← Book details Gidan Yan Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 12

Sashe 11

Gidan Yan Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

har tsakiyar kansa, sai da ya rufe idanunsa, yana buɗewa ya sakarwa Farida murmushi har da faɗin "Ƴan Matana keyi kyau sosai." Hannunta yaja suka shiga, part ɗinsa, lokacin Suhana ta sauko parlon ƙasa, ta haɗu da su, zasu haura sama ko kallonta Sultan beyi ba tanayi yimai sannu da zuwa,

ya yi banza da ita sai wani jan Farida yake a jiki, sai da suka kusa shigewa bedroom ɗinsa Farida tayiwa Suhana gwalo, suka shige ciki, gaba ɗaya ranar Suhana batayi bacci ba ga zazzaɓi dake damunta kwana biyu, sai kusan asuba ta samu bacci saboda tana jin ihun Sultan da Farida suna sex,

tun daga ranar komai ya sauyawa Sultan baya kulata idan tayi mai magana sai wulaƙanci da hantara, wani lokaci sai tana zaune parlo zasu fito tare da Farida yace ta tashi ta basu wuri wani lokaci basuyi mata magana sai ta ga sun fara isakancin su ta bar musu parlo, abinda ya ƙara ɗaure mata idan taje fita part ɗinsu

Security su hana mata fita, wai umurnin Sultan ne, haka su Afiya idan sun zo wurinta, security sun gaya musu Suhana bata gari tayi tafiya, ita da Sultan sun yarda saboda basu ganin Sultan, kai abin ya basu mamaki rashin sanar dasu zasu bar ƙasa,

Hajiya Uwani kuwa washegarin ranar assabar, ta kira Hajiya Ruky suka bar garin Sokoto zuwa Maiduguri, wurin wani sabon malami, Suhana kuwa duk abin duniya ya dameta, saboda Farida ta saka Sultan ya karɓe mata waya, ga rashin lafiya dake damunta, tanason gaya masa amma babu dama,.

Daddy kuwa shagali kawai suke sha shi da su Afiya, har wani haske fatarsa ta ƙarayi ta goge, kai da gani kasan hutuwa da kulawa sun samu, satin Hajiya Uwani biyu kana suka dawo, ta fara bine wasu layu, cikin gidan, ta zagaya baya, ta saka laya bayan part ɗin Afiya, tana gama sakawa, ta wuce ashe Afiya ta fito, zataje part ɗin Daddy,

ta ganta, sai da ta wuce, ita kuma taje ta buɗe ramen, ta fitar da layun sun kai guda biyar, part ɗinta ta koma ta ƙona, su kana ta fito, part ɗin Lili taje ta sanar da ita, tace suje su duba, dole itama ta saka mata Lili tace " meyasa baki sameta a wurin ba kiyi mata dukan Allah tsine uwar mai ƙarya, ai wallahi idan nice kasheta ne kawai bazanyi ba."

Afiya tace "Laila ba haka zamu yi ba yanzu idanu zamu saka mata, duk wani abu da takeyi, yanzu zan saka Kamal ya kawo muna CCT Camera, mu saka duk abinda takeyi a part ɗinmu zamu ganta, idan ta gama muje mu fitar da abinda ta ajiye, saboda idan muka fito ta ganmu ta wani bangare zata koma ta cutar damu."

haka suka gama tattaunawa suka fita, bayan part, ɗin Lili nan ma suka samu wasu layu da wasu tarkace, Lili tace ko muje part ɗin Suhana mugani, kesan fa ba ƙaunarmu takeyi ba gaba ɗaya Afiya tace ke kawo shawara suka tafi, cikin folawowin dake bayan part din suka fara tono rami, sun fitarda wasu manyan ƙorai da layu da wasu ƙohonin rago,

wani abu da suka fitar har da wani baƙin hayaƙi, ya fito ya tashi sama, abubuwa sosai suka fitar, kana suka dawo, cike da mamakin wannan rashin imani irin na Hajiya Uwani,

suna zauna Daddy ya kira waya yana son ganinsu yansu, gaba ɗaya sai da ƙirjinsu ya yi wani dukan uku-uku, suka fito da addu'a fal a bakinsu, zaune suka tarar da Daddy parlonsa Hajiya Uwani na gefe, ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, zama Afiya tayi gefen Daddy ita kuwa Lili ta haye kan ƙafafunsa, ta rungumusa tace "Baby ya akayi ne kana buƙatar wani abu ne.?"

