← Book details Gidan Yan Bariki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 12

Sashe 12

Gidan Yan Bariki Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

Buhari ne ya tashi Kamar wani mahaukaci yanyo hannun Suhana, tana tirjewa Hajiya BINTA, tariƙe hannun ƴarta, tace "Wallahi Wallahi na rantse da Allah Zainab bazata zauna da wannan ɗan iska ba mashayi!." Matar dake Zaune tace "Ashe abinda ake gayamin gaskiya ne, baki da mutunci a gabana kike zagar min ƴaro."

Hajiya BINTA tace "Na zage shi ai wallahi koke hajiya Luba zan iya zagi saboda kece marar mutunci bani ba." Alhaji yace, " wallahi idan kika koma magana a bakin aurenki ke koma Zainab idan baki bi Buhari ba, saina tsini miki albarka.!" Haka Buhari yaja Suhana Kamar kayan wanki ya fita uwarsa ta mara mai baya suka fita,

Jamal ya bisu da gudu yana kuka su dawo mai da matarsa, Hajiya BINTA kuwa sama ta haura tana kuka,

Koya wannan chakwakiyar zata kasance idan Sultan ya dawo hayyacinsa ta ina zai fara neman Suhana gashi tana ɗauke da cikinsa a jikinta shin ya zata kasance tsakanin Suhana da Buhari mahaifinta ya ɗaura mata aure bayan ta ɗauke shekaru bata gida shin auren wa aka fara ɗaurawa na Buhari ko na Sultan, menene sanadin barinta gida, ta shiga barki, har ta chanza suna daga Zainba zuwa Suhana ,

Ya Jamal zai ƙare da rashin Suhana?

Burin Suhana zai cika na gina ƙaton gida ta saka mai suna GIDAN ƳAN BARIKI,

Ya su Afiya zasu ƙare da Hajiya Uwani? Suwaye dangin Mahaifiyar Sultan? Duk waɗannan tambayoyi zaku samu amsar su a cikin Book2 karku bari ayi wannan tafiyar babuku,

Writer ✍️ Bey *PINKY DARLING MRS JAY*
anan na kawo ƙarshen wannan littafi na ɗaya duk mai buƙatar Book2 zai biya ₦500 ne duk mai buƙata ya yi min magana ta wannan number 09033580667
Chapter 12 · 0% Book details