana kuwa ta haye kan Farida sai jibagar banza takeyi, duk ƙibarta ta kasa kwatar kanta, a hannun Suhana,

banda ihu babu abinda suke su Lili kuwa sai jibagar banza sukeyi saida suka haɗa musu jini da majina, kana suka janyosu waje kamar kayan wanki, Suhana ta kalli Hajiya Uwani tace "To tsohowar banza me halin banza, ko gobe ki kwaso wannan gayyar tsiyar kuzo kiga yadda zan lallasa muku fata.!"

Lili tace "Ai ki bar bahamagiya idan ta ƙara wannan kuskuren saina na zubar mata da haƙora!." kana suka shige ciki suka bar su Jidda na jan ƙafafuwansu da ƙyar saboda azabar duka, koda suka ƙarasa part ɗinsu Maryam ta dawo hospital, da kallo ta bisu yadda suke tafiya ga jikinsu duk ya kumbura,

lips ɗin Jidda duk ya kumbara kamar ba ita ba, Farida kuwa gaba ɗaya Suhana ta sauya mata haliltar fuska, Hajiya Uwani tace "Maryam taimaka ki duba min Ƴan Uwanki, idan waɗannacen karuwan basu halaka min su ba."

cikin mamaki Maryam tace "Me ya samesu ne Mommy.?" Nan ta kwashe komai ta gayawa Maryam dariya ce ta kwace mata kana tace "Amma wallahi Mommy bakuda hankali, ai yanzu an dena ya yin wannan shirme, amma koda yake kunyi nisa ba kwajin kira, Allah bada sa'a ko gobe ku ƙara!."

ran Mommy ne ya ɓaci cikin taikaci tace "Wallahi Maryam ki fita idano saboda ke mayar dani sa'anki shine zaki tasani a gaba kina gayamin magana, ni narasa abinda ya sauya ki." Jidda tace "Dukan Ya Sultan ya sauya ta ke manta lokacin da yana cikin wannan haukar ai har masu aikin gidan nan gardawa da su amma dukan tsiya yake musu,

kega ni Wallahi Mommy bazan koma bin shawarar ki ba jifa yadda ta fasa min jiki kina kallo bayan kece kika saka mu nace ki bari muyi hayar ƴan iska suzo su ya galgala ma na ita kikace ai bata da wani ƙarfi saboda bata da jiki, mun isheta, saiga shi, ta watso mu kamar shara." Farida tace "Ai mun auna arziki da Sultan baya gidan da yau sai na lahira yafi mu jindaɗi,

saboda har yanzu ban mata marin da ya yi min ba sai da na dena gani na kwana biyu.!" Dijah ce tace "Please ku rabamu da wannan surutu Maryama duba min lafiyata kafin mijina yazo ɗaukata, ni bansan ma tsautsayin da ya kawoni gidan nan ba idan Daddyn Mu'azam ya ga hannuna me zan gaya masa.?"

Babbar Yayarsu Zuhura tace "Ai wallahi basu dake banza ba yadda sukayi mana haka zamu rama ne amma ta wani ɓangare zamu bi yanzu muyi banza da iskancin da sukeyi." haka suka ci-gaba da tattaunawa, yadda zasu rama abinda Suhana tayi musu,

ɓangaren su Afiya kuwa gyara paroln sukayi tas kamar babu abinda ya faru, Kamal yazo suka koma gida, Suhana kuwa wanka tayi bayan ta idar da sallar isha'i, ta shirya cikin wata dogowar rigar abaya Black tayi mata kyau sosai, kamar balaraba, sai zuba ƙamshi takeyi, haka kawai taji tana son fita ta zaga gidan,

fitowarta kenan saiga Sultan ya dawo, ɗaure fuska y yi kana yace "ina zakije.?" Yadda ya ɓata fuska sai ya yi mata kwarjini sosai juyar da kanta tayi tace "zaga gidan nikeson yi." Tsaki yaja kana ya barta nan tsaye, bayansa tabi suka shige tare bedroom ɗinsa ta shiga ruwan wanka ta haɗa mai ta fito shi kuma ya tuɓe

Ya shiga wanka kitchen ta shiga ta haɗa mai abinci ta aje mai kan tebur

KANO STATE Unguwar GRA

Wannan Babban gida ne da ya amsa sunansa kaf unguwar babu gidan da yakai shi haɗuwa da tsari mai zaka ɗauka gidan shugaban ƙasa ne kutsa kaina nayi cikin wannan kai tsaye hanyar da zata sadani da parlo na nufa muryar wata mata naji kamar ana faɗa paroln na shiga wata Babbar mace na hango tsaye ita da wani Babban Mutum suna musayar yawo da shi,

"Wallahi Hajiya Binta idan ki ka koma yi maganar mai sunan Mama a bakin aurenki yarinyar da ta tozarta ni a idon duniya, ta walaƙanta ni wallahi keji na rantse duk lokacin da ta dawo wannan gida sai na kaita gidan mijinta, sai dai ta haɗe zuciya ta mutu yarinyar banza!." Wacce ya kira da Hajiya Binta idanunta cike da hawaye,

tace "Naji bazan koma yima maganar ta ba amma wallahi Alhaji bazaka kashe min ƴa ba a banza ko ta dawo bazan taɓa bari ta zauna da Buhari ba, yaron da kowa ya sani ɗan shaye-shaye da neman matan banza! na roƙe Allah ya sa duk inda Zainab take tayi aure zanga yacce zakayi da auren da kasa aka ɗaura mata."

"Yanzu Hajiya BINTA a gaban Alhaji ki ke kiran ɗan Yayarsa ɗan biyar mata mazimaci!.?" Wata mata ce ta ida maganar tana sauka kan step." Hajiya BINTA tace " To tsohowar munafuka hatsabibiya na faɗa idan ke isa ki hana ni kwana a gidan nan komai nisan jifa kisani ƙasa zai dawo sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'aje ba."

Alhaji ne yace "Kuluwa rabuda ita, duk wannan haukar da takeyi bazai hana ni kai Mai sunan mama gida Buhari ba." Wata dariya Hajiya BINTA tayi kana tace "Ai duk wannan abin dake faruwa kece sanadin komai ta Allah ba taki ba." Tana gama faɗar haka ta haura sama, ta barsu nan Alhaji fita ya yi ita kuma kuluwa,
Chapter 6 · 0% Book details