← Book details Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 20

Sashe 19

Fatima Da Zarah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta shiga ciki domin ta dauko mini .

Da wowarta ya yi daidai da fitowar Abba daga dakin Nasir cikin fusata ya bangaje Hajjiya Samira ta fadi."

Nan kowa zuciyarshi ta fara bugun ....

"Da sauri na nufi gunta , amma bata iya ko bude idoba , hakan ya bawa tunani cewa ta mutu .

A ranar naga tashin hankali a idanun Abba wanda ban taba gani ba

Ya ringayi mani magiya kan na rufa masa asiri daga yau ya dena komai ya tuba ,

Hakan yasa na amince ya tafi , saboda ko ba komai d'ana na daukeshi ."

Wani kuka take kamar mai shirin shidewa

"Hakan ya sa na nemi mafita , nasan da cewar Nasir baisan abin daya faruba ,
A wannan yanayi sai Zarah ta fito , shi ke nan na dora mana wannan laifi domin samin salama ta da Abba Alajiiiiiii."

Ta kai kasa tana kuka

Dactor Zarah wani yanayi ne ya rufeta kawai ta fara kuka

Kotu aka barke da hayaniya , caaaaaa shaaaa wannan ya ce wannan ya mayar masa .

Alkali ya bukaci a yi shiruuuushiruuuu

07040805269
WhatsApp only

Autar Marubuta
FATIMA DA ZARAH🎀
Na

Autar Marubuta
________________________________________
*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing❌

Page
44 & 45

Bayan kotu ta yi shiru , kawai kukan Hajjiya binta kawai ake ji

Zarah kuwa hawaye take

Nan alkali ya bada sammacin kawo Abba Alaji a duk inda yake

Aiko yana gida mahaifin shi yana shirin su tafi filin jirgi domin Abba zai koma makaranta, basu kai ga tafiya ba
Aka kamo Abba Alaji aka taho kotu , nan Hajjiya Nana da Alaji Sani hankali su ya tashi suka biyo bayansa.

Ana shigo da Abba Alaji ya kalli Hajjiya Binta yana cewa.

Cikin kuka
"Wato saida kika bayyana komai , bayan kin yi mini alkawarin rufa mini asiri , wannan ita ce soyyaya da kike mini ,bayan na shiryu na dena kin yaudare ni ."

Kotu ta sake barkewa da ka ce, na ce , alkali ya bada umarnin shiru

Nan kotu ta karantawa Abba Alaji irin tuhumar da ake masa, nan ya amsa laifinsa bisa kuskure

Hankulan jama'a suka sake tashi sosai

Barrister Fatima ji take kamar ta fesawa Hajjiya binta mari domin wani abu take jin ya tsaya mata a zuciya

Su kam su Faruk yau gasu ga makashin mahaifiyar su kawai hukunci suke jiran kotu ta yanke .

Zarah kukan farin ciki take yi da bakin ciki a hade, Kamal kuwa zuciyarshi cike da zumudi

Nan Alkali ya fara gabatar da irin tuhumar da aka yiwa Zarah Sale

Nan ya tabbatar wa al'uma kotu ta wanke Zarah Sale bisa wannan zargi da ake mata , sannan kotu ta sallameta .

Abba Alaji bisa wani shashi na kundin tsarin mulki aka yanke masa hukuncin zama a gidan yari har karshen rayuwarsa .

Sannan Hajjiya Binta bisa kazafi na kisa data dorawa Zarah Sale
Duba da wasu shashin kundin tsarin mulkin kasa
Alkali ya tabbatar mata da dangwama a gidan yari har karshen rayuwarta .

Sannan alkali ya sallami wannan shari'a tare da wanda bai yadda da wannan shari'a ba yana da damar daukaka kara cikin watanni uku .

Khalid kuka ya fashe dashi na matukar tashin hankali dajin irin wannan hukunci da aka yankewa mahaifiyar shi .

