← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 20

Sashe 17

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ta fito ne ya kalleta yana fadin.
"Hajjiya Binta shin mene alakarki da marigayiya Hajjiya Samira."

Hajjiya Binta ta yi ajiyar zuciya kana ta fara magana .
"Ni da ita miji guda muka aura tsawon wani lokaci kafin Allah ya rabamu , ma" ana kafin Alaji Mustapha ya sake ta ."

Barrister Nuhu ya ce .
"Alhamdulillah kina nufin dai abokan zama ne a dah ."?

Hajjiya Binta ta ce ." Eh ."

Barrister Nuhu ya ce .
"Hajjiya Binta ki sanar da kotu yadda wannan lamarin ya faru har ya kai ga hajjiya Samira ta rasu , wato ma'ana yadda komai ya faru a gaban idonki ."

Hajjiya ta gyara mayafin dake jikinta kana ta fara cewa .

"A wannan ranar na kaiwa Hajjiya Samira ziyara sakamakon ta zo daga saudiya kuma zata koma da wuri , ana cikin haka sai Fatima ta tafi wajen aiki wanda ita 'yace ga marigayiya Hajjiya Samira, dama shi mijinsu Kamal ban same shi a gidan ba ,

Sai ya zama babu kowa cikin gidan sai mu 3 , ni da Hajjiya muna hira a falo, har na ce mata ta dauko mini tsarabar turare na , sai ta tashi a domin ta kawomin ,

Ita kuma a wannan lokacin Zarah ta fito daga dakinta ta tsaya mini a ka tana hararata, sai ga Hajjiya ta fito tare da turaren da taje kawo mini ."

Hajjiya Binta ta aje ajiyar zuciya sannan ta cigaba da cewa.
"Kawai Hajjiya Samira tana yiwa Zarah magana , sai ta fara mata rashin kunya ta hankad'eta ta fadi . Shi ke nan rai ya yi halinsa

Amma na tabbatar cewa ita Zarah batai tsammanin abin zai kai ga mutuwa ba ."

Barrister fatima ta yi wani murmushi na takama da mamaki

Zarah ta sunkuyar da kai dajin yadda Hajjiya Binta ta tona mata asiri

Barrister Nuhu ya kalli alkali yana fadin.
"Ya mai girma mai shari'a, wannan shi ne abin da muke son sanarwa kotu , ina rokon wannan kotu mai adalci data gaggauta yankewa Zarah sale hukunci .Na gode ya mai shari'a."

Cikin takun isa ya koma ya zauna

Alaji Sale ajiyar zuciya ya sauke yana kiran sunan Allah

Shi kam Kamal ba a cewa komai.

"Barrister Fatima shin kina da abin cewa ."?
Alkali ya jefawa Fatima tambaya

Cikin girmamawa Barrister ta tashi tsaye tana cewa.
" Ina da abin cewa ga Hajjiya Binta ya mai shari'a. "

"Kotu ta baki dama." Alkali ya mayar mata

Barrister Fatima ta karaso gaban Hajjiya Binta
Sannan ta fara cewa .

"Ya mai girma mai shari'a, wacce ake zargin Zarah ta kashe da mommy take kiranta , sannan a daren da marigayiya ta zo Nigeria , to ciwon zuciyarta ya tashi kuma Zarah da ake tuhuma ita ce likitan data duba lafiyarta a cikin dare ."

Barrister fatima ta gyara rigarta ta cigaba da cewa .
"To me yasa idan Zarah tana son kashe Hajjiya Samira bata kasheta tun a asubiti ba?
Sai da aka dawo gida , kuma ta rasa yadda zata kasheta sai ta hanyar da Hajjiya Binta ta bada bayani ."?

Alaji Mustapha ya girgiza kai tare da cigaba da saurara

" Ya mai girma mai shari'a, ina rokon wannan kotu mai adalci data sake komawa baya domin bibiyar wasu zantuka na kuskure da Hajjiya Binta ta yi yayin had'a labarin ta ."

