← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 20

Sashe 3

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Abin mamaki wannan aure bakatatan haka Fatima, amma dan Allah waye angon."

Murmushi ta yi kafin bata amsa cikin nutsuwa Fatima ta fara cewa ,"Na shirya tunkarar kaddarata ko wacce iri ce , bani da damuwa ko fargaba Fiddausi, duk yadda rayuwata ta juya mini zan yi abin da ya dace ."

Ta aje maganar tana kallon Fiddausi, sannan ta d'ora da cewa ,"Kin san dai abokin baba Alaji Mansur to d'ansa ."

Cikin mamaki matuka Fiddausi ta kalli Fatima

"Wai kamal kike nufi ."? Ta jefa mata tambaya da mamaki

Dariya Fatima ta yi , daga bisani ta ce ," Ke ma dai kinsan ba shi da wani d'ah banda Kamal. "

"Tabbbbb! Jan aiki kika d'auko ki ce ." Fiddausi ta fad'a tana ri'ke ha'bar ta

Bata jira cewar Fatima ba ta cigaba da magana ,"Wannan gayen da kowa yasan yarinyar da yake so Zarah Sale .Wannan yarinyar da suke da uwar kudi da kadarori , sannan gata marubuciya mai masoya , kuma likita ce fa.Me ya kai ki ke kuwa Fatima ga Kamal. "?

Tsaki Fatima taja najin haushin kalaman kawar tata hakan ya sa ta fara cewa ," Ke kika san wata Zarah Sale da kike karanta novels, amma koma wace ita , ni Fatima na tabbatar baza ta fini komai ba , kudin banza Fiddausi, muna da kudi muna da komai , dan haka shima Kamal d'in ko ya yake santa shi ya sani ga zabin iyayensa ."

"Babbar magana." Cewar Fiddausi

"Ai ko dai da kina karanta novels zaki san Zarah sale Salisu.To wannan aure ni dai Allah ya nuna mana ."

"Haka za ki ce kawai." Fatima ta fad'a tana hararar kawar tata.

07040805269
WhatsApp only

Alkalamin Autar marubuta ne .

FATIMA DA ZARAH🎀

Na
Autar Marubuta

________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing❌

Page 6 & 7

Washe gari

Karin kumallo suke cikin hira da farin ciki
Hajjiya Sa'adatu kawai abincinta take ci ba tare da tana shiga hirar 'ya'yan nata ba .

"Alhamdulillah yau ba aiki sai zaman gida ." Zarah ta yi magna da farin ciki tana gyara zaman Bluetooth d'in dake kunnenta

Umar ne ya ce ,"Hmmm aunty Zarah ke nan , kwana biyu kin dena rubutu."

Wani kallo ta jefa masa tana cewa ,"Yanzu na fi bawa gidan television d'in mu muhimmanci , dah ni za su tura Dubai wallahi na 'ki zuwa."

Mahmud kawai murmushi ya yi , sannan ya kalli Mommy yana cewa ,"Yau babu dadi breakfast Daddy ba ya nan ."

Sai a lokacin Hajjiya ta d'ago kai tana cewa, "Yau ai sammako ya yi yana gidan gona."

Sannan ta kalli Zarah tana cewa, "Ya yi mini magana a kan ki da Kamal ya ce ki masa magana a yi a wuce wajen babu amfanin 'bata lokacin."

Murmushin ya'ke Zarah ta yi tana kallon 'ya uwan nata

Yayin da sukai mata murmushi suma tabbas wannan rana Zarah ke jira ita da Kamal.

Haka suma gidan Alaji Mansur suna zaune suna jiran fitowar Alaji domin su fara cin abinci

"Laila ki temake ni ki mini guga dan Allah, kin ga na kusa komawa makaranta."

Cewar Nasir

Wata harara Laila ta buga wa Nasir tana cewa ,"Hmmm mommy kin ji shi yanzu fa ya gama cewa bani da amfani , to wallahi bazan maka ba."

Hajjiya ta kwashe da dariya kafin ta ce ,"Ai gaskiya kawai aure zan had'a ku na huta , kuje can ku 'karata.Shikenan tuwo na mai na ."

Nasir Cikin jin haushin maganar da Laila ta fad'a masa ya ce ,"Tabb mommy, ni me zan da wannan yarinyar gata mummuna Allah na fita kyau tabb , waye ma zai aure ki."

Sai a lokacin Kamal ya yi dariya yana sake baza kunne yana sauraran hirar tasu , lokacin guda kuma yana tunanin idan zai fita company zai biya ya ga Zarah.

A ajiyar zuciya Laila ta yi sannan taja tsaki tana kallon Nasir, "Ni wallahi gara ma ka koma makarantar na huta ."

A lokacin Alaji Mansur ya fito cikin farin ciki ya samu guri ya zauna

Haka zalika suma duk sun kula da irin wannan gagarumin farin ciki da ya ke ciki

Bata abinci yake ba ma shi magana ya fara kamar haka ,"Gaskiya na ji dad'in ganin du duk anan domin akwai magana mai daraja da muhimmanci da zami ko na ce da zan sanar daku ."

Kamal ya kalli mahaifiyarshi cikin murmushi, haka Nasir ya kalli Laila

Mommy ce ta ce ,"Ai ni Alaji tun jiya da kaje gidan Alaji Mustapha na kula da wani farin ciki da kake , na ce mene ka ce kawai ni ma na gode Allah na yi murna bayan baka fad'a mini komai ba ."