Lili ta faɗa tana shafa fuskarsa, har zuwa wuyansa, wani abu Daddy yaji yana saukar masa har tsakiyar kansa, gaba ɗaya ya kasa magana saboda shafar da Lili Keyi masa, Hajiya Uwani takaici ne ya kamata rai ɓace ta tace "Alhaji kiransu kayi fa saboda ka sallamesu su bar min gida amma ka biyewa karuwan banza.... Tas Lili ta kwaɗa wa Uwani mari,

tace "Don ubanki ban hanamiki kiranmu da karuwai ba, tare da uwarki ko ubanki mukayi yawon karuwanci ne.?" Afiya tace Au wai ta sa shi kikayi a gaba ya sake mu to wallahi bari kiji gida mun riga mun shigo sai dai ki fita ki bamu wuri, idan ma mun fita, sai dai ki nemi mijinki ki rasa, saboda karuwamcin da kike magana akai munayi, lokacin zamu nuna miki asalin kalarmu ƙatuwar banza."

Daddy yace "Afiya Please bana son wannan rigimar dan Allah ku dena." Lili tace "yadda kakeso haka za'ayi Babyna.!" Hajiya Uwani kuwa fita tayi ko minti goma ba'ayi ba ta dawo tare da su, Jidda tace ko Daddy Kar su ragawa idan ya tsaya suyi mai dukan tsiya, nan fa rigima ta ɓarki, sai dukan juna suke suna fasa kayan dake parlon,

Daddy ya shiga rabasu, Hajiya Uwani ta kwaɗa mai muciya a hannu, Lili ta tafi kaiwa Jidda duka, ta goce sai a fuskar Daddy hancinsa ya fashe da jini, gaba ɗaya sai da suka har gitsa parlon suka fashe abinda fashewa suka lalata komai, Afiya kuwa ta fasawa Hajiya Uwani baki ta buge mata ƙafa, , gaba ɗaya kowa yaji jiki,

Afiya ta kira Mustafa ya zo ya kaisu hospital har Daddy, sai da akayi mai gyaran hannu, saboda ya samu rauni, Afiya gilas ya yanke mata hannu, Lili kuwa a ƙafa ta taka galis, bayan an gama duba su aka basu magunguna suka dawo gida Su Jidda kuwa Maryam ce ta duba su,

Suhana kuwa yanzu wata uku bataga al'adarta ta zo ba kayanta ta duba anan ta samu pt cikin jakarta, tayi test ɗin fitsari ya nuna tana ɗauke da ciki! Tayi iya ƙoƙarinta ta sanar da Sultan amma abu ya gagara dole ta haƙura ta cigaba da kulawa da cikinta,

Ƙarfe 12:00 na rana

Suhana tana zaune taji kamar ana kiran sunanta amma bata amsa ba, chan taji muryar Mahaifiyarta na kiranta, ta fito, tayi sa'a ba kowa waje, haka ta rinƙa zaga gidan amma bataji inda Muryar ke fitowa ba, tayi tafiya mai nisa cikin gidan har ta kawo bakin get, ta fita, shura taji ta dena jin muryar, mai a dai-daita sahu ta shiga

tace Ya kaita Bafarawa estate, gidan Jamal yana direta tace ya jira ta kawo mai kuɗinsa gidan buɗe yake amma Jamal baya nan bedroom ɗinsa ta shiga inda yake ajiye kuɗi ta duba ta ɗauko ta bawa mai adai-daita sahu,ta koma ciki kwanciya tayi saboda kanta dake masifar ciyo wani bacci ya yi gaba da ita,

