Sashe 11
Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kowa ya shiryawa wannan biki , musamman wajen dinner irin babban mawakin da aka gayyato , ga baki duk sun hallara , 'yan uwan amarya dana ango gurin taro ya cika fall masha Allah.
Ga Alaji Mustapha da Alaji Mansur duk sun sha ado , su Hajjiya Amina iyayen amarya
Kamal ma an sha kyau matuka, ga Nasir da abokanshi , Fatima da Zarah sun sha kaya irin daya sun yi matukar kyau
Kawayen amarya da manyan baki sai murna ake
A can daga saman stage ga Laila amarya👰
Tare da angonta Dactor Sadiq sun hadu sosai sai jan hankali suke .
Mawakin da aka gayyato yana fara wakarsa , su Alaji Mustapha suka ja zugar su , domin yin wani pati din da ya shirya don haka babu wasu manyan iyaye maza a gun
Gurin sai tashin kamshi yashe da walwali
A lokacin ne aka saki wakar da aka yiwa amarya ta fito ita da angonta suna takawa .
Kafin ka ce komai 'yan uwa suka fara zuba liki
Hajjiya Amina ce ta zo da wasu kudi dummm tuli guda zugar dubu-dubu tana likasu
Shima kamal ya kwaso nashi ya zuba musu ya koma
Fatima da Zarah suka taso
Zarah ta fara likin dari biyar biyar masu yawa ,
Fatima na ganin haka , ta maida kudin hannunta ta d'ebo dubu-dubu tana lika musu
Lokacin da Zarah ta fahimci hakan , sai ta zaro daloli a cikin jakarta tana rawa tana likawa
Ita ma Fatima wannan dalolin ta kwaso a jaka kawai tana watsawa .
Tuni guri ya rude , kowa hankalinshi ya koma gun su , maxa da mata kuwa ana fadin "matan Kamal ne
Da Fatima da Zarah, daya lauya ce dayar kuma likita ce ."
Haka wanda basu san masoyiyarsu Zarah Sale ba suka ringa farin cikin ganinta .
Guri ya rude da dalolin dasu Zarah suke watsawa
Shi kam Kamal ranshi idan ya yi dubu , to duk sun 'bata masa shi
Ya matukar jin bakin ciki yadda suke gasar zubar da kudi a gurin nan ko a jikinsu .Bayan jan kunnen da ya yi musu amma sun yi watsi da maganar sa.
Haka ran kamal ya sake matukar baci , kawai ya fita , ya hau mota ya nufi gida .
Yana tuka mota abin yanata damunsa a ranshi
"Yanzu me suke nufi ban isa dasu ba ke nan kome , kudi hauka ne , suna da ilmi amma vasa amfani dashi ."
Cikin bacin ran nan ya koma gida , ya zauna a falo abinsa .
Anata cakarewa ana murna bayan an tashi suka nufo hanyar gida .
Nasir ne ya fara shigowa bai ma kula da Kamal ba , hakan ya sa ya nufi dakinsa.
Fatima da Zarah suka shigo suna magana , inda Zarah take cewa .
"Bari kuma gobe , ai wannan kudin ba komai ba ne , dan ma dear ya hana canza mota mai tsada ."
Fatima ta ce .
"Zancen kike so an ce da gwauro ya iyali ."
Suka karasa falon a daidai wannan lokacin suna zama
Wani bakin ciki Kamal yaji ya sake turnike masa zuciya, wato ma ko nadama basa yi
Yadda Kamal yake jinshi zai iyay musu komai idan bai kai zuciyarshi nesa ba , don ji yake kamar ya rufesu da duka .
Haka Allah ya hani kowacce a cikin su da ta lura da halin da Kamal yake ciki , bare si masa magana .
"Aikin kawai dadin abin ni na canza mota , ke ce ta gagare ki." Cewar Fatima
Zarah ta ce .
"Dan kin canza mota ai ba .. "
Kafin Zarah ta karasa magana taji saukar mari a kuncinta , kafin Fatima ta kula da abin da yake faruwa ta ji ita ma an sauke mata wannan mari .
Kamal ne a tsaye a kansu idanunsa sun yi jajir , jijiyoyin kanshi duk sun tashi , sai wani huci yake , ka ce wani zaki.
Ya kalli kowacce dake rike da kuncinta cikin mamaki da suke kallon shi
"Ku wanne kalar marasa tunanine da rashin hankali.
Ni ban isa daku ba , duk irin maganar dana fada muku , bayan kun aikata abin da kuka gadama a wajen dinner kun zo gida kuma zaku tayar mini da hankali."
Yaja dogon ajiyar zuciya mai zafi sannan ya cigaba da magana .
Next page
07040805269
WhatsApp only.
FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><
Editing❌
Page 26 & 27
"Ina hankulanku suke , ko daman babu ne ."?
A wannan lokacin Fatima ta sunkuyar da kai wasu hawaye suna zuraro mata
"Kun bani kunya , kun bakantan zuciya da rayuwa, tun a gida na sanar daku bana son almubazzaranci amma dake ni ba komai bane a wajen ku , kuka ture magana , kun nuna ban isa daku ba koh."?
Ya jefa musu tambayar yana zare jajayen idanunshi.
" To daga yau zan dau mataki a kan ku , tunda aikin lauya d Likita kuke takama dashi duk zaku janye shi , zan yi maganinku ."
Ya nufi kofar dakinshi cikin huci .