"Ina da jah ya mai shari'a."
Barrister Nuhu ya yi saurin kai farmaki

"Mene Barrister." Alkali ya tambaya

Cikin sauri ya fara cewa .
"Barrister Fatima tana shirin karya mana hujja tare da danganata da kagaggen labari ."

Alkali ya kalli Barrister Fatima yana fadin.
"Ki gyara barrister Fatima."

Barrister ta yi godiya ga alkali ta cigaba da cewa .

"Ya mai shari'a, ina rokon kotu data dubi kyakykyawar alakar dake tsakanin marigayiya da Zarah , domin ko kallan banza Zarah bata ta'ba yiwa Hajjiya Samira ba .

Amma ina rokon kotu data bani damar tambayar Hajjiya Binta domin sanin mene ne ya kawo Zarah ta yi wa Hajjiya rashin kunya, wato muna son ta sanar da kotu da wanne irin kalamai Zarah ta yi amfani dasu yayin rashin kunyar da kuma irin martani da ita marigayiya ta yi wa zarah har ya sa Zarah fusata ta bangajeta ."

"Ina da jah ya mai shari'a."
"Tun da aka ce rashin kunya kowa yasan rashin kunya barrister Fatima na shirin ja mana shari'a ta yi nisa bayan komai ya bayyana."

Inji barrister Nuhu

Alkali ya ce .
"Barrister Nuhu korafinka bai ansu ba ."

Alaji Mansur ya yi murmushi na farin ciki yana sake kasa kunne a domin sauraran wannan shari'a

Alkali ya kalli Fatima yana fadin.
"Kotu ta baki dama ."

Barrister Fatima ta yi murmushi tana kallon Hajjiya Binta da cewa .
"Kotu na sauraranki Hajjiya kuma malama Binta."

07040805269
WhatsApp only

FATIMA DA ZARAH🎀

Na
Autar Marubuta

_______________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing❌

Page 40 & 41

Hajjiya Binta kawai ta fara kuka tana kuma shirin fara magana
"Ni-ni ni Allah ya sani na shiga tashin hankali." Ta kuma fashewa da kuka harda majina

"Na shiga rudani babu abin da zan iya tunawa."

Wani takaici Barrister Fatima taji ya sokar mata zuciya ta kalli Hajjiya Binta tana cewa
"Kotu na sauraran ki ."
Hajjiya Binta ta cigaba da kukan ta

Lokacin Fatima ta baro gabanta ta fuskanci alkali tana cewa.
"Ya mai shari'a Hajjiya Binta akwai wani abu da take boyewa kotu , sannan wannan kotu ta tuna cewa babu babu kowa cikin gidan sai su biyu .

Amma ya mai shari'a me yasa ZARAH ce kawai zata zama abar zargi , shin ita Hajjiya Binta kotu ta yadda da ita ne ? Hajjiya binta muna da bukatar ta bude baki ta yi wa wannan kotu bayani. Amma hakan ya gagara , da haka nake rokon wannan kotu mai adalci data sake bamu lokaci a wani zaman domin samun hujjoji ga wacce ake kara .Na gode ya mai shari'a."

Ta yi godiya ta koma ta zauna

"Lauyan wanda yake kara kana da ta cewa ."?
In ji alkali

Barrister Nuhu ya ce .
" Eh ya mai shari'a. "

Ya nufi gaban Zarah yana cewa.
"Shin Zarah kuna da 'yar aiki a gida ."?

Zarah ta kalli Fatima, sannan ta ce ." A'a babu."

"Me gadi fa ."?

Ya sake jefa mata tambayar

Zarah tai ajiyar zuciya ta kuma cewa .
" A'a babu ."

"To me ya sa babu ? Bayan da cewa duk mazauna gidan fita kuke yi , sannan akwai motoci akallah guda shida a cikin gidan amma babu mai bude get ."

Zarah ta kalli barrister Nuhu tana cewa.
"Bamu da ra'ayinsu hakan ya sa bamu d'auka ba .Kuma mene alakar wannan da shari'ar."?