Da gudu Zarah ta nufi mahaifiyar ta da mahaifin ta tana rungumesu cikin wani kuka mai karya zuciya

A wannan lokacin wasu zafafan hawaye suka zubowa Fatima sanda ta tuna da mahaifiyar ta

Kamal kuwa duk ya rasa inda zaisa kanshi farin cikin da yake ciki

Alaji Mustapha da Alaji Mansur ba a cewa komai

Suna gani aka sanya Hajjiya Binta a motar gidan yari tana kuka, Alaji Mustapha ya kauda kanshi, yayin da ya hangi Khalid cikin mugun yanayi

Kawai ya tsinci kanshi shima cikin wannan yanayi

Alaji Sani abin ya yi masa yawah ga danshi ga kanwarshi , duk yabi ya susuce , to sai dai Allah baya dorawa mutum jarabawar da zata fi karfin shi .

'Yan jarida kuwa sai neman labarai suke , sai dai samm basu samu damar magana da Zarah ba .

Haka Fatima bata saurare su ba

Lokacin da Fatima take kuka ne Kamal ya rike hannunta

A lokacin su Faruk suka fito daga cikin kotun suka wuce ta gabansu

"'Yan uwana .'!

Fatima ta fada cikin muryar kuka

Su faruk suka dakata ba tare da sunce komai ba

Cikin wannan yanayin ta ce .
" Ina kaunar ku , bani da sama daku , duk shari'a ta gaskiya nake bi hakan yasa nake yin nasara."

Faruk ya sa kai ya wuce , suka bi bayanshi suka tafi

Fatima ta sake fashewa da kuka tana cewa Kamal.
"Ina kaunar su sosai ."

Kamal ya mata murmushi yana cewa.
"Suma suna alfahari dake , kuma zaki gani ."

Ta masa murmushi cikin kuka

Sannan ta ce .
"Mu tafi gida kawai domin nasan Alaji sale tare da Zarah zasu tafi sun yi kewarta ."

Kamal ya kuma yi mata murmushi sannan suka wuce suka tafi

Alaji Mustapha ya matukar shiga wani yanayi, haka kowa na cikin gidan, Hajjiya Rukayya ma abin yana matukar dukanta

Khalid ya matukar zautuwa haka Habib ba a cewa komai

Haka su Alaji Sale suka wuce gida cikin matukar jin dadi , Mahmud da Umar farin ciki ya ishe su .

Washe Gari da wajen karfe 12
Sai ga Alaji sale da Hajjiya Sa'adatu da Umar, Mahmud da Zarah sun nufo gidan Kamal

Ai kuwa Nasir da kamal duk suna gida
Bayan su Alaji sun shigo sun zauna aka gaggaisa cikin farin ciki da wasa da dariya

Sannan Fatima ta kalli Zarah tana cewa.
Cikin harshen turanci
"Barka da dawowa likitan zuciya."

Kowa murmushi ya yi , Zarah tai dariya sannan ta ce .
"Hmm abin dai kamar mafarki a karshe gaskiya ta bayyana ."

Fatima tai murmushi tana fadin .
"Ai karki damu ki aikata duk abin da kike so."

Dariya kowa ya yi sannan Zarah ta ce .
"Kar dai ki cika mini baki naje nayo kisa ki barni a ciki ."

Dariya Fatima ta kwashe da ita sannan ta ce.
"Allah dai ya kyauta Allah ya jikan mommy na ."
Wasu hawaye suka gangaro mata

Zarah ta tashi ta koma kusa da ita , kana ta rike hannayen ta tana cewa.
"Ina matukar baki hakuri Fatima, ina jajanta rashin mommy, dan Allah ki yi hakuri amma ai muna da wata uwar."

Zarah ta karasa maganar tana nuna mahaifiyar ta tana murmushi

Murmushi Fatima ta yi sannan ta had'a ido da Hajjiya Sa'adatu cikin wannan hawaye .