Jamal kuwa yana Zaune gidansu Abbansa ya tasa shi a gaba yana mai faɗan damuwar da ya saka a ransa gaba ɗaya ya koma kamar wani mahaukaci, Ummansa tace gaskiya ya shirya ya tafi Kano wurin Yayarta, haka suka tsaida shawara, kuma ya amince, saboda haka ya yi musu sallama ya wuce gidansa saboda ya haɗa kayansa,

tun a harabar gidan yake jin ƙamshin turaren Suhana, amma sai ya basar, saboda ya saba jin haka, paroln ya shiga, nan ya yi suman tsaye ganin Suhana kwance, ta falka bacci tana kallon Tv, a zatonsa Aljana ce nan ya fara addu'oi da duk suka zo bakinsa, Dariya ya bawa Suhana tace "Jamal nice fa Hana Baby, ba aljana bace

zo ka taɓa ni kagani." a tsorace ya ji ya taɓa hannunta, wata ajiyar zuciya ya sauke! Yace "Hana Please karki koma tafiya ki barni kinji, ko." Dariya tayi kana tace "yanzu dai ba wannan ba Kano nikeson tafiya yau!." Yace "Nima Kano zanje wurin Yayar Ummana muje kawai dama kayana na zo ɗauka amma ina kayanki.?"

murmushi tayi wanda yafi kuka ciyo, kana tace "a haka zanje." Be koma magana ba ya shiga bedroom ya haɗu kayansa, suka fita, sai filin jirgi, ƙarfe uku jirgi ya tashi sai garin Kano, ƙarfe biyar suka, isa, da yake Yayar Ummansa tasan da zuwansa suna isowa direba yazo ɗaukarsa, nan yace "Hana wace unguwa zakiji a fara sauke ki.?"

tace "GRA zanje." Yace "Kai Unguwa ɗaya zamuje." Suka shiga Direba yaja sai Unguwar GRA suna kusa isa get ɗin gidansu, "Suhana tace "Direba saukeni a nan." tsayawa ya yi da mota ta fita kai tsaye get ɗin gidan ta nufa, Dirba ma get ɗin gidan ya tsaya tana danna horn, mamaki ne ya kama Jamal wa Suhana ta sani a gidan dama nan ne zata zo,

koda Get Man ya buɗe ƙofa, Suhana har ta shige ciki, bata tsaya ko ina ba sai babban parlon gidan, Jamal na bayanta yana tare suka shiga, gaba ɗaya mutanen gidan suna parlo, Alhaji da Hajiya BINTA da Hajiya Kuluwa sai wani matashi kusa da Daddy tare da wata mata Kamar su ɗaya da matashin kamar da ga sama Hajiya Binta ta ga Suhana ta faɗo cikin, paroln,

da sauri ta miƙa tsaye bakinta na rawa tace "Zai zai Zainab kice kuwa ko mafalki nikeyi!.?" Suhana ta fashe da kuka tana faɗawa jikin Matar tace "Ummie nice ba mafalki bane." Jamal kuwa baki ya saki da hanci yana kallon ikon Allah Alhaji ne ya yi gyaran murya kana yace "Hajiya BINTA ki samu wuri ki zauna kun cika min kunne da haya niya"

Suhana na jikinta suka zauna Hajiya Kuluwa, sai lokacin ta kula da Jamal kana ta bashi damar zama gaba ɗaya ta rikice, amma ta dake saboda kar ayi daurin fahimtar ta, Alhaji yace "To Alhmdllh Buhari ga Matarka Zainab ta dawo bazan tambayata inda taje ko daga ina ta fito ba kawai ka ɗauketa ku tafi.!"

wata dira Jamal ya yi a gaban Alhaji yace "Na shiga uku don Allah karku yi min haka wallahi Suhana itace rayuwata, bazan iya rayuwa babu ta, don Allah karku yi min haka." Ya dawo wurin Suhana dake kuka jin abinda Abbanta ke faɗa yace " Please Hana ki faɗa mai nine Mijinki dan Allah, kar a rabamu.!"
Chapter 11 · 0% Book details