Barrister Nuhu ya kalli alkali yana cewa.
" Na gama ya mai shari'a. " Ya koma ya zauna

Bayan alkali ya yi rubutunsa ya d'ago yana cewa.

"Wannan kotu ta d'age shari'a zuwa kwana uku, a tare da hakan wacce ake tuhuma Zarah Sale za a maida ita zuwa gidan gyaran hali kafin sauraran shari'a ta gaba."

Alkali ya fad'a tare da mikewa

Kuka Zarah ta fashe dashi tana kaiwa kasa , yayin da Mahmud yaji matukar tausayinta ya sake rufe sa , sai da yaji wasu hawaye sun gangaro masa

Haka Fatima dauriya kawai tai duba da dandazon mutane , ga 'yan jarida , ga shi bata da wata hujja da zata tunkari kotu a zama na gaba .

Bayan Kamal ta bi da ya fice waje , domin ya ga an yi waje da Zarah za a sata a motar gidan yari wacce aka kawota a ciki .

Kawai kuka ya fara yana rungume mahaifin shi Alaji Mansur, Alaji Mansur wani yanayi na matukar tausayin d'an shi yaji ya fara keta masa zuciya.

Lokacin Fatima ta karaso inda suke , babu annuri a fuskarta ko kad'an

"Fatima yaushe shari'ar nan zata kawo karshe ."?
Alaji Mustapha mahaifin ta ya yi mata tambayar

Sai da taja dogon numfashi sannan ta kalli Kamal , kana ta kauda kai cikin tsananin tausayinshi ta kalli Barrister Nuhu da yake tsaye can nesa dasu Faruk suna zantawa ta ce .
" Barrister Nuhu na yi shari'a dashi sosai Daddy , koda yaushe ni nake nasara , amma bai taba karaya ba , a wannan karan yana tafe sosai domin ya karbi bangare me saukin hukunci ."

Wani tashin hankali Kamal ya sake rufe masa zuciya da jin kalaman Fatima harda kuma hawayehawaye

"Ban ce Nasara baza ta samu ba Baba amma koma mene zai faru zama na gaba kotu zatai hukunci, domin ba shari'a ce me sarkakiya ba ."

Alaji Sale ta kalla cikin rurucewa da kuka tana sake fadin .
"Idan kotu ta yankewa Zarah hukuncin kisa , sai dai mu daukaka kara."

Fatima ta tsuguna kasa tana kuka , wani firgici ne ya ziyarci kowanne su , babu kamar Alaji sale da Kamal

Kamal ya saki hannun mahaifin shi ya durkusa gaban Fatima yana kuka
"Kina nufin kin karaya kuma Zarah kasheta za ai."?

Idanunshi sun yi jajir Fatima ta kalleshi cikin matukar damuwa ba tare da tana da niyyar cewa komai ba

Alaji Mustapha ne ya durkusa ya jawo hannunshi suka taso

Sannan ya kalleshi yana cewa .
" Ka yi hakuri dan Allah Kamal , duk muma fa muna cikin wannan tashin hankalin, ita shari'a ai mace ce me ciki , ba a san mene zata haifar ba , Allah ya kaimu zama na gaba kawai mu cigaba da addu'a Allah zai bayyana gaskiya. "

Alaji Mansur ya ce .
"Wannan gaskiya ne ."

Kamal ya zare hannunshi ya nufi mota

Haka kowa ya kama hanya aka koma gida .

Yana sauran kwana 1 za a koma kotu

Kamal duk yabi ya sake lalacewa dashi

Fatima tana zauna a falo
Ta zurfafa matuka cikin tunani domin har Nasir ya shigo ya zauna bata sani ba

A lokacin ya yi ajiyar zuciya yana cewa.
"Aunty Fatima lafiya kuwa."

Fatima ta kalleshi ba tare da ta ce komai , sannan Nasir ya sake fadin
Chapter 17 · 0% Book details