Hajjiya Sa'adatu ta fara mata murmushi tana fadin .
"Haka ne Fatima, ki dauke ni uwa , domin kin yi mana abin da bamu da abin da zamu biyaki .."

"Haba ,haba mommy dan Allah." Fatima ta fada tana share hawaye

"Zarah ce ta fara komai , ta kula mini da mommy matuka , hakan yasa zan iya sadaukar da komai a domin ce to ta dan Allah kar ku yi mini godiya."

Ta aje maganar tana kallon Alaji Sale

Nasir ya yi murmushi yana kallon Kamal, kamal ma ya maida masa da murmushi na farin ciki.

Alaji Sale ajiyar zuciya ya yi sannan ya dubi Fatima ya fara mata magana .
"Bani da komai da zan biyaki Fatima, hatta kalaman da zan nuna miki matsayinki a guri na bani dasu , ki gafarce ni."

Murmushi Fatima ta sake yi tana kallon Zarah, Zarah ma ta maida mata da murmushi tana cewa.
"Wallahi Fatima ina kaunar ki matukar gaske dan Allah ki yafe mini duk abin dana yi miki wanda baki ji dadi ba."

Dariya Fatima ta yi tana cewa.
"Jibeta dan Allah."

Nasir da yanayin ya masa dadi ya yi dariya

A lokacin aka fara kwankwaso kofar falon .
Kafin kowa ya yi motsi aka fara kallon -kallon domin basa tsammanin zuwan kowa a halin yanzu

Nasir ya tashi ya nufi kofar a domin budeta

Yana bud'e wa ya ga Faruk ya fara shigowa , yana shigowa ya kalli falon ya gansu duk a zaune suna kallon shi

Lokaci guda kuma suna had'a ido da Alaji Sale.

Fatima ta mike tsaye

Sannan su Ahmad dasu Murja ,Najib suka shigo

Kamal ya tashi ya nufi wajensu yana musu nuni dasu karaso

Suka kalli juna , sannan suka nufo falon ,
Duk suka zazzauna , yayin da kujerun suka cika ne babu gurin zama shi kuma Faruk yana tsaye .

Alaji Sale ya kalleshi tare da matsawa gefe yana ce masa
"Faruk karaso ka zauna ga guri ."

Ya kalleshi tare da tuna irin sa'insar da sukai kafin shiga kotu , sannan yayi ajiyar zuciya tare da duba agogon hannunshi ya nufi wajen shi ya zauna.

Autar Marubuta
FATIMA DA ZARAH🎀
Na
Autar Marubuta
_______________________________________

*AUTAR MARUBUTA CE*✍🏻👼🏻
🌹__________🌹_________🌹__________🌹_________🌹
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_🤲🏼
<><><🌹><><><>🌹<><><>🌹<><><><>🌹<><><><><>🌹<><

Editing❌

Page 46 & 47 ________the end

Sannan ita ma Fatima ta zauna tana kallon kowanne su , shiru aka yi kowa yanata sake-sake cikin ransa

Jin wannan shirun yasa Faruk ya kalli Fatima ya fara magana cikin sanyin rai .
"Ba ke ba ce lauyan mu , amma tamkar ke ce kika bamu kariya .
Bawai nufin mu shi ne tozarta Zarah ba , muna cikin radadin da yunwar rashin mommy hakan yasa idanun mu suka rufe ."

Alaji Sale ya yi murmushi yana sake kasa kunne

"Komai ya faru cikin fushi ,hakan yasa na zo neman a fuwarki Fatima ki yafe mini da abin da ya faru ."

Murmushi Ahmad ya yi na farin ciki yana kallon Najib

Fatima ta kalli murja kana ta maida ido ga yayan nata tana cewa.
"Babu abin da kayi mini Yaya faruk, ni ce na yi muku laifi dan Allah ku yafe mini ."

Murja ta ce .
"A yanzu muna matukar alfahari dake Fatima wancen rudanin muna cikin yanayi ne . "
Chapter 19 · 0% Book details