Wata dariya Alaji Mansur ya ke ce da ita

Hakan yasa duk su Nasir suma dariya

"Daddy dan Allah ka fad'a mana mene wannan farin cikin ." Cewar Laila

Alaji Mansur ya kalli Hajjiya yana cewa ,"Wato Hajjiya ina d'aki yanzu, sai Alaji Mustapha ya kirani , to naji dadi sosai yadda Fatima ta nuna masa ya isa da ita , wato Fatima ta amince da auren Kamal kun ji dai abin farin ciki. "

Dauuu dauuu kowa yaji a cikin zuciyarshi, duk suka canja yanayi zuwa rashin fahimtar maganar Alaji

Babu wanda ya ce dashi komai , ya cigaba da cewa Hajjiya, "Wato kin san mun yanke shawarar auren Kamal da Fatima."

A karo na biyu zukatansu suka sake shiga rudani ,"Wai wanne Kamal kake magana ne Alaji. "?

Hajjiya ta yi tambaya da mamaki

" Ahhhh kin jiki fa , akwai wani Kamal bayan wannan. "Ya nuna kamal da ranshi yake a rikice da matukar tashin hankali

" Ai mun shirya tsaf ni da Alaji Mustapha domin samun cikakken zumunci."Alaji ya kara musu bayani

Kallon juna suke da matukar mamaki , Kamal dauriya ya yi yayin da kanshi yake matukar sara masa ya ce ,"Daddy wai Zarah kake nufi ko Fatima. "?

Murmushi Alaji ya yi yana cewa," Fatima dai 'yar Alaji, amma ai zaka iya kiranta da zaran idan haka kake so , daman an ce fatimatuzzahara'u."

A take Kamal ya sake jin kanshi ya matukar sara masa idanunsa sun ciko da ruwa

"Haba Alaji, wacce irin Fatima kuma , yaron nan fa Kamal Zarah yake so 'yar Alaji Sale , amma ka zo kana wata magana kuka."
Mommy ke nan

Lokaci guda Alaji Mansur ya fusata yana cewa, "Ni bansan wata maganar Zarah ba , Fatima na sani kuma ita na za'ba."

Ya juya ya kalli kamal dake cikin matukar rudani yana cewa, "Karka yadda ka nuna mini ban isa da kai ba , mene ai bun Fatima da zaka na kira mini wata Zarah, to wallahi Kamal ni ne ubanka , kuma ba a canjawa tuwo suna , mun tsaida ranar auren ku , ban yi maka dole ba , idan kana da hankali zaka yi abin da ya dace ."

Yana gama maganar ya tashi ya fita cikin fusata

Wasu hawaye suka zubowa kamal masu zafi ,kafin wasu su dire wasu na biyo bayansu

Laila da Nasir suka kalli juna da tashin hankali, Hajjiya ma haka taji wani ba'kon yanayi .

Tun da Fatima ta amince da auren Kamal, Alaji Mustapha duk ya canza mata farin cikin matukar gaske , domin har sabuwar mota Alaji ya canza mata

Lokacin da 'yan uwanta suka kirata video call, nan suke bayyana mata irin shirye-shiryen da zasi a wannan biki , zasi shagali sosai
Ita dai Fatima tana fatan auren Kamal alheri ne a gareta , ba samuwar wata sabuwar kaddarar ba .

Lokacin da dare ya yi Alaji Sale da Mahmud Umar duk suna zaune a falo hadda Hajjiya suna hira suna kallo

A lokacin Zarah ta shigo da gudu kanta babu d'ankwali ta fad'o jikin Hajjiya tana wani rurucewa da kuka .

Kafff hankulansu ya tashi tsaye da jin irin wannan kuka na Zarah

Hajjiya ta d'agota a jikinta , amma Zarah ta'ki tashi ta fuskanci kowa kawai kukanta take shekawa

"Mene ne ya faru ne haka."?
Alaji Sale ya tambaya da tashin hankali

Haka suma Mahmud da umar duk sun 'kagu su ji dalilin wannan kuka na yayarsu da basu ta'ba ganin ta a irin wannan yanayi ba

" Mene ya ke faruwa ne Zarah." Mommy ta sake tambaya yayin da ta yi nasarar d'ago Zarah

Idanunta sun yi jajir yayin da wasu hawayen suke turereniya Zarah taso fara magana amma wannan kukan ya sake shan kanta .

Cikin kokari ta d'ago tana kallon furkar mahaifiyar ta tana cewa ," Mommy amana ta yi 'karanci , mutane babu mommy Kamal aure zai ."

Wani tashin mamaki suka ji ya bugo musu zukata

Wasu sabbin hawaye suka sake zubo wa Zarah

Ta ci gaba da magana cikin takaici da bacin rai tare da hawayenta ,"Mommy nan da wata daya , wata zai aura ba ni ba , baban shi ne ya sama masa mata."

Ta karasa magna tana sake shiga wani hali tana kwanciya a jikin Hajjiya

"Innalillahi, kamal din ne ya ce miki zai aure? Kamal din ."? Mommy ta yi magana cikin mamaki tana kallon Alaji sale

Alaji sale a wannan karan ma dai bai iya cewa komai ba

Har Zarah ta sake fashewa da kuka tana cewa," Mene ya sa haka mommy, me ya sa Kamal zai barni , shi ne fa ya kirani yake fadan zai yi aure, shi ke nan na rasa shi mommy. " Ta aje maganar cikin wani gwanin ban tausayi na kuka

A lokacin Alaji sale ya kalleta yana cewa ,"Ba za ki rasa shi ba ."...

Alkalamin Autar marubuta ne

Zasu same ni a WhatsApp a wannan number
07040805269

FATIMA DA ZARAH🎀

Na
Autar marubuta

________________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing❌

Page 8 & 9

Diff Zarah ta yi ta d'ago tana kallon Alaji sale,
Duk hankalinsu ya koma kan Alaji da jin wannan magana
Chapter 3 · 0% Book details