Zarah ta cire hannu a wajen marin tana ajiyar zuciya.
Anan gidan Alaji Mustapha kuwa
Suna falo tare da Hajjiya Binta da mahaifin Abba Alaji wato Alaji Sani
Bayan Alaji Sani ya gaisa da Alaji Mustapha, nan suka gaisa da kanwarshi Hajjiya Binta
"To Alaji yanzu babu wata makaranta da aka samawa Abba Alaji ne ."?
Hajjiya Binta ta tambayi yayanta .
Alaji Sani murmushi na ciwo ya yi sannan ya ce .
" Dan Allah ki dena mini zancen Abba, Allah ya gani na yi abin da zan yi akanshi , na gaji wallahi, Allah ma ya sani , idan ba so yake ya kashe ni ba,
Yaron nan zan aje kudi na , kudin mutane duk ya kwashe , a'a wallahi na gaji , in ya shigo hannuna ai wallahi sai dai a kwace shi ."
Cikin bacin rai ya aje magana.
Alaji Mustapha ne ya ce .
"Ai hakuri za kai Alaji Sani , hannunka ba zai ribe ka yanke ka yar ba , kawai addu'a zaka runguma komai zai wuce in sha Allah."
Alaji Sani ya sake murmushi na takaici yana cewa.
"Addu'a ta nawa kuma Alaji Mustapha, kuma idan hannuka ya rube dole kuwa ka yanke ka yar ."
Alaji Mustapha ya ce .
"A dai cigaba da addu'a zai shiryu in sha Allah, Allah ya shirya mu ya shirya kowa da kowa ."
Hajjiya Binta ta ce .
"Amin ya Allah."
Alaji Sani ya tashi tsaye , yana cewa.
"To bari na koma ga shi kuwa dare ya yi ."......
Washe Gari da safiya ta yi
Kamal babu wacce ya ce da ita komai, ko abinci bai saurara ba ya fara shirin tafiya company.
Ganin haka yasa Fatima da Zarah suka tare shi suna ba shi hakuri .
Samm Kamal ba shi da niyyar hakura ,
Amma da suka fahimci duk laifunsu ne da suka kai shi bango har kuka suka yi suna ba shi hakuri.
A lokacin zuciyarshi ta karaya , ya tabbatar musu ya yafe musu , domin ma saida ya karya sannan ya fita .
Sannan aka samu saukin rayuwa a cikin gidan .
Misalin karfe 1 na dare kowa ya kwanta,
Gama karatun Nasir ke nan zai fara bacci yaji wayarshi na ringin yaja dogon tsaki ya katse kiran
" Abba Alaji ko mara zuciya, uban me zan masa ma a wannan daren , ni bansan ma me yasa ban goge number shi ba ."
Nasir ya aje maganar yana tsaki
Yayin da kiran Abba Alaji ya sake shigowa .
Nasir ya dauki wayar cikin masifa yana cewa.
"Mene kuma a wannan lokacin."
Nasir daga can kasa ya jiyo muryar Abba Alaji cikin jigata yana cewa.
"Dan Allah Nasir ka fito ka taimaka mini , ina kofar gida ."
Nasir yaja tsaki ya kashe wayar
Mamaki yaji ya kamashi yadda yaji muryar Abba cikin wani hali
Hakan yasa ya tashi ya bude kofar shi ya leka falo , yaga babu kowa , sannan ya fito cikin sanda ya bude kofar fita a hankali ya fita ba tare da ya rufe ba
Ya fita waje
Yana fita yaga Abba Alaji da farar singlet jikinshi duk jini, fuska duk ta kunbura da gani babu tambaya wannan duka ne da wani abin aka masa
"Me ya sa me ka haka ."?
Ya tambaye shi da mamaki
Abba Alaji cikin haki da wahala ya ce .
" Daddy ne ya dake ni wallahi, badaban na gudu ba kashe ni ma zai ."
Nasir ya kwashe da dariya
Sannan ya kalli Abba yana fadin .
"Allah sarki daddy wato ka kai shi bango , toni yanzu da ka zo mene zan maka ."?
Abba Alaji cikin yanayin tausayi ya ce .
" Wallahi jiki na duk ba dadi Nasir, ka temakan na kwana a dakinka zuwa safiya na tafi ."
Nasir ya zaro ido cikin rainin wayo yana cewa.
"Tabbb amma ka rainan wayo , dakin nawa da yake a cikin gida, kawai wani kato da kai zaka shigar musu gida , to gaskiya a'a 'kara gaba kawai ."
Abba Alaji cikin wata fuska ta matukar tausayi ya sake kallon Nasir yana cewa.
"Yanzu ina zani Nasir, ina zani dan Allah kai ne kawai zaka taimake ni , safiya na yi ko asuba zan fito babu wanda zai sani ."
Nasir ya dan yi jimmm yana tunani
Abba ya yi shiru
Nasir ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce
"To shi ke nan , amma wallahi ba wannan shegen baccin naka zaka yi ba , asuba na yi zan tashe ka , Yaya Kamal yana tafiya masallaci zaka fito ."
Abba ya ce .
"Naji na kuma yadda ."
Ya juya yabi bayanshi , a hankali suka shiga gidan suka rufe kofar suka koma daki .
Ya ba shi kaya ya canza , ya gasa jikinshi da ruwa , har magani Nasir ya ba shi , sannan Abba aka kwanta aka fara bacci .